
08/05/2025
DA 1st CLASS NA GAMA JAMI'A:
Nayi photocopy na takardu na adadin da bazan iya tunawa ba, ina bayarwa sabida neman aiki amma har yanzu shiru don haka na yanke shawarar in fara soya wainar fulawa da awara tunda de aikin yazama sai kasan wani ba takardar ka ake dubuwa ba.
HABIBA USMAN. GARKUWA mace ta farko data shugabanci kungiyar dalibai yan asalin Jihar Kano a Jamiar Northwest University, Kano, kuma ta farko wacce tayi ayyukan dayafi kowanne shugabanci na dalibai haka kuma itace shugaba data fita da sakamako mafi daraja a 2024. yanzu haka Comrd. habiba garkuwa tarungumi sana'ar seda waina ta ajiye takardun karatunta na (Bsc. Ed. Biology) takama fulawa da waken suya. muna rokon masu madafun iko dasu bawa wannan Malamar aiki na koyarwa tunda de tasamu shedar karatu mai inanci domin ta amfanar da yara masu tasowa mai makon cika tumbin kwamarawa da wainar fulawa da awara.
Men
Me zaku ce?