10/02/2023
YAWAN FITSARI [POLYURIA]
┈┉┅━━┅┉┈┈┉┅━━┅┉┈
Kwai abube da dama dakan iya kawo yawan fitsari k**a daga canjin yanayi, zuwa yawan shan ruwa ko kayan shaye-shaye na lemuka, samuwar juna biyu, rashin lafiya zuwa amfani da magunguna.
Yawan fitsari na faruwa yayin da mutum yaga cewa yawan zuwa bandaki domin fitsari ya ƙaru, ko yawan fitsarin dake zuba ya karu koda bai samu ƙaruwar zuwa bayan-gidan ba. Wasu kan tsuguna fitsari har kafarsu ta fara gajiya batare da sun gama ba.
Canjin yanayi daga na zafi zuwa na sanyi zai iya kawo yawan fitsari saboda tsokar dake rike da marar takan saki kaɗan.
Yawa anan na nufin zubar fitsari mai yawa ba kadan ba. Yawan shan abubuwa masu ruwa ma kan iya kawo irin wannan yawan.
Mai juna biyu ma da yafara girma wata 4 zuwa sama zata rika jin fitsari a kai-akai saboda mahaifa na danno mafitsara ballantana wacce ta tafi wata 7, 8 zuwa wata 9 na haihuwa saide zatake fitsarin ne kaɗankaɗan ko yaya ya taru bazai riƙu ba.
Sai rashin lafiya k**ar yadda ana ganin shigar kwayoyin cuta mafitsara (Urinary Tract Infection) kan iyasa yawan fitsari, amma anan yawan na nufin yawan jin fitsarin don ko anje ba'a ganin yana zuba da yawa.
Wani ciwo mai kawo irin wannan alama kuma shine na kumburin prostate a maza wadanda s**a manyanta da kuma toshewar mafitsara daga can ciki wacce ke dauko fitsari daga ƙoda shine kan gaba wajen jawo fitsari ɗiris-ɗiris (BPH).
Sai matsalar ciwon suga (diabetes) wadda ita kuma zata iya kawo yawan yin fitsari a kai-akai musamman da daddare kuma mai yawa ba kadan-kadan ba.
Sai matsalar ciwon koda k**ar yadda nace ita ma za ta iya kawo yawan fitsari kafin daga bisani ya dauke a wasu lokutan.
Daga karshe sai wasu rukunin magunguna wato magungunan da akanba wasu wadanda ruwa ko kumburi ya bayyana a jikinsu k**ar masu hawan jini, ko masu ciwon hanta, ciwon zuciya, ciwon ƙoda duk s**an iyasa yawan fitsari.
Akwai wasu na gargajiya ma wadanda mutum kan saya yasha haka nan a t**i suma zasu iya kawo yawan fitsari suma.
Don haka duk wanda yake da alamomin yawan fitsari bana canjin yanayi ko na shaye-shaye ba yana da kyau yaje aduba shi inta k**a ayi masa gwaje-gwaje don a tantance matsalar.
Musamman mai yawan tashi fitsarin dare, yawan jin kishirwa, saurin Jin yunwa, jin alamun ƙiba ko ƙarin nauyi, rashin karfin mazaƙuta, ganin Jiri ko jin ƙafafu nayin dindiris ko su riƙa ciwo-ciwo ko ganin ciwo na daukar dogon lokaci kafin ya warke hakan duk ka iya zamowa daga alamuna ciwon suga. Ai kokari aga likita
✍🏻
(Ibrahim Y. Yusuf)