13/07/2024
LALACEWAR HAKORI (TOOTH DECAY)
Lalacewar hakori (tooth decay): shine mafi zama gama-gari a cikin mutane, wanda yake faruwa sakamakon taruwar kwayoyin halittar bacteria (streptococcus mutans) da sauransu a jikin hakori. Yana kawo rami ko kogo a jikin hakori (tooth cavity).
ABUBUWAN DA SUKE KAWO LALACEWAR HAKORI
Abubuwan da suke kawo lalacewar hakori sune:
1: Yawan ci ko shan kayan zaki (consumption of sugary foods).
2: Yawan ci ko shan abubuwa masu danko (consumption of starchy foods).
3: Rashin tsabtar baki (poor oral hygiene).
4: Bushewar baki (Dry mouth).
5: Taruwar sinadarin acid a cikin baki (acid buildup in the mouth).
ALAMOMI (SIGNS AND SYMPTOMS)
Alamunsa (symptoms) sune
1: Ciwon hakori (tooth ache).
2: Rashin dadin baki idan abubuwa masu zafi ko sanyi s**a shiga cikin baki (sensitivity to hot or cold substances).
3: Kogo/rami a hakori (tooth cavity).
TREATMENT
Hanyoyin magance lalacewar hakori sune kamar haka:
1: Yin cikon kogon hakori (tooth filling).
2: Bude jijiyoyin jini na hakori (Root canal therapy RCT).
3: Cire hakori (tooth extraction).
Likita zai iya tabbatar da lalacewar hakori ne (diagnosis) ta hanyar daukar hoton hakori (tooth x-ray) ko kuma duba hakorin maras lafiya (visual examination).
Rashin magance lalacewar hakori bayan an tabbatar dashi zai iya haifar da munanan matsalolin baki, kamar taruwar gunya a cikin baki (mouth abscess) ko faduwar hakori (tooth loss).