14/03/2026
RAHOTON CIYARWAN YAUMUL IƊ'AM, QAFILATUL MAHABBAH DASS LOCAL GOVERNMENT BRANCH, 2026.
1- Abana ma kamar kowace shekara gidauniyar Qafilatul Mahabbah reshen karamar hukumar Dass ta sami daman gabatar da ciyarwan azumi na wannan shekara (2026) inda ta gabatar da ciyarwan ayammacin yau lahadi 14, March 2026 aɗakin taro na Bilyaminu othman multi-purpose town Hall.
2- Ayayin gabatar da wannan ciyarwa, gidauniyar ta samu gagarumin nasarar ciyar da mutane sama da ɗari biyu (200), karo na farko da gidauniyar ta samu damar ciyar da wannan adadi mai yawa a lokaci guda, lamarin daya nuna irin ci gaba da faɗaɗar ayyukan alherin da take yi a cikin al’umma.
3- Aɓangaren mutanen (Beneficiaries) da s**a amfana da wannan ciyarwa, suma sun nuna matuƙar farin ciki da godiya, tare da yabawa gidauniyar bisa wannan kyakkyawan aiki na tausayawa da taimakon jama'a datayi. Inda s**a bayyana cewa irin wannan shiri yana daga abinda yake taimakawa sosai wajen rage wa masu bukata wahala musamman a irin wannan lokaci na azumi, inda daga bisani s**a yi addu’o’i na musamman ga jagororin wannan gidauniya musamman jagoranta na ƙasa, wato PROF. IBRAHIM AHMAD MAQARI, wanda shi ne Babban Limamin National Mosque Abuja, inda s**a roƙi Allah (SWT) ya ƙara masa lafiya, hikima da basira tare da ba shi ikon ci gaba da jagorantar irin waɗannan ayyukan alkhairi da taimakon al’umma.
4- Daga ƙarshe, gidauniyar ta jaddada kudurinta na ci gaba da gudanar da shirye-shiryen taimako irin wannan, don cigaba da tallafa wa marasa ƙarfi da kuma ƙarfafa kwarin gwiwar al'umma wajen samar da tallafi dakuma abubuwa na taimakon juna a tsakankanin al’umma.
DAFATAN UBANGIJI ALLAH YA SAKA DA ALKHAIRI, GA DUKKAN MATAIMAKA DAKUMA WANNAN GIDAUNIYA BAƘI DAYA. 🤲✨
QAFILA MEDIA TEAM
✍️✍️14, MARCH, 2026