Faroukh creative smiles dental & health care business services

Faroukh creative smiles dental & health care business services Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Faroukh creative smiles dental & health care business services, Medical and health, AR. 23 Dokaji Street, Kaduna.

26/10/2021
be less invasive .....Bonding of a fractured Fragment
11/06/2021

be less invasive .....Bonding of a fractured Fragment

π€π‹π€πŒπŽπŒπˆπ π‚πˆπ–πŽπ π‡π€πŠπŽπ‘πˆWadannan duk abayyane suke sun kuma hada da: kumburi, yawan dalalar ko taruwar miyau, jin zogi wand...
01/05/2021

π€π‹π€πŒπŽπŒπˆπ π‚πˆπ–πŽπ π‡π€πŠπŽπ‘πˆ

Wadannan duk abayyane suke sun kuma hada da: kumburi, yawan dalalar ko taruwar miyau, jin zogi wanda ke kuΙ—a har kunne ma ake jin ciwon, haka jin zogin ciwon har wuya, wahalar hadiyar abinci, zafi yayin tauna, zafin yayin waige, ko hakori yake ruwa, nauyin numfashi, da warin numfashi... duk ciwon hakori na haddasa wannan.

Haka sensitivity wato inkasa abu mai sanyi zakaji ya dau kuΙ—a, ko kuma inka bude iska ta shiga da kaluluwa a kasan mukamiki.

Ciwon hakori tare da zazza6i lokaci guda yana nuna yanzu haka kwayoyin cutar suna kan aikinsu ma, kamar kurace ke cin barewa da ranta batare data kashe ba.. shyasa bazaka daure azabar ba.

Haka jin kaluluwa a mukamiki na sanar da likita yiwuwar kwayoyin cutar sun shiga jijiyoyin jini dole yaima systemic treatment wato kada tunanin magani ya tsaya ga hakori kurum duk sauran sassan jiki ta shafesu... domin gudun abunda kwayoyin cutar zasu iyayi. Rashin sanin hakan kunga ai illah ne, shyasa aiki sai mai shi, inkaga case yafi karfinka matsayin karamin jami'in lafiya maza tura mutum ga manyan likitoci a asibitin gaba.

:::::::::::::::::::::::::::●●5●●::::::::::::::::::::::::::::

πŒπ„πŠπ„ 𝐍𝐔𝐍𝐀 πŒπ”π“π”πŒ π™π€πˆ πˆπ˜π€ 𝐇𝐀𝐃𝐔𝐖𝐀 𝐃𝐀 π‚πˆπ–πŽπ

β–  Karancin tsaftar baki da hakora wato "poor dental & oral hygiene" gaskiya shine kan gaba. Kamar yadda nasha fada kurum kurkure baki bashine tsafta ba, hatta yin brush fa kwai yadda akeyi sai ankoya. Sannan bayan angoge sai ankoyi sa zare ana sakuce space din tsakanin hakora, shyasa ynxu duk sabon gidan brushi ake saka wata yar karamar roba mai kamar igiyar robe ta sakuce tsakanin hakori... saboda cire abincin da ya makale wanda inba haka kwayoyin cuta sun sami mazauni.

Haka koda an iya brush to yinsa sau 1 ayini yai kadan ya samar da tsaro ga hakora.

β–  Yawan shan zaΖ™i, kamar yadda na fada asama: su soft drinks, cokes, maltinas, chocolate, alawa, mazarkwaila, tea, rake, da duk wani abu me zaki. Mutum mai ta'ammali dasu tunma bamai tauna sweets ba zai iya wayar gari da kogon hakori wato cavities. Shyasa ko yara aka fiye basu kayan zaqi batare da kamasu awanke musu baki ba za aji suma bakinsu na ďoyi ko cin zanza.

β–  Bushewar baki kila sanadiyyar wani magani da aka rubutawa mutum yake sha, ko kuwa barinsa abushe ya zamto mutum baya shan ruwa akai akai, musamman a tsoffi wannan yafi.

Amma de adunkule gaskiya ciwon hakori karan cin tsaftar baki ne. Don haka dole mutum ya lura inyanason cetonsu.

:::::::::::::::::::::::::::●●6●●::::::::::::::::::::::::::::

πŒπ€π†π€ππˆπ π‚πˆπ–πŽπ

β–ͺ︎ Idan akwai zazza6i, za aba mutum maganin zazza6i wato Antipyretics musammsn fitacce wato: Patacetamol.

β–ͺ︎ Idan akwai zogi za'a ba mutum maganin zogi wato anti inflammatory gasunan birjik irinsu: Aspirin, cafenol, feldin, diclofenac, ibuprofen, Novalgin, mefenemic da sauransu.

Amma de asani rukunin Anti inf. suna kunshe da caffeine don haka gamai ulcer ya kwan da sanin zasu iya tayar da ita koma susa mutum inyai amai yaga jini.... saide ciwon hakori alokacin ya danne azabar ulcer dinne. Wato benefits outweighs risk, amma de likitan da kagani shi yasan plan din da ya dace dakai.

Shin za'a iya hada paracetamol da anti inflammatory musamman in akwai zazza6i amsa eh.

β–  Anti biotics; tunda munji bacteria din kai tsaye rukunin maganin da zai kasheta za aba mutum, domin ba duk antibiotic ne zai kasheta ba sai wanda zai iya yunwatar da ita, ya fasa jikinta, ya toshe mata hanyar numfashi ta mutu. Antibiotic ba OTC bane don haka doka ne ambatar sunan antibiotics a post. Sai anje ga likita shine zai duba abunda ya dace da mutum.

β–  Neurogesic ko opiods rukunin magunguna masu karfi idan duk wadancan na rage zogin basui aiki ba shine likita ke badasu.. wasu kuma na shafawane ta waje ko fesawa acikin hakorin.

β–  Sai kuma in kogo ne yai zurfi toh ana iya cikesa.

β–  Idan kogon yai zurfi sosai kuma ya zamto duk an cinyesa toh anan ko an cikesa idan likitan hakori yaga cikewar na iya sa cigaba da jin zafi toh CIRE hakorin yafi cikon. inajin inda ake samun sa6anin shawara kenan wasu ke cewa bayan an musu ciko zafi ya rikayi har saida aka cire hakorin.... dama yai mutuwar da ciresa shine abunyi ba ciko ba.

β–  Kurkure baki da ruwan dumi me gishiri agida na taimakawa wajen rage kwayoyin cutar da kuma zogi. Duk sanda akaci wani abu koda sau nawa ne toh da an gama kar azauna, maza asami ruwan dumi akurkure... hakan koda da kogo zai hana kumewa da kumburin gurin.

β–  Rage surutu musamman a irin wannan lokaci na sanyi na rage zogi da azaba. Gami da cin abu me ruwa ruwa.

β–  A kuma yi hakuri da kwanciya a siminti mai sanyi, ko cikin Ac ko shan drinks masu sanyi da kankara irinsu yoghurts.

β–  Sannan baya ga hakorin in likita ya lura da wata matsalar to nan ma yana iya karawa da magungunan da s**a dace walau supplements irinsu vitamin c & b- complex, antideppressants ko steroids

β–  Matukar ba acike kogon nan ba zaka iya shekara 10 kana yi domin bacteria din taita dawowa kenan tunda magani kurum kakesha ba'a kiyayewa. Idan duk anyi anyi yaki dena ciwo toh ko babu kogo kaje kaga likitan hakori ku tattauna yiwuwar cire kurum. Amma de kar a manta a kar6i prophylaxis na Amoxicillin na tsawon kwana 14 kafin acire tunma ba inyana ruwa ba.

β˜† Kar a manta shan magani zogi baya maganin ciwon hakori saide adena jin zafi na dan wani lokaci amma zai dawo. Dole ahada da maganin da zai kashe giram neegetib da fozitib baki daya.
:::::::::::::::::::::::::::●●7●●::::::::::::::::::::::::::::

πŒπ€π“π€πŠπ€π πŠπ€π‘πˆπ˜π€

1. Lura da tsaftar hakora shine mahimmi. Don haka inkana kokonto game da yadda ake brush ka daure ka ware lokaci minti 5 kacal ya isa ka bude YOUTUBE kai saearching video akan How to properly brush your teeth.

2. Bayan ka iya ko ka koya toh Mafi karancin shine ka goge baki sau 2 arana, mafi inganci sau 4 ko duk bayan gama cin abinci.

3. Yayin goge baki in angoga makilin to ba nan da nan ake kurkurewa ba, dole ajira minti 2 zuwa 5 abari fluorides din makilin din yai aikin kashe kwayoyin cutar inba haka ba koda angoga brushi yadda ya dace baza akashe komi ba, kuma hakan bazai hana hakora ciwo ba.

4. Ake amfani da dental floss ko interdental cleaner ana tsefewa ko sakace tsakanin hakori. Saboda wannan ma mahimmi ne, galibi ta inda bakteriya din ke fara samun mazauni kenan

5. Kada abubuwa masu suga suke zamtowa a abincinka na karin kumallo da kuma na karshe aanda daga shi sai bacci. Akuma rage cin zaki ko tauna abubuwa masu zaki ko sha... ko don gudun ciwon suga.

6. Shi kansa brush akwai bukatar koda sati sati ake tsomashi aruwan dumi yadan dahu saboda bakteria din. Sannan kusani brush na expire a wata 3 ne inde kullum ana amfani dashi. Don haka duk wata 3 zuwa 4 ake canza sabo. Wasu sai subar brush ya shekara ma.... habaa kuskure ne.

β–  Sannan arika zuwa wankin wankin hakora haka kurum koda basa ciwo akalla duk wata 6 hakan zaisa agani matsala da wuri in akwai. In babu kuma zaisa karin lafiya bama ta baki ba har idanu da kwakwalwa da kunnuwa.

Kuyi hakuri naci lokacinku da yawa wajen karatu, fatana Allah sa kun ilmantu.

::::::::::::::::::::::::::::●●●●:::::::::::::::::::::::

Happy New year my colleague wishing you long life and prosperity in this year and happy survival from the year that have...
03/01/2021

Happy New year my colleague wishing you long life and prosperity in this year and happy survival from the year that have a lot of challenge πŸ™

Once the outside hospital announced that the implanted teeth were to be removed, we chose the replantation technique, re...
04/12/2020

Once the outside hospital announced that the implanted teeth were to be removed, we chose the replantation technique, re-implanting after resin restoration and root canal filling. After 2 months, the looseness of the tooth was less than 1 degree, and the resin filling part of the distal tooth was covered by the gum, no obvious discomfort to the teeth

full protocol for class 1 compositepractice time 😍πŸ”₯i hope you like it ❀
02/12/2020

full protocol for class 1 composite
practice time 😍πŸ”₯
i hope you like it ❀

30/11/2020

Welcome to the page of Faroukh creative smiles dental & health care business services - where you’re not just a patient. You’re family!

Address

AR. 23 Dokaji Street
Kaduna

Telephone

+2348071341755

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Faroukh creative smiles dental & health care business services posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Practice

Send a message to Faroukh creative smiles dental & health care business services:

Share