23/10/2023
*Ido baiwa daga Allah sarkin iya halitta. Har yau duniyar science ta kasa yin artificial eye don mayarwa ko dashe idan na wani ya mutu ko ya lalace.
*Yana da kyau mu kula da idanun mu sosai don ba'a samun sifayafat (spare part) in ya lalace.
* Ko kasan sanya Tabarau yayin hawa babur, keke, mota budaddiya yana kare mana idanu sosai da sosai! Haka ma lakacin tsananin rana??
*Ina masu saran Bishiya?
Yana da matuƙar kyau ku na sanya tubarau din ku don kare idanun ku,. Sautari muna samun mara sa lafiya da a sanadiyyar saran itace idanun su sun lalace gabadaya
*Ina Malaman makarantu (Islamiyya, Boko da Tsangaya da sauran su?
Mu guji marin yara ko dukan su a fuska, hakan yana taimakawa wajen tabbatar da lafiyar idanun su, don sune manyan gobe
* Ina manoma yan uwana?
Ko kun san yin feshin maganin kwari, ko kashe chiyawa ba tare da sa kariya a ido ba yana da hatsari sosai??
Hakika sanya shield 🛡 irin Wanda aka yi amfani dashi lokachin Corona Virus yana da matuƙar amfanin gaske. Ko kuma ka nemi farin Tubarau ɗin ka ka makala a idanun ka.
* Ina Masu amfani da wayoyi, cumputers, Tvs, Games??
Ku tabbata kuna rage hasken wayar ku ko TV 📺 din ku musamman da daddare. Ku riƙa sanya alamar dare dake jikin wayar ku, ko laptop ɗin ku, Ko kuma duk wata na'urar mai fidda haske. Hakan yana sanya idanun mu su zauna lafiya tsawon lokachi.
*A sami lokachi ana zuwa asibitin Ido akalla sau daya duk bayan wata shidda don gwajin Glaucoma, Cataract (Yana) da sauran su.
Shi ciwon Galuacoma (jawan-jinin ido) ba a gane shi idan ba gwaji aka maka ba. Daga lokachin da ya bayyana kansa a jikin ka, to ya fara maka illa.. Gadon sa ake yi daga iyaye, kunga yana da kyau a samu lokachin don dubawa.
*idan akwai tambaya, mu hadu a comment section.
*Good Night. Sweet dreams.
Remember : Lafiya Uwar jiki...