06/01/2026
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa makomarsa a zaɓen shekarar 2027 tana hannun Allah Maɗaukaki, ba a hannun ɗan Adam ba, yana mai jaddada cewa mulki kyauta ce daga Allah.
Gwamnan ya yi wannan bayani ne yayin da yake mayar da martani ga jita-jita da hasashe da ake yi game da siyasar Kano da kuma batun zaɓen 2027. Ya ce bai damu da maganganun siyasa ko tsinkayar wasu mutane ba, domin duk abin da zai faru, Allah ne kaɗai ke da ikon yanke hukunci.
Abba Kabir Yusuf ya ƙara da cewa a matsayinsa na shugaba, abin da ya fi ba shi muhimmanci shi ne aikin da aka ɗora masa na jagorantar al’ummar Kano yadda ya dace, ta hanyar aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da za su amfani jama’a.
Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da mai da hankali kan inganta rayuwar al’umma, gina ababen more rayuwa, ilimi, lafiya da walwalar jama’a, maimakon shiga rudanin siyasar gaba tun yanzu.
Gwamnan ya kuma yi kira ga magoya baya da al’ummar jihar Kano da su ci gaba da yin addu’a, su kuma guji duk wani abu da zai iya haddasa rarrabuwar kai, yana mai cewa hadin kai da zaman lafiya su ne ginshiƙan ci gaban kowace al’umma.
A cewarsa, duk wanda Allah Ya nufa da mulki, babu wanda zai iya hana shi, haka kuma wanda Allah bai nufa ba, babu yadda za a yi ya same shi.
ME ZA KU CE ?