Albarkan Allah Dental & health care Service

  • Home
  • Albarkan Allah Dental & health care Service

Albarkan Allah Dental & health care Service prevention is better than ..........

23/09/2025

Malamin Gona
(Kashi Na-73)

Cutar Tushen Yabanya
(Root Diseases)

A wani ƙauye mai nisa, akwai wata yarinya mai suna Zainabu.

Ita yarinya ce wadda take son noma shinkafa da wake tare da mahaifiyarta.

Amma a wannan shekara, gonar wake ta fara nuna alamu na rashin lafiya.

Zainabu ta lura:
* Ganyen wake sun fara yin rawaya.

* Wasu tsirrai sun tsaya cak ba su ƙara girma.

* Wasu kuma sun fara bushewa duk da ruwan sama yana yawan sauka.

Sai ta tambayi mahaifiyarta:
“Ummana, me ya sa wakenmu ya yi rauni haka?”

Mahaifiyarta ta ce:
“Zainabu, idan ganye ya canza, idan tsiro ya tsaya, to tushen ne ya faɗi gaskiya. Mu je mu tono mu duba.”

S**a tono tushen tsirrai. Sai s**a gano:

* Tushen ya kumbura kamar ƙwai (root galls):
Mahaifiyarta ta ce: “Wannan alamar ƙwari nematodes ne s**a shiga, suna shan jinin tsiro.”

* Tushen ya ruɓe, ya yi baki (root rot):
Ta ce: “Wannan kuwa fungi ko bacteria ne, suna sa tsiro ya ruɓe daga ƙasa.”

* Tushen ya yi ƙanƙanta, bai bazu ba:
Ta ce: “Idan tushen bai bazu ba, tsiro ba zai iya shan ruwa da abinci ba. Wannan rashin sinadarin ƙasa ne ko ƙasa ta yi tauri.”

* Tushen ya bushe gaba ɗaya:
Ta ce: “Idan haka ta faru, to ruwa bai kai masa ba ko kuma cutar wilt ta toshe jijiyoyinsa.”

Zainabu ta yi mamaki ta ce:
“Toh, kenan tushen yana magana ne, amma sai wanda ya iya karantawa zai gane?”

Mahaifiyarta ta murmusa ta ce:
“Haka ne. Tushen tsiro littafi ne, yana gaya mana sirrin cuta. Idan muka duba da hankali, ba za mu rasa mafita ba.”

Za mu fahimci cewa;

* Tushen tsiro yana bayyana cututtuka ta hanyoyi daban-daban.

* Ganewar cuta daga tushen yana taimaka wa manomi wajen gano matsala tun da wuri.

* Idan aka kula da tushen, tsiro zai girma lafiya.

Domin Karin Bayani ko Shiga Shafinmu na WhatsApp 07032596712

WARI KO HAMAMIN BAKI {MOUTH ODOUR} ┈┉┅━💚💕💗💕💚━┅┉┈Warin baki abu ne me wuyar faɗi ga aboki ko wani da ake jin nauyinsa, to...
19/01/2025

WARI KO HAMAMIN BAKI {MOUTH ODOUR}
┈┉┅━💚💕💗💕💚━┅┉┈

Warin baki abu ne me wuyar faɗi ga aboki ko wani da ake jin nauyinsa, toh saide dole akwana atashi mutum zai san yana dashi domin wasu baza su iya kauda kai ba sai sun faɗama cewa kana dashi, wani kuma Kaine zaka laqanta inkana magana Kaga ana kau da kai,

Kwai lokutan da dole akan ɗanji baki ya canza wanda canjin ka iya zama normal musamman in ana axumi ko anjima ba'a sa komi a baki ba, ko in anci abinci a kwanta batare da an brush ba. Wannan daban

Saide in warin baki ya zamto koda yaushe akai-akai da har yakai yana hana mutum sakewa toh muhimmin abu shine ai ƙokarin gano abinda ke haddasa hakan tukun domin a magancesa' ta haka ne za'a iya raba kai da matsalar.

┈┉┅━💕🌷💕━┅┉┈

Wasu lokutan ba rashin brush bane ko rashin tsafta bane kurum kamar yadda mutane kan ɗauka, kwai abubuwa da dama akarkashin hakan wanda s**a ƙunshi:

1- Daɗɗiyar cutar ulcer, in mutum ya jima dauke da ulcer batare da maganceta ba, hakan nasa warin baki ko numfashi wanda ke tasowa daga can cikin uwar hanji tunda gyambo ne dama,
Shyasa akan kirata da gyambon ciki tunda ko gyambon dake waje yakanyi wari ballantana na can cikin ciki da iska bata ratsawa... sakamakon kwayar cutar dake haddasa ulcer ɗin heliko bakta failorus dakesa gyambon ya kume.

2- Haka nan toshewar kafafofin salivary gland wato bututun sashin dake samar da miyau abaki sakamakon tsakuwa data toshesa ta "salivary stones" hakan yana sa warin baki sosai kuwa,

3- Haka ma samuwar tsakuwoyin tonsils wato tonsils stones dake faruwa sanadiyyar abincin dakan makale abaki da hakoran mu bayan gama cin abinci, inda ahankali yakan haɗu da kwayoyin cutar bacteria a bakin ya haddasa wannan tsakuwar dake haddasa warin bakin mara daɗi wanda har numfashi haka za'a ji yana ɗoyi.

4- Haka ma matsalar shigar kwayoyin cuta ramuka ko kogunan ƙashin fuska (sinuses) dake ƙasan hanci su haddasa "sinusitis" wato rauni agun, kaji harta hanci ko tusonon mutum wari yake gami da ciwon kai ko ciwon fuska.

5- Haka yanayin abincin da mutum ke ci akai akai irinsu albasa ko tafarnuwa batare da tsafyar baki me kyau ba.

┈┉┅━💕🌷💕━┅┉┈

6- Ɗabi'ar shan ababen zaqi kamar tea empty ko yaushe, chocolates, candy, coke da lemukan gwangwani dana roba. Duk in baki ba'a tsaftace sa dakyau tare da amfani da "tongue scrapper" ana karce saman harshen a wankesa bayan anyi brush to ana iya wayar gari da warin baki akwana a tashi.

7- Ko kuma idan mutum nada kogon haƙori sakamakon abincin dakan shiga ciki ya maqale nan ma yana iya haddasa warin baki

8- Haka zalika rashin iya wanke baki koda ana yi kullum, shima brush din iyawa ne, don haka in ba a sakuce ko ina da kyau ana iya wayar gari da matsalar.

9- Haka ma idan mutum na kwanciya bacci batare da wanke baki ba bayan yaci wani abu komi kankantarsa koda kuwa biscuits ne kada araina, wannan bama warin baki ba hatta miyawun bacci na daga abinda ke kawosa wato kwanciya batare da cikakken tsaftar baki ba.

┈┉┅━💕🌷💕━┅┉┈

MATAKAN ƊAUKA

Maganin matsalar ya ta allaqa ga abinda ya zamto shine aka gano dalilin wari.

1. Idan tsakuwoyin stones ne dole sai anhuda anciresu, saide wannan aikin likita ne domin ba ganinsu ake ba ido da ido shine yasan mazauninsu a bakin, warin bakinsu yafi hamami in sune kamar anbude irin tukunyar Gas dinnan haka zakaji bakin mutum,

2. Idan rashin yin brush da kyau ne toh ya dace agyara akuma ke samun abu ana sakuce tsakanin hakora.

3. Idan hakori me kogo mutum garesa yaje a wanke acike kogon ko acire hakorin in bazai ciku ba, shikenan anrabu,

4. Haka zalik in wani abu mutum yake ci toh sai ya kaurace masa musamman gab da kwanciya bacci, karka ci komi awa 2 kafin yin bacci inba ruwa ba.

5- Wanke baki da ruwan sinadarin hydrogen peroxide irin wanda ake sayarwa don wankin ciwo, bayan antsiyaya anɗan qara masa ruwa kaɗan ankashe zafinsa sai ai amfani dashi ya zamto ana kurkure baki dashi sau 2 ko 3 ayini... yakan taimaka wajen rage matsalar idan har dalilin kwayoyin cuta ne

6. Tauna kanumfari kamar kwaya 3 yana sa aji saukin abin musamman wanda hakan ke hanasu more jima'i.

In wajen jima'i ne kuma anason kiss da sauransu toh ai amfani da kanumfarin atauna kafin afara artabun yana dauke warin baki nan take har kui artabunku ku gama tukun.

7. Ko kuma tafasa kanumfarin kwaya 7 zusa sama a wadace da ruwa daidai misali arika kurkure baki da ruwan ana zubarwa ahankali, ake yi safe da yamma zuwa wani dan lokaci, musamman ace ana qarawa da gishiri acikin ruwan kanumfarin zaifi aiki, ana iya ake kurkurawa sau uku ayini basai iya sau biyu ba, ya danganta da tsananin warin da ake ji.

8- In ulcer ce ai maganinta itama, sannan ake brush kullum kafin a kwanta.

9- Haka in "SINUSITIS" ne da hatta mutum shi kansa yana jin inya buso iskar hancinsa ya shaka tana warin ga ciwon kai toh shima yaje ga likita abashi magani a asibiti a warkar da abin.

10- Ko amfani da apple cider vinegar wajen kurkure baki safe da yamma inba kanumfari duk yakan taimaka.

11- Hakama amfani man olive azuba arika kurkurawa tsawon minti 20 a baki kafin a zubar, hakan ajere akai-akai zai tallafa

12- Hakama amfani da baking soda wajen wanke baki safe da yamma ko duk bayan sanda aka gama cin abinci a madadin amfani da makilin

13- Sai canza brush akai akai kada yake wuce wata 3 ana amfani da brush guda.

14- Koyon halayyar zuwa arika wankin hakora a clinics na dentist duk bayan wata 6 kimanin sau 2 a shekara zai taimaka, har lafiyar idanu da kunne saita ƙaru, basai me ciwon hakori ba wannan, zuwa flossing abu ne da akeso ga kowa.

✍🏻
Ibrahim Y. Yusuf

13/07/2024

LALACEWAR HAKORI (TOOTH DECAY)

Lalacewar hakori (tooth decay): shine mafi zama gama-gari a cikin mutane, wanda yake faruwa sakamakon taruwar kwayoyin halittar bacteria (streptococcus mutans) da sauransu a jikin hakori. Yana kawo rami ko kogo a jikin hakori (tooth cavity).

ABUBUWAN DA SUKE KAWO LALACEWAR HAKORI

Abubuwan da suke kawo lalacewar hakori sune:
1: Yawan ci ko shan kayan zaki (consumption of sugary foods).
2: Yawan ci ko shan abubuwa masu danko (consumption of starchy foods).
3: Rashin tsabtar baki (poor oral hygiene).
4: Bushewar baki (Dry mouth).
5: Taruwar sinadarin acid a cikin baki (acid buildup in the mouth).

ALAMOMI (SIGNS AND SYMPTOMS)

Alamunsa (symptoms) sune
1: Ciwon hakori (tooth ache).
2: Rashin dadin baki idan abubuwa masu zafi ko sanyi s**a shiga cikin baki (sensitivity to hot or cold substances).
3: Kogo/rami a hakori (tooth cavity).

TREATMENT
Hanyoyin magance lalacewar hakori sune kamar haka:
1: Yin cikon kogon hakori (tooth filling).
2: Bude jijiyoyin jini na hakori (Root canal therapy RCT).
3: Cire hakori (tooth extraction).

Likita zai iya tabbatar da lalacewar hakori ne (diagnosis) ta hanyar daukar hoton hakori (tooth x-ray) ko kuma duba hakorin maras lafiya (visual examination).

Rashin magance lalacewar hakori bayan an tabbatar dashi zai iya haifar da munanan matsalolin baki, kamar taruwar gunya a cikin baki (mouth abscess) ko faduwar hakori (tooth loss).

02/06/2024

Masha allahu

20/03/2024
HAPPY WORLD ORAL HEALTH DAY FOR ALL DENTIST IN THE WORLD
20/03/2024

HAPPY WORLD ORAL HEALTH DAY FOR ALL DENTIST IN THE WORLD

Dr Adam Muhammad happy world oral health  day
20/03/2024

Dr Adam Muhammad happy world oral health day

20/03/2024

HAPPY WORLD ORAL HEALTH DAY FOR ALL DENTIST IN THE WORLD 🌎

Shin kokasan cewa duk bayan wata uku ko hudu ya kamata ace kacenza brush dinda kake wanke baki?
22/01/2024

Shin kokasan cewa duk bayan wata uku ko hudu ya kamata ace kacenza brush dinda kake wanke baki?

21/01/2024

Cutar ƙwai
( Egg Drop Syndrome)

Hankalin duk mai kiwon kaji layers kan tashi da zarar yaga yawan kwansu na raguwa( watau egg drop syndrome).

Egg drop syndrome ( EDS76) cuta ce wacce ta samo asali daga agwagi na gida asanadiyar virus mai suna duck adenovirus ( a shekara ta 1976 aka fara gano egg drop syndrome a kaji layers shi yasa ake kiransa da suna EDS76).

Ita wannan cuta tana yaduwa ta hanyar baragurbin kwai ( contaminated egg), farantin kwai ( egg tray ), maikula da kaji, ruwa da abincin su.

Kaji ( hen) , agwagi na gida ( duck) da na turawa ( geese) , salwa (quail) an ruwaito su s**afi kamuwa.

Babban alamar EDS76 ta farko itace canzawar launin kwai ( pigment), rashin kwari ( soft) da rashin girma ( thin).

Ana samun raguwar kwai daga kaso 10% zuwa 40% ( idan ya ta'azzara) rashin daukan mataki da wuri yanasa EDS76 zama cikin kaji na tsawon mako 4 zuwa 10 ( ana fama da raguwar kwai 40%).

Dalilai da dama kan haddasa egg drop ( raguwar kwai) bayan wadanda ita EDS76 ke haddasawa.

Rashin ingantaccen sinadarin abinci ( ingredients) kamar salt, vitamin, calcium, protein da sauran su suna taimakawa raguwar kwai.

Tsananin zafin rana ( high temperature), kuma ( ectoparasites), kunna musu wuta da dare da shan kwai ( egg eating habit da predators kamar bera, macizai (suma suna taka muhimmiyar rawa gurin raguwar yawan kwai).

A duk sanda kuka tsinci kanku cikin halin egg drop kuyi kokarin tambayar kawunanku wadannan tambayoyin tareda neman amsar su ;
* Kajin sati ko watannin su nawa ? Domin da akwai lokacin da wajibi ne su daina kwai kamar lokacin moulting da kuma tsufa.

* Yawan abinci da suke ci a rana ? Domin idan suna ci fiye da kima lallai za'a samu matsala ( domin kaji 200 masu kwai suna cin buhu guda ne a rana 25kg).

* Shin cinsu ya ragu ? Domin da zarar cin ya ragu lallai da akwai abinda ya haddasa haka abincika .

* Shin kun canza masu abinci ? Da zarar an canza masu abinci daga wani kamfani zuwa wani ba tareda bin ka'idaba za'a samu matsala.

* A wanni nawa suke kasancewa cikin haske ? Domin suna bukatar awa 16 na haske sauran a awa 8 suyi bacci.

* Shin kajin a cunkushe suke ? Cunkoson kaji na haddasa matsaloli akiyaye.

* Suna cikin koshin lafiya ? Domin da zarar basu da lafiya lallai za'a samu egg drop.

* Anyi feshin maganin ciyawa ( herbicide ) ko kwari ( pesticide) cikin inda suke ko a kewaye? Lallai feshin magani kamar herbicide ko pesticide na haddasa masu matsaloli.

* Kuna kula da kuzarin su kuwa? Rashin kuzari alamace ta matsala.

* Shin canjin yanayi ( weather) yana da tasiri ga kajin kwai? Kwarai da gaske idan weather ta canza yana iya shafar yawan kwansu.

* Magani na iya haddasa raguwar kwai ? Lallai a lokuta da dama antibiotics dangin sulphate yana iya haddasa matsala ta egg drop sabida karfin sa.

Domin yin riga kafin EDS76 ku kiyayi baiwa kaji ruwan dam, rafi da korama. Ku tabbata agwagi da wadansu tsuntsaye basu shiga inda layers suke. A karshe ku kawarda kazar da ta kamu da EDS76 cikin hanzari.

Ina mafita ? Idan kajin ku s**a kamu da matsalar egg drop( EDS76) kuna iya basu Egg Push Formula na tsawon kwana 5 a ruwa litre 4( Wannan mujarrabi ne).

Domin mai uwa a gindin murhu ba zai ci tuwansa gaya ba!.

Domin Karin Bayani ko Shiga shafin mu na WhatsApp ( 07032596712) ko greenarian12@gmail.com ko www.greenarianagritek.com
Facebook :Greenarian Agritek
YouTube : Greenarian Agritek
Instagram : greenarianagritek

Address

Shanono Street Rigasa

Opening Hours

Monday 09:00 - 17:00
Tuesday 09:00 - 17:00
Wednesday 09:00 - 17:00
Thursday 09:00 - 17:00
Friday 09:00 - 17:00
Saturday 09:00 - 17:00
Sunday 09:00 - 17:00

Telephone

+2348038742530

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Albarkan Allah Dental & health care Service posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Practice

Send a message to Albarkan Allah Dental & health care Service:

  • Want your practice to be the top-listed Clinic?

Share

Share on Facebook Share on Twitter Share on LinkedIn
Share on Pinterest Share on Reddit Share via Email
Share on WhatsApp Share on Instagram Share on Telegram