Daru Shifa Islamic and Herbal Medicine

Daru Shifa Islamic and Herbal Medicine Herbal Medicine Practitioner

MAGANIN CUTAR KODA (KIDNEY FAILURE)A wannan zamani, cutar koda ta zama babbar matsala da ke jefa mutane da dama cikin ma...
26/09/2025

MAGANIN CUTAR KODA (KIDNEY FAILURE)

A wannan zamani, cutar koda ta zama babbar matsala da ke jefa mutane da dama cikin mawuyacin hali. Wasu har ma suna rasa rayuwarsu sakamakon gazawar koda.

A wata jarida mai suna UKAZ da ke Falasdinu, an ruwaito wani saurayi mai shekaru 35 wanda ya shafe shekara guda yana yin wankin koda (dialysis). Amma daga baya, ya warke bayan amfani da Karon (Farar Kaya). Likitansa ya tabbatar masa cewa kodarsa ta murmure gaba ɗaya, kuma baya bukatar dialysis din nan gaba.

Haka kuma, an samu labarin wata yarinya mai shekaru 21 wacce creatinine nata ya kai 550, amma bayan amfani da Karo na tsawon mako uku, ya sauka zuwa 200. Wannan ya nuna irin rawar da wannan Karo (Farar Kaya) yake takawa wajen taimaka wa masu irin wannan matsala.

Yadda ake amfani da Karon (Farar Kaya):

1. A nika Karon (Farar Kaya) sosai ya zama gari.

2. A debi cokali na shayi (teaspoon) guda, a saka cikin kofin ruwa daya.

3. A barshi ya jiku na awanni 2–3.

4. A girgiza sosai sannan a tace.

5. A sha ƙaramin kofi da safe kafin karin kumallo, sannan kuma kafin bacci.

Muhimman Bayanai:

✅ Abin da ake amfani da shi shi ne asalin Karon Farar Kaya.

✅ Masu yawan creatinine da aka gwada aka tabbatar – sune za su iya amfani da shi.

✅ Ana amfani da shi har sai an ga sauƙi.

✅ Ba shi da illa (side effect) kamar wasu magunguna.

Zaku iya Samun Asalin wannan Karon a Wajen mu da yardar Allah.

DARU-SHIFA PROPHETIC AND HERBAL MEDICINE STORE, Kawo – Kaduna
📞 WhatsApp: 08037624598

Ku yada wannan bayani domin amfanin al’umma baki ɗaya.

Infection na Koda (Kidney Infection)Ana kiran infection na koda da Pyelonephritis a Turanci. Wannan cuta tana faruwa ne ...
11/09/2025

Infection na Koda (Kidney Infection)

Ana kiran infection na koda da Pyelonephritis a Turanci. Wannan cuta tana faruwa ne idan kwayoyin cuta (bacteria) daga fitsari ko mafitsara s**a haura zuwa koda.

Alamomin Kidney Infection:

Zazzabi mai tsanani

Jin sanyi da rawar jiki

Zafi ko radadi a baya ko gefe (dai dai a inda kodan suke)

Yawan jin fitsari

Fitsari mai wari, duhu, ko kuma jini ya gauraya

Jin kasala sosai ko gajiya

Ciwon ciki ko tashin zuciya

DALILAN DA SUKE HADDASA CIWON:

Yawan jinkirta yin fitsari Wato rike fitsari tsawon lokaci.

Ciwon urinary tract infection (UTI) da ba a yi mashi magani ba.

Duwatsun koda (kidney stones)

Mata sun fi kamuwa da Cutar sabo da gajeren bututun mafitsara da suke da ita.

Cutar suga (diabetes)

Raguwar karfin garkuwar jikin Dan'adam.

Illolin Da Cutar zata iya yi idan ba a kula ba:

Cutar zata iya lalata koda

Zata iya zama hanyar yaduwar kwayoyin cuta a cikin jini wanda ke da hatsari ga rayuwar Dan'adam.

Zata iya zama ciwon koda na dindindin (chronic kidney disease)

Allah ya tsare Mana Lafiyar mu Baki Daya Ameeen.

WHATSAPP 08037624598

Muhimmancin Maganin Gargajiya na Itatuwa da Ganyayyaki a Jikin Dan’adamDaga Cibiyar Magungunan ta DARU-SHIFA PROPHETIC A...
31/08/2025

Muhimmancin Maganin Gargajiya na Itatuwa da Ganyayyaki a Jikin Dan’adam

Daga Cibiyar Magungunan ta DARU-SHIFA PROPHETIC AND HERBAL MEDICINE STORE KAWO KADUNA WHATSAPP 08037624598

Maganin gargajiya na itatuwa da ganyayyaki wani muhimmin ɓangare ne na lafiyar ɗan’adam. Tun kaka da kakanni, al’umma suna dogaro da shi wajen samun lafiya da warkar da cututtuka. Wannan ya nuna cewa Allah ya halicci bishiyoyi, ganye, tsaba da ‘ya’yan itatuwa domin taimakon ɗan’adam.

Fa’idodin Maganin Gargajiya:

1. Ƙarfafa garkuwar jiki:
Wasu ganye suna ƙara ƙarfin garkuwar jiki wajen yaƙar cututtuka.

2. Warkar da cututtuka cikin sauƙi:
Ana amfani da su wajen maganin ciwon ciki, basir, zazzabi, ciwon makogwaro da sauransu.

3. Ba sa da illa sosai:
Idan aka yi amfani da su yadda ya dace, suna da aminci fiye da wasu magungunan zamani.

4. Tsaftace jini da rage kitse:
Ganye da tsaba suna taimakawa wajen tsaftace jini, rage kitsen jini da hana toshewar jijiyoyin zuciya.

5. Sauƙin samu da saukin Kashe kudi:
Yawancin su suna samuwa cikin gida ko kasuwa ba tare da tsada mai yawa ba.



Habbatussauda (Black seed):
Ana mata kirari da magani ga kowanne cuta sai mutuwa da tsufa. Yana ƙarfafa garkuwar jiki tare da rage ciwon suga da hawan jini.

Tafarnuwa:
Yana kashe ƙwayoyin cuta a jiki, rage hawan jini, tsaftace jini, kuma yana taimakawa wajen narkewar abinci.

Zuma:
Abinci ne kuma magani. Yana maganin ciwon makogwaro, yana ƙara kuzari, yana kuma taimaka wajen warkar da raunuka da Ciwon ciki ga wasu.

Zaitun da Man Zaitun:
Yana rage ciwon zuciya, yana tsaftace jini, kuma yana taimakawa wajen narkewar abinci.

Ganyen Zogale (Moringa):
Yana ƙara ƙarfin jiki, tsaftace hanta, rage hawan jini da kuma magance matsalar gajiya.

Citta da Tafarnuwa:
Ana amfani da su wajen ƙara ƙarfi, narkewar abinci, da magance mura da zazzabi.

Kammalawa:

Maganin gargajiya wata kyauta ce daga Allah ga ɗan’adam. Yin amfani da ganyayyaki da itatuwa wajen magani yana da matuƙar muhimmanci wajen kare lafiya da ƙara ƙarfin jiki. Sai dai wajibi ne a yi amfani da su cikin hikima da shawarar masana, domin kaucewa matsaloli.
゚viralシviralシfypシ゚viralシalシ

NATURAL MA********ON CLEANSER & SEXUAL HEALTH BOOSTER Are you struggling with premature ej*******on, low sexual desire, ...
31/08/2025

NATURAL MA********ON CLEANSER & SEXUAL HEALTH BOOSTER

Are you struggling with premature ej*******on, low sexual desire, or weakness of the private organ❓
Here is a powerful and effective herbal medicine from Daru-Shifa Prophetic & Herbal Medicine Store, Kawo Kaduna ✨

✅ Helps cleanse the effects of ma********on
✅ Strengthens the immune system
✅ Restores and boosts sexual desire for men & women
✅ 100% Natural & Prophetic Herbal Remedy – Safe with no side effects

📍 Available at Daru-Shifa Prophetic & Herbal Medicine Store, Kawo Kaduna

📞 Contact us on WhatsApp: 08037624598

Daru-Shifa – Your Natural Path to Complete
Shamsiyya Abdullahi

Menene Ge***al Wart (Warts na Gabobin Jiki)?Ge***al warts su ne tsiro ko kumbura masu kauri ko laushi da ke fitowa a gab...
07/08/2025

Menene Ge***al Wart (Warts na Gabobin Jiki)?

Ge***al warts su ne tsiro ko kumbura masu kauri ko laushi da ke fitowa a gabobin jima’i na maza da mata. Su na daya daga cikin cututtukan da ake ɗauka ta hanyar jima’i (STI – Sexually Transmitted Infection) kuma kwayar cutar HPV (Human Papillomavirus) ce ke haddasawa – musamman nau'in HPV 6 da 11.

Wajen da S**a Fi Fitowa:

A Maza:

* Kan azzakari

* Bawon azzakari (fo****in)

* A kusa da dubura

* Cikin bututun fitsari

A Mata:

* Farji (va**na)

* L***a (leɓɓun farji)

* Cikin mahaifa (cervix)

* A kusa da dubura

Alamomin Ge***al Wart: Gasu kamar haka:

* Tsiron fata mai kauri ko laushi

* Yakan kasance kamar 'kabeji' ko 'tsaba'

* Yana iya zama ɗaya ko da yawa (kamar rukuni)

* Yana iya janyo kaikayi, kumburi ko ƙaiƙayi

* Ba lallai ya kasance da ciwo ba, sai dai idan ya kumbura sosai

* A jikin wasu mata, yana iya zama a cikin inda ba za a ganshi ba.

Hanyoyin Kamuwa da Cutar:

* Hanyar jima’i mara kariya (va**nal, oral ko a**l)

* Taɓa fatar Mai Dauke da Cutar

* Daga uwa zuwa jariri a lokacin haihuwa (sai dai da wuya muddin aka haihu a Asibiti.

Hanyar Kariya

* Ayi kokari kiyaye jima'i da matar da ba na mutum ba.

* Ayi kokarin kiyaye taba Wajen wannan kuraje batare da safar hannun ba.

(c) Taskar Murtala Kawo

08037624598

02/07/2025

Yanda Zaku Magance Matsalar Hepatitis A and C

24/06/2025

MASU MATSALAR HAWAN JINI KU SAURARI WANNAN BIDIYON ZAKUJI MAFITA DA YARDAR ALLAH

18/06/2025

Hanyoyin Samun Ni'ima Ga Matan Aure Cikin Sauki

14/06/2025

Domin Samun Magungunan Matsalolin da kuke Fama dasu na Jinya A Tuntubemu a WhatsApp 08037624598

04/06/2025

Masu Matsalar Istimana'i ga wata garabasa

Wasu Daga Cikin Alamomin Shafar junnu/Sihiri Daga Cikin Littafin Assarimul-Battar1. Mutum ya zama ba ya son karatun Alku...
04/06/2025

Wasu Daga Cikin Alamomin Shafar junnu/Sihiri Daga Cikin Littafin Assarimul-Battar

1. Mutum ya zama ba ya son karatun Alkur'ani ko saurarensa

2. Rashin son yin ibada kamar sallah, ko a yi ta cikin bacin rai da kasala.

3. Yawan ciwon kai mai tsanani ko 6arin kai ko kuma jiri.

4. Yawan ciwon mara ko baya ko kwankwaso ko kuma ciki wanda ba ya jin magana kuma an rasa me ke kawo shi.

5. Yawan jin tafiyar wani abu a jiki kamar kiyashi ko tsutsa ko kwarkwata tana yawo a kai amma idan an duba ba za a ga komai ba.

6. Yawan mafarke mafarke na abun tsoro ko firgirta da surutai a cikin bacci ko kuma mutum ya ji wani abu mai nauyi ya danne shi ko ya shake masa wuya.

7. Yawan jin tsoro ko faduwar gaba ko wani abu ya dinga yi ma ka gizo ko kuma ka ji kamar ana kiran sunan ki amma ba za ka mai kiran ba.

8. Yawan jin sanyi ko zafi ko rikewar kafa ko wani sashe na jiki ba tare da wani sanannen dalili ba.

9. Rashin iya bacci da daddare ko yawan jin motsin wani abu ko surutai ko kuma takun tafiya.

10. Rashin son yin kitso ko aski kuma a taba m ka/ki kai.

11. Yawan bacin rai ko jin haushin mutane ba tare da wani dalili ba.

12. Rashin son shiga cikin mutane ko yawan zargin su ko kuma yawa rigima da su.

13. Yawan kuka ko dariya ko murmushi ba tare da wani dalili ba.

14. Yawan jin kamar ana yi ma ka rada a kunne ko a ringa raya ma ka zuciya akan ka aikata wani lefin kamar kisan kai ko zina ko kuma sata

15. Rashin son yin Aure ko korar samari ko kasa tsayar da guda daya kwakwara. Haka ma ga namiji abun ya ke.

16. Daukewar Sha'awa ko rashin jin dadin saduwa da muji ko kuma tsanar sa da wulakan tashi ba tare da wani dalili ba. Shi ma namiji haka zai dinga ji.

17. Yawan kallon mudubi ko Sha'awar kallon tsiraici.

18. Yawan son kade-kade da raye-raye.

19. Yawan son dare ko cikin duhu ko yin shuru kamar ba ka gurin.

20. Rikicewar Jinin Al'da ko na Nifasi ga mace.

21. Rashin Haihuwa ko yawan Bari ko Haihuwar dan babu rai ko kuma wasu matsaloli su biyo bayan Haihuwa kamar jijjiga.

22. Aikata wani abu ba a cikin hankalinka ba, sai daga baya ka ringa nadama ko mamakin yadda akayi ka aikata.

23 Yankewar jiki a fadi kasa ba a cikin hayyaci ba ko kuma ihu da rugawa a guje ba tare da ka san inda za ka ba.

24. Yawan wasuwasi ko mantuwa acikin dukkanin Al'amura musamman a lokacin ibada.

25. Tabuwar kwakwalwa ko kasa fahimtar ko wane irin abu.

26. Rashin tsafta da son zama cikin kazanta da dauda.

27. Yawan fita waje mara dalili ko tarewa a wani wuri kamar karkashin bishiya, kan bola, bandaki, jeji, bakin ruwa, da sauran su.

28. Rashin lafiyar da za'a kasa gane kanta.

29. Rashin son Wa'azi ko zama da mutanen kirki.

30. Yawan jin tsoron Rukuya ko masu yinta.

Allahu Ta'ala A'alam

Zaku Iya Samun Magungunan jinyan da s**a shafi matsalar Junnu da Sihiri dss.

Daru-Shifa Prophetic and Herbal Medicine Store kawo Kaduna Whatsapp 08037624598

29/05/2025

Maganin Ciwon Hanta Mai Tara Ruwa don Allah Yan'uwa Muyi Kokarin Share domin Al'umma su amfana

Address

Masanawa Road, Kawo, Kaduna
Kaduna
800283

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Daru Shifa Islamic and Herbal Medicine posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Share on Facebook Share on Twitter Share on LinkedIn
Share on Pinterest Share on Reddit Share via Email
Share on WhatsApp Share on Instagram Share on Telegram