15/06/2025
Bakar Cin Amana Daga Kamfanin GoDaddy!
Jama'a barkanmu da warhaka. Na rubuto muku wannan saƙo be domin sanar da ku muhimman abubuwa da s**a faru game da horon kwamfuta da ICT na CUPS kyauta, wanda muka shirya zai fara a yau, kuma munyi niyya ya amfani mutane 16,000 daga cikinmu, wadanda mafi yawansu ba su da isasshen ilimi a fannin Kwamfuta da ICT.
A cikin watanni huɗu da s**a wuce, mun yi aiki tukuru wajen gina ingantaccen tsarin ICT da kuma samun ƙwararrun ma'aikata domin tabbatar da cewa horon zai fara cikin sauƙi kuma a kan lokaci. Mun aiwatar da muhimman abubuwa kamar haka:
1. Mun sayi sabon domain daga GoDaddy (www.cupsorganisation.uk).
2. Mun sayi domain hosting domin wannan shafin yanar gizo.
3. Mun sayi tsarin email marketing da ke bayar da damar aika saƙonni har 870,000 a kowane wata, wanda zai ba mu damar aika saƙonni sau 54 ga kowanne ɗalibi daga cikin dalibai 16,000 a wata guda! Dubascreen shot da muka lika da wannan sakon.
4. Mun rattaba hannu kan yarjejeniya da ODEH, kamfani mai ƙwarewa a software da horon kwamfuta ta yanar gizo domin samar da tsarin horon da za mu yi amfani da shi.
5. Mun rattaba hannu da ƙwararru 16 a fannin Kwamfuta da ICT domin su gudanar da horo na tsawon watanni 4. Kowannensu zai yi aiki na awanni 80 a wata (da dare) kuma ya karɓi albashin N100,000.
6. Mun tsara tsarin karatu mai zurfi da zai ɗauki duk tsawon watannin 4 na horon.
7. Mun rattaba hannu da wata jami'a mai daraja domin bayar da shaidar kammala horo ga waɗanda s**a halarta aƙalla 90% cikin dari.
8. Mun tanadi shirin jagoranci domin taimaka wa waɗanda s**a kammala horon su shiga aiki ko kuma su kafa nasu kasuwanci.
Don taƙaita labarin, bayan da muka kammala duk waɗannan shirye-shiryen, GoDaddy — kamfanin da ke da alhakin hosting da email marketing — ya cin amanar mu. Wannan kuwa kamfani ne da ake ɗauka a matsayin daya daga cikin manyan kamfanoni masu karfi a duniya a wannan fanni.
Jama' tun ranar Talata, 10 ga Yuni, 2025, muka fara fuskantar matsaloli. Da farko, mun ci karo da matsala wajen kokarin loda jerin adiresoshin imel na dalibai cikin akwatuna da ake kira “Customer List”. Bayan dogon waya da tattaunawa da tawagar tallan imel na GoDaddy an warware matsalar. Amma kwatsam, ba tare da wata gargadi ba, a ranar Alhamis, 12 ga Yuni, muka gane cewa ba za mu iya hade Customer List na Ajin 3 da sakon imel da muka rigaya muka shirya ba. Duba screen dump. Ku lura da cewa zabin customer list an dakileshi da gangan.
Nan take na tuntubi sashen tallafin kwastomomi na GoDaddy Email Marketing. S**a ce sai na bar cikakken bayani game da matsalar a wani shafin musamman da aka ware don matsalolin Email Marketing, kuma hakan na yi.
A ranar Jumma'a, 13 ga Yuni, na samu sakon amsa daga gare su. Ku dubi screen dump. Tun daga lokacin, duk da yawan kiran wayar da na yi wa GoDaddy, ban samu wani taimako daga gare su ba don warware wannan matsala mai matukar muhimmanci. GoDaddy na sane da cewa yau ce ranar da muka tsara fara horo.
Yanzu haka, mun samu nasarar aikawa da imel zuwa ga daliban ajinan 1, 2 da 7 kawai. Kuma a gaskiya, wadannan imel din gwaji ne kawai. Mun shirya aika imel zagaye na biyu mai dauke da cikakken umarni. Abin takaici, an tsaida mu ne a lokacin da muke kokarin aika sakon imel ga daliban Ajin 3. Daliban ajinan 3, 4, 5, 6 da 8 ba su samu ko sakon imel guda ba har yanzu. Kafin na shiga yanar gizo yanzu, na sake kokarin aikawa da daliban Ajin 3, amma har yanzu ba za a iya hade jerin sunayen imel da sakon ba!
Na yi taro da Daraktocin CUPS guda 7 jiya da dare da kuma safiyar yau. Mun yanke shawara daya, cewa ba za mu iya fara horas da dalibai marasa isasshen bayani ba – wadanda ba su wuce 4,000 ba daga cikin dalibai 16,000. Wannan yana da hadari kwarai da gaske.
Mun yanke shawarar jinkirta fara horon na tsawon mako biyu. Wannan zai bamu damar neman wani kamfani daban, wanda muke fatan zai kasance kamfani da ke cikin Birtaniya (UK).
Jama'a, a madadin Hukumar Kula da CUPS da kuma Kwamitin Daraktocin CUPS, ina mika gundarin afuwa bisa wannan lamari mai cike da takaici wanda aka tilasta mana.
Muna matukan takaici bisa bacin rai da wannan jinkiri zai iya janyo muku. Muna tabbatar muku da cewa za mu yi duk mai yiwuwa don mu ci gaba da wannan tafiya na horo cikin makonni masu zuwa.
Jama'a na barku lafiya.
Dr. Idris Ahmed.
CUPS.
15/6/2025.