Kula The Lafiya

Kula The Lafiya Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Kula The Lafiya, Medical and health, Arewa, Arewa.

Yadda ake fadar Barka da Sallah cikin ire iren yaren da muke da su a fadin duniya.Kar dai a manta,   a ko yaushe shine f...
19/07/2021

Yadda ake fadar Barka da Sallah cikin ire iren yaren da muke da su a fadin duniya.

Kar dai a manta, a ko yaushe shine fatanmu gareku..

M E N E N E    G E N O T Y P E ? Irin tambayoyin da muke ta samu daga maza da mata, a yau zamu yi takaitaccen bayani aka...
18/07/2021

M E N E N E G E N O T Y P E ?

Irin tambayoyin da muke ta samu daga maza da mata, a yau zamu yi takaitaccen bayani akan abin da ake nufi da genotype cikin harshen hausa tare da tasirin saninsa kafin aure.
.Dukkan d'an Adam an halicceshi ne tare da wasu kwayoyin halitta wanda ke gudana a jikinsa, su wad'annan kwayoyin halittar gadonsu ake yi, wato dai 'ya'ya suna samun sune daga nau'in wanda iyaye suke dashi. Idan iyaye s**a zama da nau'i mai kyau za a samar da 'ya'ya lafiyayyu, akasin haka za a samu 'ya'ya masu rauni da matsalar amosanin jini wato sikila.

Masana sun raba genotype kaso uku: homozygous dominant, homozygous recessive da kuma heterozygous.

Ana sanin genotype ne idan anyi gwajin jini, wanda bayan gwajin jinin ne ake samun bayanai akan nau'in da ke jikin mutum cikin nau'i guda uku kamar haka: AA, AS, SS.

AA sune masu cikakkiyar kwayar halitta, AS su ake kira da carrier, akwai d'an rauni a kwayar halittarsu, na ukun sune SS wato masu dauke da amosanin jini (sikila) saboda raunin ita wannan kwayar halittar yakai makura.

Abu mai muhimmanci da ya kamata a lura da shi kafin aure bayan gwajin genotype sune kamar haka: (Miji + Mata = Sakamakon 'ya'yan da za a samu)

1. AA + AA = AA, AA, AA, AA (za a samar da 'ya'ya masu cikakkiyar lafiya)
2. AA + AS = AA, AS, AA, AS (shima wannan babu matsala a lafiyar yaran da za a haifa, amma bai kai na saman ba)
3. AA + SS = AS, AS, AS, AS (yaran da za a haifa zasu zo a AS wato carriers)
4. AS + AS = AS, AS, SS, SS (za a samu d'a ko 'ya mai cutar sikila)
5. AS + SS = AS, SS, SS, SS ('ya'ya kusan kaso 80 zasu zama masu sikila)
6. SS + SS = SS, SS, SS, SS (akwai matsala sosai, domin dukkanin iyaye da 'ya'ya sikila ne, akwai tsanani da wahala na rashin lafiya).

Yana da matukar kyau da muhimmanci kafin aure ayi kwajin genotype domin lura da wadannan matakan. Misali "idan ina da sikila, wanda zan aura kuma ba sikila bane (AA), zamuyi aurenmu ba tare da mun haifi yara masu sikila ba".

Bambancewa tsakanin AA da AS abune wanda dole sai anyi gwajin genotype, SS yafi cancanta suyi aure da masu AA fiye da AS, domin Auren SS da AS za a samu 'ya'ya kaso mafi yawa masu cutar sikila(SS). Amma idan SS (sikila) da AA s**ai aure, zasu haifi yara marasa sikila (AS).

Kulawa da wad'annan matakai, nayin gwajin jini kafin aure, tare da sauraron shawarar likita bayan gwaji, zai kawo mana raguwa ko ma karshen cutar amosanin jini (sikila). Allah Ya kara mana lafiya, Ya kuma bawa marasa lafiyarmu lafiya, Ameen.

Address

Arewa
Arewa

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kula The Lafiya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Share on Facebook Share on Twitter Share on LinkedIn
Share on Pinterest Share on Reddit Share via Email
Share on WhatsApp Share on Instagram Share on Telegram