05/09/2023
Falalar Tasbihi, Da Godiya Ga Allah, Da Yin La ilaha Illal Lah, da yin Kabbara, Da Istigfari, Da Tuba zuwa ga Allah.
بسم الله الرحمن الرحيم
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinqai.
Abu Huraira (R.A) ya ruwaito cewa; Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; wanda ya ce;
سُبْحَانَ اللهِ الْعَظِيمِ وَبِحَمْدِهِ.
Subhanallahil azeem wabihamdihi.
Sau dari (100) a rana, za a kankare masa zunubansa ko da sun kasance kamar kumfar teku ne (wajen yawa).
Abu Ayyub Al-Ansari (R.A) ya ruwaito daga Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, cewa ya ce: "Wanda Ya ce;
لاَ إِلهَ إِلاَّ اللهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ.
La ilaha illal-lahu wahdahu la shareeka lah, lahul-mulku walahul-hamd, wahuwa 'ala kulli shayin.
MA'ANA:
Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai; babu abokin tarayya a gareShi. Mulki ya tabbata gare Shi kuma Shi mai ikone a kan komai.
(Sau Goma).
To, kwatankwacin ladar su kamar mutuminda ya 'yanta bayi hudu ne daga cikin 'ya'yan (Annabi) Isma'ila.
Abu Huraira (R.A) ya ce; Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi, ya ce; "Akwai wassu kalmomi guda biyu masu saukin fada a harshe, masu nauyi a kan mizani (na ayyuka ranar al-Qiyama), masu soyuwa ga Allah mai yawan jin kai (su ne).
سُبْحَانَ اللهِ وَبِحَمْدِهِ سُبْحَانَ اللهِ العَظِيمِ.
Subhanal-lahi wabihamdih, wasubhanal-lahil-'azeem.
MA'ANA:
Tsarki ya tabbata ga Allah, tare da Shi; tsarki ya tabbata ga Allah Mai girma.
Abu Huraira (R.A) ya ce; "Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; Fadin:
سُبْحَانَ اللهِ، والْحَمْدُ للهِ، لَا إِلَهَ إلاَّ اللهُ واللهُ أَكْبَرُ.
Subhanal-lah, walhamdu lillah, la ilaha illal-lah wallahu akbar.
MA'ANA:
Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma yabo ya tabbata ga Allah, kuma babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Allah ne Mafi girma.
Sauran falalar tana a camment section🙏🙏👇👇👇👇kazo ka idasa ladarka . Alhamdulillah.