01/07/2025
Ki daina ganin namiji bai isa dake ba. Wannan tunani yana ƙara yawan matsaloli a cikin aure da zamantakewar mu. Miji gata ne a gare ki rufin asirinki ne, kuma garkuwarki ce a rayuwa. Idan kika girmama shi, Allah zai girmama ki fiye da yadda k**e zato.
Kada ki yarda a zuga ki ki raina miji. Akwai mata da ake koya musu cewa biyayya rauni ne, ko kuma cewa kar su saurari duk abin da miji ke faɗi. Wannan hanya ce ta rugujewar zaman lafiya. Ki nisanci irin waɗannan matan da dama daga cikinsu sun rasa kwanciyar hankali kuma sun fita daga hanyar da addini ya shar’anta.
Girmama miji ba kaskanci ba ne, wata hanya ce ta samun ɗaukaka. Mace mai ladabi, biyayya, da natsuwa tana da ƙima fiye da wanda ke yawan faɗa da gardama. Kuma irin wannan mace tana da daraja a wajen Allah da kuma mijinta.
Ki dinga tuna makomar ki a wajen Ubangiji. Rayuwar aure da mutunci na farawa ne da yadda ki ke kallon mijinki. Idan kika ɗauke shi da mutunci, rayuwarki za ta cika da albarka.
Idan kina ganin wannan sakon yana da amfani, ki raba shi da wata ’yar uwarki.
Kuma idan kina fatan zaman aure na kwanciyar hankali, ki ce: “Ameen.”
Maryam I Bununu