14/07/2024
Drs wai meyasa matan turawa harsu haihu zakaga nonuwa a tsaye,amma namu matan wasu tunkafin aure nonuwa sunzube
Amsa :
Kai! Nono, nono, nono. Hakika maza sun damu da nono sosai, kuma hakan shine yake ingiza matanmu wajen yin shaye-shaye da shafe-shafen magunguna domin ganin nonuwansu basu zube ba.
Gaskiyar magana ita ce siffar nonon mace ta tsayuwa kyam (perkiness), ko zubewa (sagging), tanada nasaba da abubuwa ne masu yawa wadanda s**a kunshi gado (genetic predisposition), tsarin tafiyar da rayuwa (lifestyle), al'ada (cultural factors), da lafiyar jikin mace (overall body health condition).
Amma yanada kyau mu fahimci ba daidai bane ayiwa mata kudin goro game da siffar nononsu k**ar yadda kayi yanzu. Ma'ana, kuskure ne kace matan kabila kaza, ko gari kaza, ko jinsi kaza, koda yaushe nonuwansu basu zubewa, kuma na wasu koda yaushe suna zubewa.
Idan hujjarka ta fadin hakan ita ce saboda kana ganin matan turawa a cikin fina-finai da nonuwa tsattsaye, to, kayi kuskure, domin yawancin nonuwansu bana gaskiya bane. Wadanda aka yiwa tiyatar implants ne kake gani, ko kuma an tallabe su da rigar nono ne (support bra), ko kuma na roba ne (prosthetic breasts).
Sa'annan nonuwan matanmu da kake daukar cewa suna saurin zubewa, wasuma tun kafin suyi aure ko su shayar, shima wadanda ka gani kenan. Amma akwai mata masu yawa wadanda nonuwansu basu saurin zubewa k**ar yadda kake tsammani. Ina tabbatar maka da cewa akwai matanmu wadanda har zasu gama haife-haifensu, amma nonuwansu basu zube ba.
Sa'annan magana ta gama-gari ita ce yawancin nonuwan mata a duniya gaba daya suna zubewa, saidai idan lokacin zubewar baiyi ba.
Amma idan s**a zube, to, yanzu aiki ya dawo wajenmu maza domin mu taimakawa matanmu domin dawo da martabarsu, ta hanyar:
1. Nuna musu rashin kyama.
2. Daina kyararsu.
3. Samar musu da sutura ta kwalisa.
4. Wadata su da abinci da abinsha mai rai-da-lafiya, gwagwadon karfinmu.
Na bata lokaci ne wajen yin wannan bayanin domin matsalar tana damun matanmu da yawa MORE......... sashin comments