Pharm. Kaameel Sani Azare

Pharm. Kaameel Sani Azare Public health activist, Drug expert, Lecturer, Entrepreneur, Pharmaceuticist, Counselor, Pharmaceutical care giver and rational drug usage advocate.

CIWON GABOBI A YANAYI NA SANYI Yanayin sanyi na zuwa da cututtuka daban daban wadda ciwon gabobi (Arthritis) na daya dag...
06/11/2024

CIWON GABOBI A YANAYI NA SANYI

Yanayin sanyi na zuwa da cututtuka daban daban wadda ciwon gabobi (Arthritis) na daya daga cikinsu. Har yanzu ba'a san takamammen abinda ke jawo ciwon gabobi ba, wato arthritis. Amma bincike ya nuna cewa yanayin sanyi na haddasa karuwar ciwon, hade da kumburi da Kuma rikewar gabobin.

Hanyoyin da zasu taimaka wajen rage radadi ciwon gabobi a yanayi na sanyi sun hada da:

1. Motsa jiki wato exercise akai akai.
2. Cin abinci mai inganci wadda ke dauke da sinadarin omega-3 da antioxidants kamar kifi, gyada, ganyayyaki, yayan itatuwa da sauransu.
3. Rage shiga waje mai tsananin sanyi.
4. Rage cin abubuwa masu gishiri da yawa.
5. Kiyayewa daga sanya tufafi mai damshi.
6. Kiyayewa daga zama a waje mai damshi.
7. Samun gamsashshen hutu yayin aiki mai yawa ko mai tsanani.
8. Kula da ciwon da wuri da kuma ganin likita ba tare da bata lokaci ba don samun kulawar da ta dace.

Don samun shawarwari da karin bayanai game da cututtuka dake damunku, ko kuma magungunanku, zaku iya chatting da Pharmacist Kaameel Sani a wannan number: +2348032384079.

05/11/2024
Ciwon sanyin haqarqari (Pneumonia) wani  ciwo ne wadda kwayoyin halitta wadda basa ganuwa da ido, wato microorganisms, k...
03/11/2024

Ciwon sanyin haqarqari (Pneumonia) wani ciwo ne wadda kwayoyin halitta wadda basa ganuwa da ido, wato microorganisms, ke haddasa shi. Su wadannan kwayoyin halitta sun hada da bacteria, virus, mycobacteria, fungi, da dai sauransu. Alamomin ciwon sanyin haqarqari sun hada da: zazzaɓi, numfashi da sauri kuma da kyar, tari, majina a kirji, ciwon kirji, da sauransu.

Yaya mutum zai yi don kiyaye kamuwa da ciwon sanyin haqarqari?

1. Yawaita wanke hannu da ruwa mai tsafta da sabulu
2. Tsaftace jiki, tufafi da kuma muhalli
3. Yawaita shan ruwa musamman mai dan dumi
4. Barin shan taba ga wadanda suke smoking
5. Karancin shiga dandazon mutane musamman a lokaci irin wannan da ake sanyi don kiyaye yaɗuwar kwayar cutar.
6. Cin abinci mai inganci wanda zai habaka garkuwar jiki

Lafiyarka jarinka daga Pharmacist Kaameel Sani.

03/11/2024

NAFDAC Alerts Public on Recalled Nivea Deodorant Product Top Stories | Pharmanewsonline

03/11/2024

Bincike ya nuna cewa hanyoyi da ake bi don inganta lafiyar zuciya na taimakawa wajen inganta lafiyar ƙwaƙwalwa har ila yau. Wadannan hanyoyi sun hada da motsa jiki, barin shan taba, kula da hawan jini, cin abinci mai inganci samun ingantaccen barci, da dai sauransu.

Naku har a kullum, Pharmacist Kaameel Sani

Call now to connect with business.

Address

No. 13, Old Kano Road Azare
Azare
751101

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Pharm. Kaameel Sani Azare posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Share on Facebook Share on Twitter Share on LinkedIn
Share on Pinterest Share on Reddit Share via Email
Share on WhatsApp Share on Instagram Share on Telegram