09/01/2023
Hanyoyin Kiyaye Tashin Ciwon Gaɓoɓi Lokacin Sanyi
Ciwon gaɓoɓi lalurori ne da ke da tasirin gurgunta lafiya, ingancin rayuwa, walwala da tattalin arziƙin mutum. Akwai lalurori fiye da ɗari da ke da alaƙa da ciwon gaɓoɓi. Sai dai, akwai nau'in ciwon gaɓoɓin da s**a fi afkuwa a cikin al'ummar wannan yanki.
Lalurorin ciwon gaɓoɓi da s**a fi afkuwa sun haɗa da:
1. Amosanin gaɓa: ciwon amosanin gaɓa, wanda ake kira da "osteoarthritis" a turancin likita. Ciwon gaɓa ne sakamakon sauye-sauye da ke faruwa a gaɓa wanda ke janyo zaizayewar gurunguntsin gaɓa.
2. Ciwon sanyin ƙashi: ciwon gaɓa na sanyin ƙashi, wato "rheumatoid arthritis" a turancin likita. Ciwon gaɓa ne da ke afkuwa yayin da ƙwayoyin halittar garkuwar jiki, wato "immune cells", s**a rikice, a maimakon su yaƙi ƙwayoyin cuta da s**a shiga jiki sai su koma yaƙar ƙwayoyin halittar jiki.
3. Ciwon gawut: ciwon gaɓa na gawut, wato "gouty arthritis" a turancin likita, ciwon gaɓa ne da ke afkuwa idan sinadarin "uric acid" ya hauhawa fiye da ƙima a cikin jini, wanda hakan kuma ke haifar da taruwar gishirin "urate".
4. Harbin ƙwayoyin cuta: ciwon gaɓa ne sakamakon harɓin ƙwayoyin cuta kamar bakteriya, wato "septic arthritis" a turancin likita.
5. Ciwon gaɓa daga bugu: "traumatic arthritis", ciwon gaɓa ne sakamakon lahani ga gaɓa daga bugu, faɗuwa, faɗowa, haɗuran ababen hawa ko mummunan lahani daga wasannin guje-guje da tsalle-tsalle.
Alamomin Ciwon Gaɓoɓi
Alamomin ciwon gaɓoɓi sun haɗa da:
1. Ciwo a gaɓa
2. Riƙewar gaɓa
3. Kumburi a gaɓa
4. Wahala, kassarewa ko nakasar aikin gaɓa.
Alaƙar sanyi da ciwon gaɓoɓi
Da farko, a nan muna magana ne a kan sananniyar ma'anar sanyi, wato sanyi kishiyar zafi ko ɗumi. Wato kamar sanyi daga yanayin sanyi, ɗari ko hunturu, sanyin danshi ko laima, da kuma sanyin damuna ko sanyin fadama da dai sauransu.
Tashi ko ta'azzarar ciwon gaɓoɓi na daga cikin ƙorafe-ƙorafen da aka fi yi wa likita lokacin sanyi ko hunturu. Sai dai, kamar yadda muka fayyace bayani kan sabuban nau'o'in ciwon gaɓoɓi a sama, za mu ga cewa bayanin ya saɓa da tatsuniyar da ke yawo a cikin al'umma cewa sanyi ne sababin ciwon gaɓoɓin. Kamar yadda ake cewa, "tashi" ko "ta'azzara", wato ciwon gaɓoɓin daman yana nan sai dai sanyin ne kawai ke tayar ko ta'azzara shi.
To amma me ke janyo tashi ko ta'azzarar ciwon gaɓoɓi lokacin sanyi?
Har zuwa yanzu, a kimiyyance, ba a san haƙiƙanin sababin tashi ko ta'azzarar ciwon gaɓoɓi lokacin sanyi ba. Sai dai, ana alaƙanta tashi ko ta'azzarar ciwon gaɓoɓin da abubuwa kamar haka:
1. Raguwar zafi ko ɗumi a muhalli ko sararin samaniya.
2. Danshi, laima ko kaɗawar sassanyar iska a muhalli ko sararin samaniya.
3. Raguwa ko ƙarancin sinadarin bitamin D.
4. Gado: Mafi yawan mutane sun gaji ƙwayoyin halitta da ke tayar ko ta'azzara ciwon gaɓoɓi lokacin sanyi. Saboda haka, akwai mutane ƙalilan da sanyin ba ya tayarwa ko ta'azzara musu ciwon gaɓoɓi.
Hanyoyin kiyaye tashi ko ta'azzarar ciwon gaɓoɓi lokacin sanyi.
1. Sanya tufafi ko sutura mai kauri ko kuma a ninninka tufafi domin jiki ya kasance cikin ɗumi. Haka nan, ya kamata a sanya safar hannu da safar ƙafa da kuma sanya takalmi sawu-ciki domin kauce wa ratsawar sanyi.
2. Amfani da ruwan ɗumi yayin ayyukan yau da kullum, kamar: sha, alwala ko wanka. Haka nan, masu aiki ko sana'a da ruwa, za su iya zaɓar ruwan ɗumi ko kuma ɗumama jiki lokaci-lokaci a yini domin kasancewar jiki cikin ɗumi.
3. Hasken rana: Lokacin sanyi hasken rana a muhallahi na raguwa. Shi kuwa hasken rana muhimmin sinadari ne wajen samar da sinadarin bitamin D, wanda jigo ne wajen gina lafiyayyen ƙashi da kuma magance lalurorin da ke lalata ƙashi da gaɓa.
Yayin da hasken rana ya sauka a kan fatar mutum, fata na amfani da hasken ranar domin samar da sinadarin bitamin D. Saboda haka, akwai buƙatar shan hasken rana lokacin sanyi domin samun wannan alfanu.
Har wa yau, zai fi kyau a zaɓi awannin aiki lokacin da gari ya yi ɗumi idan hakan mai yiwuwa ne.
4. Ingantaccen abinci/abinsha: Cina 'ya'yan itatuwa, ganyayyaki da kuma datsar hatsi na samar da muhimman sinadaran kiwon lafiyayyen ƙashi da gaɓoɓi. Bugu da ƙari, rage siga a abinci ko abinsha da kuma rage sarrafaffun abinci ko abinsha na taimaka wa gaɓoɓi su zauna lafiya. Siga da sarrafaffun abinci ko abinsha na da haɗarin haddasa kumburi a gaɓoɓi.
5. Atisaye ko motsa jiki: Kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta ba da shawarar yin atisaye ko motsa jiki aƙalla na mituna 30 a kullum. Atisaye na taimaka wa jiki ya kasance cikin ɗumi. Kuma gaɓoɓin jiki za su kasance cikin lafiya da ingancin aiki yayin ayyukan yau da kullum.
Daga ƙarshe, idan kana fama da ciwon gaɓa, akwai buƙatar ganin likita domin gano sababin ciwon gaɓar domin bin hanyoyin magancewa dogaro da sababin ciwon gaɓar da likita ya gano.
©Physiotherapy Hausa