22/08/2025
Janar Mohammed Tanimu Abdullahi Ya Karɓi Ragamar Rundunar Yakin Intanet ta Sojin Najeriya
Daga Wakilinmu | Abuja | 22 ga Agusta, 2025
A ranar Juma’a, 22 ga watan Agusta, 2025, an gudanar da bikin mika mulki a rundunar Nigerian Army Cyber Warfare Command (NACWC) dake Abuja, inda Manjo Janar Mohammed Tanimu Abdullahi ya karɓi ragamar jagorancin rundunar a matsayin kwamanda na 6.
A yayin bikin, tsohon kwamandan rundunar, Manjo Janar Ayannuga, ya godewa Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, tare da godewa Allah bisa damar da aka ba shi na jagorantar rundunar. Haka kuma, ya yabawa jami’an sojoji da ma’aikatan farar hula na NACWC bisa goyon baya da s**a bashi, inda ya roƙe su da su ci gaba da bayar da irin wannan haɗin kai ga sabon kwamandan.
Bikin ya haɗa da sanya hannu kan takardun mikawa da karɓar aiki, sanya sabuwar alamar rundunar ga Manjo Janar Abdullahi, da kuma jawabin bankwana.
Haka zalika, an miƙa sabuwar tutar rundunar ga sabon kwamandan, wacce aka daga a wajen Quarter Guard a matsayin alamar sabon shugabanci.
Wannan sauyin jagoranci na daga cikin muhimman matakai a tarihin rundunar NACWC, inda ake sa ran Manjo Janar Abdullahi zai gina kan nasarorin da aka samu a baya tare da ɗaukar rundunar zuwa sabon mataki.
Hotuna 📸 Nig Army