30/12/2025
SHAHADA INSHA ALLAH
Masu garkuwa da mutane sun kai hari wani gida a Pindiga, Karamar Hukumar Akko, Jihar Gombe ranar Lahadi da ta gabata
Wani matashi da ya yi kokarin kare kanwarsa an harbe shi kuma aka ¥anka shi har ya rasu, sannan kanwarsa mai suna Fa’iza an harbe ta tana dauke da juna biyu ita ma ta rasu
Bayan haka maharan sun sace 'yan mata biyu da marar lafiya, wadda rayuwarta ke cikin babbar barazana a halin yanzu.
Muna rokon Allah Ya karbi shahadarsu, Allah Ya tona asirin wadanda s**a aikata laifin