22/01/2026
DON ALLAH IYAYE MATA (UWAYEN MIJI) KU DINGA BARIN MATAN YAYAN KU SUNA ZAMAN AUREN SU A GIDAJENSU!!
Wani case da aka kawo mana abun yabamu mamaki sosai duk da cikin ikon Allah yanzu komai ya koma normal kuma insha Allah yanzu Baza a sake ba.
Wata uwar miji ce mai yawan bibiya da bin kwakwkwafin rayuwar auren danta. Suna zaune lafiya a gidansu ita ma uwar tana gidanta Amma sai ta takura sai ya dawo da ita gidansa sun zauna tare da matarsa (wannan duk ba kuskure bane), haka kuwa yayi sannan da ta dawo sai abincin da tace tana so akeyi a gidan (hakanma duk babu matsala ai itace Sanadin zuwansa duniya), a gidan yazama ita ake tambaya idan za aje unguwa Koda yace Eh idan ita AA ce to tata za a dauka (wannan ma ba damuwa bace, amma an shiga wani hurumin) Karshe dai wata matsala da da tafi duk wadannan ta faru wadda matar taga yakamata tayi wani move domin ganin samun sauki.
Gaskiya munsha aiki Sosai kafin shawo kan matsalar Amma dai karshe munyi Nasara.
DON ALLAH IYAYE KAMAR YADDA KUKA YI ZAMANINKU, KU BAR MATAN YAYANKU SUYI NASU.
KU KUMA MATAN YAYA KODA WASA KADA KU RAINA UWAYEN YAYANKU, KU DARAJASU, KU MUTUNTA SU DOMIN SUN CANCANCI SAMA DA HAKAN AGUNMU.
ALBARKA DALILIN AURE BISA SUNAH CENTER
(Cibiyar hadin Aure da bada shawarwari ga maaurata)
RC: 8779470
08069590002
Albarkamatchmaking@gmail. Com
22nd January, 2026