Lambun Ma'aurata

Lambun Ma'aurata Shafi ne domin tattaunawa kan matssalolin zamantakewar aure da nufin gano bakin zaren wajen warwarewa

Wani magidanci ne yace da matarsa yana ƙaunarta ɗari bisa ɗari.Ita kuwa gogar taku sai ta kada baki tace: " Ai sai dai n...
04/08/2025

Wani magidanci ne yace da matarsa yana ƙaunarta ɗari bisa ɗari.

Ita kuwa gogar taku sai ta kada baki tace: " Ai sai dai na samu kaso 25%"

Da ya tambayeta ko mene ne ɗalili sai ta ce: ai mata ne kawai suke iya son namiji 100%, amma shi namiji ai mijin mace huɗu ne!

Shin kun yarda da wannan azanci na matar nan kuwa?

Sai mun ga ra'ayoyinku.a sashen sharhi.

Wannan matar wani gwamna ce a jihohin Arewa. Amma ga ta nan ta duƙufa a madafa tana aikin miji. Ko dan ita bata taɓa cin...
31/07/2025

Wannan matar wani gwamna ce a jihohin Arewa. Amma ga ta nan ta duƙufa a madafa tana aikin miji. Ko dan ita bata taɓa cin pizza ba ne oho!

Hukuncin Ado da Kwalliya a Musulunce"Wanda duk yayi kamanceceniya da wasu mutane, to yana cikinsu"A ƙa'ida sananniya ta ...
31/07/2025

Hukuncin Ado da Kwalliya a Musulunce

"Wanda duk yayi kamanceceniya da wasu mutane, to yana cikinsu"

A ƙa'ida sananniya ta ado da kwalliya a addini.Musulunci, duk wata shiga ko wani.na'u'in ado da ake siffanta gungun wasu.fajirai da.shi., to wannan abin ya zama haramun.

A zamanin baya yin shasshawa.da.zane-zane a fuska kamarnsu kalamgi, ba wani laifi bane, hasalima sai ƴar gata ake yiwa. Amma daga lokacin da kilalai s**a ara.s**a yafa akan yin kalangu, har ma.s**a.mayar da.shi wani.signboard, to daga lokacin ne kuma duk mutanen kirkims**a.dawo.daga rakiyarsa aka bar musu kayansu.

Idan sanya zobe a hanci daman can al'adar garinku.ce ki.cigaɓa da sanyawa. Amma idan sai bayan fasiƙan.Tiktok sun fara.yin signboard da shi kika fara sha'awa, to gaskiyar magana bisa ga waɗancan.ƙa'idoji da hukunce-hukuncen sanya tufafi da kwalliya a Musulunci, to aikata hakan ya zama. haramun!

Mutuwar Yawa........Idan kika biyewa zancen ƴan rajin kare haƙƙin mata, to kema haka nan za ki tsofe a waje, babu ko mas...
24/07/2025

Mutuwar Yawa........

Idan kika biyewa zancen ƴan rajin kare haƙƙin mata, to kema haka nan za ki tsofe a waje, babu ko mashinshini, wadda ke ɗakin mijin kuma so suke su ga ta fito waje domin su ƙara yawa.

Ai daman ance mutuwar yawa kaka ce.
Don haka ƴan uwa mata, ayi hattara da wakilan sheɗan masu hurewa mata kunne da sunan ƴanci da kuma wayewa.

Allah ya tsare mu daga faɗawa tarkon mayaudara.

24/07/2025

Ya ruwa yan uwa?
Kwana biyu mun shiga rububi ne.
Da fatan za a dakace mu.

"Kada ka taɓa barin ƴarka da shaƙu da wani saurayi" Wannan maganar da ke sama ta Sheikh Daurawa ce. Ya yi wannan maganar...
08/07/2025

"Kada ka taɓa barin ƴarka da shaƙu da wani saurayi"

Wannan maganar da ke sama ta Sheikh Daurawa ce. Ya yi wannan maganar ce saboda irin yanda suke yawan samun ƙorafe-ƙorafen iyaye a Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, kan yanda yara mata kan bijirewa iyayensu akan saurayin da s**a riga s**a shaƙu kuma ake son raɓa su.

Akwai mataye da yawa da ba sa iya rabuwa da waɗannan samarin koda kuwa da auren wani akan su. Wannan wani babban hatsari ne da wannnan al'ummar tamu ke fuskanta wanda kuma ba zai taɓa haifar mana da ɗa mai ido ba.

Idan kuna bibiyar labarai kun ji, yanda a mako da ke ƙarewa aka samu wasu matasan da s**a aurar da kan su saboda iyayen saurayin ɗsn shekara 21 sun ce bai isa aure ba, shi kuma ya ƙagu, don haka s**a shirya aurenau da gangan da amaryarsa ta bogi ƴar shekara 16.

Ire-iren waɗannan ƙorafe-ƙorafen na nan ba za ma su kirgu ba. Wasu ma tuni sun daɗe da sanin menene auren tun suna da ƙananun sheƙaru. Suna ta tafka masha'a kuma saboda sakacin iyayen ba su ma san me ya ke gudana tsakanin su ba, har sai abun kunya ya bayyana sannan a fara zance ta karkata kai.

Ya kamata iyaye su ƙara bayar da himma wajen kiyayewa da duk kiwon da Allah SWT ya ba su, domin su ɗin ababaen tambaya ne abisa kiwon da aka basu.

Allah ya kare mana xuriyar mu daga faɗaea cikin fitintunun wannan zamanin, waɗanda kuma s**a riga s**a faɗa tarkon sheiɗan Allah ya shirye su.

Da me ka dinga tallafawa matarka a lokacin da ta haifi tagwaye? ゚  ゚
01/07/2025

Da me ka dinga tallafawa matarka a lokacin da ta haifi tagwaye?

゚ ゚

Wace hanya ce mafi sauki domin magance fitsarin kwancen yara? ゚        ゚
30/06/2025

Wace hanya ce mafi sauki domin magance fitsarin kwancen yara?

゚ ゚

29/06/2025

Wace dabara ki ke yiwa yaro mai kukan dare, don yan uwa su amfana?

28/06/2025

Wadda ba ta taba yin yaji ba ta daga hannu!

Address

Nasarawa GRA
Gra

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Lambun Ma'aurata posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Practice

Send a message to Lambun Ma'aurata:

Share

Share on Facebook Share on Twitter Share on LinkedIn
Share on Pinterest Share on Reddit Share via Email
Share on WhatsApp Share on Instagram Share on Telegram