20/01/2023
BAYARDA TALLAFI GA MATAN GARIN JEGA DAKUMA ILLELAH
A yau Lahadi 17-01-2023 shahararriyar ƙungiyar Tallafawa Mata marasa Ƙarfi dake Jega/Kebbi State,ƙarƙashin jagorancin Hon Hayatu Bawa Jega Commissioner Of Environment Kuma Daya Daga Cikin Matasan Yan Siyasa Dake Garin Jega Tasake Dawowa Kamar yadda tasaba wurin taimaka mata masu kana nan sana’a kuma dake kowane ward/mazaba a karamar hukumar mulki dake jega.
Domin dogara da kansu ta kungiyar ƙaddamarda bayar da tallafin kuɗɗi Naira Dubu Goma 10k ga macce Dari ukku 300 a Ƙaramar Hukumar Mulki ta jega a karkashin jagoran cin in Mai dakin gwamna jahar kebbi, kuma uwar marayun kebbi haka zalika First Lady a jahar kebbi
Mai girma matar gwamnan jahar Kebbi H.E Dr. Zainab Shinkafi Bagudu a jawabinta ta kara kira ga mata da su fito su nemi sana’a Domin Dogara da g*i kai kuma kara Jan hankalin mata Da su fito su karbi voters card/ katin zabe Domin zaben shuwagabani na gari a Jam’iyar Apc mai Alamar tsinsiya.
Tayi godiya ga mai girma Gwamna Gwamnoni H.E Sen Abubakar Bagudu a bisa kukari da Gwamnatin jahar keyi Domin ganin chigaban Mata haka zalika takara kira ga dan takarar Gwamna kebbi wato Alhaji Dr Nasir idris kaura Gwandu da yayi koyi ga Gwamna H.E Sen Abubakar Bagudu wurin kukarin taimaka mata Domin dogara dakai. Tawagar uwar marayun k
Kebbi ta hada da Hon Tsahara Bawa, Hon zara Wali, Hajiya Aisha maikurata,Hajiya Asma’u Alkali, Khadi Malami Foundation Members, Team A Members,Apc women’s dasauran manyan matan siyasar kebbi.
Hon Faruku Umar Dan Takarar Kujerar Dan Majalisa Na Jahar Jega shima yabada nashi Tallafi ga matan garin illelah daga cikin karamar Hukumar mulki ta Jega a yau wanda uwar Marayun jahar kebbi ta jagoranta, Hon Faruku Umar yayi godiya ga uwar marayun kebbi a sisa Irin na mijin kukarinda takeyi wurin ganin Chigaban mata da wayarda kansu da sunfito a Dama dasu.
Hon Murtala Musa Habib Jega Chairman a Garin jega yayi jawabin godiya ga dukkanin Mutane da s**a halarci wanan bayar da Tallafin Ya kuma