09/04/2025
Muhimmancin Yawan Shan Ruwa Ga Lafiyar Ƙoda, Ku Kiyaye Kuɗin Magani!
Ƙoda na ɗaya daga cikin muhimman sassa a jikin ɗan adam, domin suna tace jininmu daga gubobi da fitar da su ta hanyar fitsari. Sai dai da yawa daga cikinmu ba ma kula da lafiyar ƙoda har sai mun fuskanci matsala, daga abinda ke jawo matsalar ƙoda musamman itace rashin yawan shan ruwa.
Shan ruwa mai yawa yana taimaka wa ƙoda wajen aiki yadda ya kamata. Idan baka shan ruwa sosai, fitsarinka yana ƙara ƙwari, abinda zai cutar da jikin ka na taruwa a jiki, kuma hakan na iya haifar da cututtukan ƙoda kamar kidney stone ko kidney failure. Wadannan matsaloli kuma suna buƙatar kulawar likita wanda hakan yana da tsada sosai.
Yanzu haka, farashin magani da jinyar ciwon ƙoda ya yi tashin gwauron zabi. A wasu asibitoci, ana kashe dubban kuɗi har zuwa miliyoyi wajen yi wa marasa lafiya dialysis ko ma dashen ƙoda (kidney transplant). Wannan ba abu ne da kowa zai iya daukar nauyin sa ba.
Amma da ruwa kawai za ka iya kare kanka daga hakan. Ka tabbata kana shan aƙalla glass 8 zuwa 10 na ruwa a rana. Musamman a wannan lokaci na zafi ana son kake shan ruwa sosai. Musamman kuma da bayan motsa jiki.
A duk lokacin da kaga fitsarinka ya yi duhu ko yellow, ko ya yi wari, hakan na iya nuni da ƙarancin shan ruwa da kakeyi.
Lafiya na da daraja fiye da dukiya. Shan ruwa bai da tsada, amma rashin shansa na iya kai ka ga kashe dukkan abin da ka tara. Ka fara yau, ka kare ƙodarka, ka ceci kuɗinka.
Kar ka yarda masu kuɗi su fika kuɗi da cin abu mai daɗi, sannan su fika yawan shan ruwa.
Farashin dashen koda a Najeriya yana da tsada sosai. A wasu asibitocin gwamnati, ana kiyasta farashin tsakanin Naira miliyan 9 zuwa Naira miliyan 15. A asibitocin masu zaman kansu, farashin na iya kaiwa har Naira miliyan 20 zuwa Naira miliyan 25. Wadannan farashin sun hada da aikin dashen koda da magungunan da ake bukata bayan aikin.
Da yawan shan ruwa da zamuke yi, zamu taƙaita riskin kamuwa da wannan cuta In shaa Allahu.