24/08/2021
CUTAR SYPHILIS!!!
Ciwon syphilis Yana daya daga cikin cutuka masu yaduwa ta hanyar saduwa wato Sexual Transmitted Infections (STI's) cuta ce da takan jawo illoli ga jiki dan harma takan kashe yaro a ciki ko ayi barinsa koma a haifeshi bakwaini, wato kafin lokacin isa haihuwa. Kamar yadda nai bayani cutar Syphilis cutace da ake dauka ta hanyar saduwa da wanda ke dauke da kwayoyin cutar, ko oral s*x, ko masu saduwa ta dubura. Sannan ita wannan muguwar cuta ta kan k**a wurare da dama a jikin dan Adam k**ar baki, harshe, cikin farji, tsakiya, da waje-wajen bakin farji, mahadar mahaifa, da kuma azzakari a maza. Saide zanyi magana ne akan syphilis wanda kan shafi gaban macen dana namiji. Ita wannan nau'in cuta ta Syphilis kwayar cuta ta bacteria ke haddasata mai suna; (Spirochete Bacterium Treponema Pallidum),
Ita wannan kwayar cutar tana da matukar illa ga rayuwa dan misali idan mace na dauke da ita bata sani ba to wajen haihuwa takan goga ma jaririn cutar ya zamto (Congenital Syphilis) ko kuma idan ta dade ba ai maganinta ba to takan wa yaron dake cikin illa ko ta kashe yaron ma k**ar yadda na fada.
ALAMOMIN SA Alamomin wannan cuta ta Syphilis, mata kaine guda 4, kuma kowanne alamun kan iya 6acewa ko warkewa ba tare da anyi magani ba alhalin kwayar cutar tana nan cikin jini.
MATAKI NA 1. A wannan mataki na cutar za'aga wani karamin kurji ma'ana {shanker} zagayayye daidai inda bacteria din ta shiga misali agansa akan zakarin ko farjin mace. Amman da andade zai tafi ba dole ma sai ansha magani ba.
MATAKI NA 2 a wannan mataki kuraje zasu bayyana akan fata marasa kaikayi musamman a tafin hannu da kafa, amman zasu iya fitowa ko ina ajika ba lallai se nan basu wadannan kurajen suna samuwa ne bayan sati 10 da shigar cutar, suma zasu iya tafiya ko ba a bada magani ba. Amman idan s**a taho warkewa suna fitar da alamu na ciwon makoshi, Gajiya, Ciwon kai da sauransu.
MATAKI NA 3 Yayin da alamun ciwon Syphilis na biyu ya tafi to akwai mataki naga ba wato {Latent stage} ma'ana.