02/03/2025
Alhamdulillah, Allah ya kawo mu wata mai daraja, wata na Ramadan, wata da ake bukatar kame kai da tsarkake zuciya. Daga cikin manyan abubuwan da ake bukatar kiyayewa ga masu aure a wannan wata shi ne nisantar juna da rana, domin kada azuminsu ya lalace.
Hukuncin Yin Jima’i da Rana a Ramadan
Allah ya hana jima’i da rana a watan Ramadan, kuma duk wanda ya aikata hakan ya yi babban kuskure tare da karye dokar Allah a cikin Al-Qur’ani Allah yace:
“An halatta muku jima’i da matayenku a daren azumi; su abokanku ne, ku kuma abokansu ne. Allah ya san kun kasance kuna yaudarar kawukanku, sai ya karɓi tubarku, ya gafarta muku. To, yanzu ku sadu da su, ku nemi abin da Allah ya rubuta muku (wato ’ya’ya). Kuma ku ci, ku sha, har farin zare ya bayyana muku daga bakin zare (wato alfijir), sannan ku kammala azumi har zuwa dare…” (Suratul Baqarah: 187)
Daga wannan aya, zamu fahimci cewa yin jima’i da dare a ramadan, amma haramun ne ba laifi bane. Bayan an sha ruwa namiji zai iya sadu da matarsa har zowa lokacin da za a yi suhur.
Hukuncin Wanda Ya Yi Jima’i da Rana a Ramadan
Idan miji da mace sun yi jima’i da rana a watan Ramadan, to:
1. Azuminsu ya karye, dole su rama azumin ranar.
2. Dole su yi kaffara (wanda ya fi rinjaye akan miji ne, •Zai yi azumi tsawon kwanaki 60 a jere.
•Idan ba zai iya yin azumin ba saboda rashin lafiya ko wani uzuri, sai ya ciyar da miskinai sittin (60).
•idan yana da iko, zai ’yanta bawa, amma yanzu ba a yin hakan saboda babu bawa.
Dalili: Wannan hukunci ya fito daga hadisin Abu Hurairah (RA), inda wani mutum ya zo wurin Manzon Allah (SAW) yana cewa ya aikata jima’i da rana a Ramadan, sai Manzon Allah (SAW) ya ce masa ya ’yanta bawa. Idan ba zai iya ba, sai ya yi azumi kwanaki 60 a jere. Idan ba zai iya ba, sai ya ciyar da miskinai sittin. (Bukhari da Muslim)
Yadda Ma’aurata Zasu Nisanci Juna da Rana
✅ Ka nisanci kusantar juna da rana – Kada a rungumi juna ko a zauna a wuri ɗaya da zai iya tada sha’awa.
Duk da cewa idan an yi hakan ba laifi b