20/09/2025
Pelvic organ prolapse( POP )
Kashi na daya
MENENE POP ?
POP shine zazzagowan mahaifa ko mafitsara ko kuma wa wani bangare na babban hanji ko ƙaramin hanji cikin gaban mace.
TYPES (KASHE KASHEN ) POP
1. Anterior vaginal: Shi kuma ya kasu kashi biyu. (a) Urethrocele shine zazzagowan hanyan fitsari ta bangon gaban mace ta gaba
(b) Cystocele shine zazzagowan rumbun adana fitsari ta gaban mace.
2. Posterior vaginal shima wannan ya kasu Kashi. (a) Rectocele: Shine zazzagowan babban hanji ta gaban mace . (b) Enterocele shine zazzagowan ƙaramin hanji ta gaban ce.
3. Uterovaginal prolapse: shine zazzagowan mahaifa ta gaban mace.
YA ZA'AYI MACE TA GANE TANADA PELVIC ORGAN PROLAPSE (POP) ?
1. Daga farko mace tana fara jin shi ne a cikin gaban musamman a lokacin da tazo fitsari
2. Wasu kuma in sun sa hanu ne a cikin gaban nasu suke iya tabo mahaifar tasu ko kuma mafitsarar tasu.
3. Wasu kuma a Lokacin da suke fitsari ne suke Ganin wani abu kaman tsoka ya fito musu a gaba, sai ya koma bayan sun gama fitsarin daga baya kuma yazo baya iya komawa, yana kara girma har mahaifar ko rumbun fitsarin ta fito waje gaba daya.
4. Wasu kuma na iya samun daya ko fiye da haka daga cikin wadannan matsaloli da zan ambata; zuban jini ta gaba, zubar da ruwa mai wari ta gaba, zafi Lokacin saduwa, zafi yayin fitsari, yawan fitsari, rashin iya riƙe fitsari, ciwon mara, kumburin ciki ta qasa da dai sauransu.
MEKE JAWO PELVIC ORGAN PROLAPSE ?
YA AKE MAGANIN PELVIC ORGAN PROLAPSE?
YA MUTUM ZAI KARE KANSHI DAGA SAMUN PELVIC ORGAN PROLAPSE?
Duk mai bukatan amsoshin wadannan tambayoyi ya biyo mu a KASHI NA BIYU a wannan shafi Lafiya Uwar JIKI
Wanda kuma ya sani ya sa mana a comment.
Bisaalam.