03/09/2024
*๐ฉถ๐ฅNasiha ga masu sukar masu sanya Niqabi...*
*๐ฉถ๐ฅGaba ta farko:*
*Babu sabani a wajen Malaman Musulunci akan kasancewar Matan Annabi (SAW)-iyayen Muminai- cewa tun bayan saukar ayar ta 59, ta cikin Suratul Ahzaab, a shekara ta 5 zuwa 6 bayan Hijira, sun kasance suna rufe jikinsu daga sama har kasa, abinda ya hada har da fuskarsu (Niqab), basa bayyana fuskarsu ga ajnabi...*
*๐ฉถ๐ฅGaba ta biyu!*
*Babu sabani a wajen Malaman Mazhabobin Fiqhu fitattu guda hudu (Hanafiyya, Malikiyya, Shafi'iyya, Hanabila) akan wajabcin Mace ta rufe fuskarta idan anji tsoron aukuwar fitina, fitinar nan kuma itace, idan Mace tana da dan karen kyawu, zata fitini Maza, ko kuma idan lalacewar zamani ta kai Maza basa iya rumtse ganinsu, wannan babu sabani akansa, duka Mazhabobin sun fadi haka...*
*๐ฉถ๐ฅGaba ta uku!*
*Malaman Fiqhu sunyi sabani game da hukuncin sanya Niqabi, idan an aminta daga fitina zuwa maganganu gida biyu:..*
*๐ฉถ๐ฅ(i) Masu ganin Halascin bude fuska!*
*Mafiya yawan Malamai sun tafi akan halascin bude fuskar Mace ga Ajnabi, idan an aminta daga fitina, k**a daga Malikiyya, Hanafiyya zuwa Shafi'iyya.*
*๐ฅZan takaita akan kawo magana daya rak, daga kowace Mazhaba.*
*๐ฉถ๐ฅโขMalikiyya:*
*Ibnul Qasim (Dalibin Imam Malik) ya tambayi Imam game da Matar da Mijinta ya mata Zihari (ya haramtawa kansa ita), shin matar zata haramta masa kanta, idan ya kusanceta?*
*Imam Malik ya amsa:*
*Eh, zata hana masa kanta, kuma bai halasta ya kalli gashin kanta ko kirjinta ba.*
*Ibnul Qasim ya sake tambaya:*
*Shin zai kalli fuskarta?*
*Imam Malik: Eh, waninsa ma ya halasta ya kalli fuskarta.*
*{Mudawwanah 2/334-335}*
*๐ฉถ๐ฅWannan riwayar kai tsaye, tana bayyana halascin Mace ta bude fuskar ga wanda ba muharraminta ba (idan an aminta daga fitina, k**ar yadda bayani ya gabata a sama)...*
*๐ฉถ๐ฅโขHanafiyya Muhammad Bin Hasan Al-Shaibany (Dalibin Imam Abu Hanifa ne), ya ambata acikin Al'asl, k**ar haka*
*((ุฃู
ุง ุงูู
ุฑุฃุฉ ุงูุญุฑุฉ ุงูุชู ูุง ููุงุญ ุจููู ูุจูููุงุ ููุง ุญุฑู
ุฉุ ู
ู
ู ูุญู ูู ููุงุญูุง : ูููุณ ููุจุบู ูู ุฃู ููุธ