19/12/2024
Ɗabi'u 7 da likitoci ba sa son ka nuna masu yayin da ka je asibiti.
Ɗabi'un sun haɗa da:
1. Ƙoƙarin nuna kai ma mai ilmi ne.
2. Ƙoƙarin nuna kai ma wayayye ne.
3. Ƙoƙarin nuna kai ma idonka ya buɗe.
4. Ƙoƙarin nuna kai ma mai muƙami ne a wani wuri.
5. Ƙoƙarin nuna kai ma ka san "wani" a asibitin.
6. Ƙoƙarin nuna kai ma ka san ƴancinka ko haƙƙinka.
7. Mafi muni shi ne, ƙoƙarin nuna wa likita aikinsa.
A duk lokacin da ka ji likita ya ce "to aikina za ka nuna min?!" To gaskiya ka kai shi bango! Ya kamata ka tausasa kalami domin sakko da shi.
Ana yi wa likitoci kyakkyawan horon mu'amala da hulɗa da majinyata da sauran mutane iri-iri domin su iya shanye munanan ɗabi'u da halayen mutane a asibiti. Amma fa, su ma ƴan'adam ne!
Saboda da haka, babu buƙatar nuna wa likita waɗannan ɗabi'u idan kana son cin ribar zuwa asibiti.
Kawai ka bari mu'amalarka ta fassara wane irin mutum ne kai.
Kuma ƙasƙan-da-kai ai ba ƙasƙantar da kai ba ne!