13/10/2023
Rubutun Dr Abdulazizi T Bako
Shafi Mu Lera: Ya abin ya ke a kimiyyance?
Abdulaziz T. Bako, MBBS, MPH, PhD.
An shafe shekaru ana azabtar da mutanen da ba su ji ba ba su gani ba bisa zargin cewa sun sacewa wani yayan maraina ko al'aurar wani namiji ta hanyar siddabaru ko tsafi.
A kan irin wannan zargi maras tushe an kashe mutane masu yawa, an kuma jikkata mutane da dama. Tarihi ya nuna cewa wannan dabi'a an fara ta ne a Najeriya a shekarun 1970s sannan ta yadu a kusan dukkanin sassan kasashen Afirka.
A garuruwan Asia akwai kwatankwacin irin wannan dabi'ar wacce su ke kira 'Koro,' duk da cewa lokaci zuwa lokaci a kan dan samu barkewar cutar kasashen yamma jefi-jefi. Cutar Koro k**ar annoba ce da ta ke sanya wasu sassa na mutane su hakikance cewa tabbas al'aurarsu tana motsewa tana komawa cikin jikinsu, kuma su rika ji cewa idan ba'a yi komai ba al'aurar zata bace bat ta shige cikin jikinsu.
A lokuta da dama mutum daya ne ya ke fara cewa ya ga al'aurarsa tana motsewa, kwatsam kawai sai sauran mutane su ma su ga cewa su ma fa al'aurarsu ta fara motsewa. Irin wannan abu galibi matsala ce ta kwakwalwa (psychological problem) da kan addabi al'umma a lokaci guda wacce a je kira da "mass hysteria."
Sai dai Bambancin "Koro" da shafi mu lera shine cewa su masu Koro galibi ba wani suke zargin cewa ya yi musu asiri ba ballantana su k**a wani wanda bai ji ba bai gani ba da duka. Sannan kuma cutar Koro ba ta ta'allaqa da maza zallaba. Mata ma suna yi. Sai dai da ya ke maganar shafi mu lera muke yi ba zan tsawaita jawabi a kan cutar Koro ba.
Da yawa daga cikin masu zargin cewa an yi musu shafi mu lera su kan ce sun hadu da wani mutum sun gaisa da shi. Sai kuma daga gaisawar s**a ji wani abu ya yi musu yar a jikinsu k**ar shocking. Daga nan kuma sai s**a duba yayan marainansu sai s**a ji babu su.
Daga nan kuma kawai sai su kwarma ihu. Idan mutumin da suke zargi yana kusa su k**a shi a yi ta duka. Idan azaba ta yi azaba sai wanda ake zargin ya yadda cewa ya aikata. Amma zai dawo wa mutum da abinsa bayan wani lokaci. Idan kuwa a ka jirayi lokacin sai a ga ya dawo din. Shikenan sai mutane su gaskata cewa tabbas satar yayan marainan a ka yi.
Kafin na yi bayani a kan yadda wannan abu ya ke faruwa a kimiyyance ya k**ata na yi takaitaccen bayani a kan yadda yayan marainan dan Adam suke samuwa tun yana ciki. Su dai yayan marainan dan Adam farko suna samuwa ne a can saman cikin dan Adam. Daga baya suke sakkowa su yo kasa su zauna a cikin jakar yayan maraina (sc***um) kusa kusa da lokacin da zaa haifi mutum. Shi ya sa wasu yaran idan aka samu matsala a kan haife su da yayan marainan su a ciki ba su sakko kasa ba (undescended te**es).
A yayin da yayn maraina suke sakkowa daga ciki zuwa jakar yayan maraina, akwai abubuwa da yawa da suke biyo su ko don basu kariya ko kuma don wasu dalilai. A cikin wadannan abubuwa akawai wani nama da ake kira da suna Cremaster Muscle.
Kafin mu fadi aikin shi wannan yadin nama na Cremaster Muscle yana da kyau mu gane cewa su yayan maraina ba sa son zafi ya yi yawa ko sanyi ya yi yawa, domin kuwa aikin hada maniyyin dan Adam da a ke yi a cikin yayan maraina (spermatogenesis) ba zai yiwu ba idan zafi ko sanyi ya yi yawa.
Saboda haka sai Allah cikin ikonsa ya halicci shi wannan cremaster muscle din tare da sauran wasu abubuwa k**ar Dartos muscle da su ke tabbatar da cewa zafi ko sanyi bai yi wa yayan maraina yawa ba.
Idan zafi ya yi yawa cremaster muscle ya kan saki jikinsa sai yayan maraina su sakko kasa su sha iska. Idan kuma sanyi ya yi yawa sai cremaster muscle ya motse ya ja yayan maraina sama kusa da cikin dan Adam wanda zai zamewa yayan marainan k**ar heater. Wannan dalilin ne ma yasa a ke baiwa maza shawarar su rage saka matsatstsun dan kamfe (panties) saboda kada zafi ya rika yi wa yayan marainansu yawa.
A halittar shi wannan cremaster muscle akwai abinda a ke kira kuma cremaster reflex, wanda ya ke janyowa shi wannan cremaster muscle din ya motse ya ja yayan maraina sama sama ba wai don saboda sanyi ya yi yawa ba. Abubuwan da suke jawo cremaster reflex sun hada da idan aka shafi wurin jijiyar da ta ke baiwa shi cremaster muscle sak'o, ko kuma abubuwa k**ar matsanancin tsoro da sauransu.
A galibin lokuta shi wannan cremaster reflex ba wani can sama ya ke jan yayan maraina ba, amma a kan samu a wasu tsirarun mutane cewa motsewar da cremaster muscle dinsu ya yi yana da karfi sosai (overactive cremaster muscle), wanda wannan karfin motsewar zai iya sanyawa su ji k**ar shocking a jikinsu, kuma ya ja yayan marainan su koma can sama kusa da mafitsarsu (inguinal region) k**ar zasu koma can cikin ciki (ana kiran hakan retractile te**es).
Idan irin hakan ta faru zata iya yiwuwa a nemi yayan marainan a cikin jakarsu a rasa, amma ba wai sace su a ka yi ba. Su na nan a jikin mutum kawai dai sun yi can sama ne ta yadda ba za a iya jinsu a cikin jakar yayan maraina ba. Kana zuwa wurin likita zai nuna maka inda yayan marainanka s**a makale.
Idan an gane bayanin da na yi a sama to sai mu ce abinda ya ke faruwa shi ne mutum ya gaisa da wani da bai sani ba. Kwatsam kawai sai ya ji cewa fa ya yi kuskure don mutumin nan zai iya zama mai shafi mu lera. Kwatsam sai yanayin tsoro ya k**a shi.
Wannan karfin tsoron da ya ji sai ya saka ya ji yar a jikinsa, shima cremaster muscle ya harba ya motse sai ya ji k**ar an yi masa shocking a yayan marainansa sannan ya ja yayan marainansa sama. Daga nan kuma sai ya taba yayan maraina ya ji ko babu su ko kuma k**ar sun motse daga yadda ya san su da. Shi kenan sai a k**a wani da duka. Azaba ta sa ya yadda cewa ya saci yayan marainan, sannan ya yi alkawarin zai dawo da su. Wannan abin zai kwantarwa da wanda ya ke zargin an sace masa kayan nasa shikenan bayan wani dan kankanin lokaci ya dawo hayyacinsa ya ji komai ya dawo normal (saboda hankalinsa ya kwanta, ba wai don wani ya sace masa wani abu ya dawo masa da shi ba).
Haka abin ya ke ga masu zargin an sace musu al'aura wai ta motse. Shi ma yanayin fargaba ne da tsoro ya ke sanyawa jikin dan Adam ya fara fitar da wasu sinadarai. A gurguje, A jikin dan Adam akwai abinda a ke kira sympathetic nervous system (SNS) da parasympathetic nervous system (PSN). Saboda saukakawa mai karatu ya fahimta, shi SNS shi ke harbawa yayin da mutum ya ke cikin halin firgici da sauransu (fight and flight), shi kuma PNS shi ke harbawa a lokacin da mutum ya ke halin hutu da kwanciyar hankali.
Don haka a yayin da mutum ya ke cikin firgicin tsoron cewa an sace masa al'aura ko kuma al'aurarsa ta motse wannan tsoron ba zai bari ya ji cewa al'aurar tana yadda take ba, saboda a lokacin sympathetic nervous system ne ya ke aiki. Har sai ya samu nutsuwa hankalinsa ya dawo kansa sannan zaa gane cewa babu abinda ya same shi.
A wannan rubutu na saukake (simplifying) abubuwa da yawa saboda na saukakawa masu karatu yadda zasu fahimta. Amma muhallush shahid shine cewa babu wani abu wai shi shafi mu lera. Mu guji azabtar da mutane babu gaira babu sabab saboda wai zargin an sace musu al'aura ko yayan maraina. Duk inda mutum ya yi ihun an sace masa wani abu a yi maza a garzaya da shi asibiti ya ga likita. Babu wanda ya sace masa komai.