Na'Rasulu Islamic Medicine

Na'Rasulu Islamic Medicine Wannan page ze dinga kawo muku yadda zaka sarrafa magunguna Na Islamic Medicine da tallata maka magan

29/03/2024
Kana fama da typhoid?WhatsApp: ☏+2348069368301Maza matso nan, karka damu.Kaje wajan mai saida da kayan marmari, kace ya ...
29/03/2024

Kana fama da typhoid?

WhatsApp: ☏+2348069368301

Maza matso nan, karka damu.

Kaje wajan mai saida da kayan marmari, kace ya baka Abarba (pineapple) kwallo daya, bayan ka siya, ka gaya mishi bawon kake so zakai amfani da shi, idan yana da wani bawan dan Allah ya baka.

Dalilin siyan, shine wani idan kace mishi ya baka bawon kyauta, ba zai baka ba. Amma idan kai mishi ciniki, idan yana dashi zai kara maka.

Note:-Ga Duk wadda take da bukatar gyara ko wata matsala a lafiya ta, ko Kuma wata cuta ta bangaren mu'amala da maigidanta.

Zaka iya samun maganin mu a kowane gari ko jiha kake a Nigeria indai ba cikin kauye bane, wato muna turawa a duk inda kake.

Sai ka dawo gida ka samu ruwa dai-dai wa dai-da, bayan ka wanke bawon sai ka tafasashi da ruwa mai kyau, ya samu kamar minti 15 akan wuta, yana tafasa. Sai ka sauke shi ka tace, ka barshi ya huce, sai ka dunga shan cikin kofi daya sau biyu a rana, idan kaso zaka iya saka mishi zuma, zuwa kwana uku zaka sha, idan kuma tana da yawa a jikin ka, ka sha na sati daya.

Idan ka gama, kaje Asibiti a sake gwada ka, Insha za'a samu waraka. Kwallon abarba (pineapple) yanzu baya wuce 1k.

09/03/2024

Saƙo Ga Sabbin Angwaye Da Masu Niyar Aure.:

Ganin Jini A Daren Farko Bashi Ne Budurci Ba:

A zamanin da can, anyi lokacin da ake shinfida farin kyale akan shifidar sabbin ma'aurata domin a tabbatar da budurcin amaryar.
Idan jini ya zuba a daren farkon saduwarta da mijinta to wannan itace budurwa abar alfahari ga iyayenta dama zuri'ansu gaba daya. Idan kuwa ba a ga jini ya malale wannan farin kyalen ba to wannan amaryar ba budurwa bace aka auro, ma'ana tana zina ko ta taba yin zina. Wanda hakan na iya rusa wannan auren.

Wannnan maguzanci tonon silili yayi tasiri sosai cikin wasu kabilun African ciki harda kabilun Hausa da Fulani. Wanda tasirinsa ya jima cikin al'uma sosai kamin kungiyoyin addini su yaki irin wannan bakar al'adar.

Wasu mazan suna dauka cewa muddin basu ga jini ya zuba a darensu na farko da sabuwar amaryarsu ba to a tunaninsu wannan amaryar ta taba yin zina ko kuma tanayin zina.

Wasu mazan kuwa suna daukar cewa muddin basu sha wahala ba wajen shigar da azzakarinsu farjin amaryarsu a daren farko wannan ma alamune na amaryar tana zina. So suke suga a ranar farko babu kofa a farjin amaryarsu sai sun shiga da kyar.

Wannan camfin ko tunani da har yanzu yake da tasiri ga wasu mazan yasa yanzu haka 'yan mata masu niyar aure wandan kuma s**a taba zina ko suke zina suke da dabaru da damar gaske da suke amfani dasu wajen tsuke gabansu ya dawo tamkar na yar shekaru 7 da haihuwa.

A yanzu haka akwai hanyoyi na zamani dana gargajiya masu yawan gaske da 'yan mata suke bi kuma suke amfani dasu domin su tsuke gabansu har sai jini yayi zuba a daren farko aurensu. Inda ango sai yayi ta murna da farin cikin ya samu matarsa a budurwa nan ko baisan dawan gari ba.

Sai dai kuma yana da kyau maza su fahimci cewa ita fa budurwa da akwai hanyoyi masu yawan gaske da zata iya fita daga budurci kuma batasan wani danamiji da sunan jima'i ba.

 'awaAssalamu Alaykum wa rahmatullah, barkan mu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan...
19/11/2023

'awa

Assalamu Alaykum wa rahmatullah, barkan mu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin.

Ga bayani da zai amsa tambayoyin da da masu karatu matasa s**a aiko kan yadda za su magance matsalar matsananciyar sha’awa da ta addabi rayuwarsu, da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.

Tambaya

Malama Nabila don Allah ki yi man bayani game da mutum mai yawan jin sha’awa kuma ga shi babu yadda za ai gidansu a yi masa aure saboda karatu ga shi kuma yana jin tsoron aikata fasikanci don ya san hukuncin wanda ya yi haka wurin Allah; don Allah wadanne hanyoyi zai bi don magance matsalar? Daga Haidar.

Amsa: Ga hanyoyin da matashi zai bi don yakar matsananciyar sha’awa ya kasance ba ta kai shi ga fada wa cikin halaka ba:

Fahimta Kyakykyawa: Abu na farko na maganin wannan matsala shi ne ta hanyar yi mata cikakkiya kuma kyakykyawar fahimta:

Ø Matsananciyar sha’awa wani yanayi da sha’awar mutum ke yawan motsuwa nan da nan kuma kusan kowane irin lokaci, musamman a lokuttan da ba ya bukatar motsuwarta. Wannan yanayi yana faruwa ga duka masu aure da marasa aure, maza da mata, kuma yana takurawa ga rayuwarsu, sannan yana jefa wasu ga yin zinace-zinace; zinar hannu da kallon fina-finan batsa, wadanda duk wasu muggan ayyuka ne da ba su kawo sauki ga matsalar sai dai su kara ruruta ta, sannan suna kawo bakantar dabi’ar masu aikata haka da raunana masu imaninsu.

Yana da kyau ga mai fama da matsananciyar sha’awa ya fahimci cewa, sha’awa ba komai ba ce illa daya daga cikin al’amuran gudanarwar jikin dan’adam da Allah Ya halitta shi da su. Kamar yadda wani ya fi wani tsawo; wani da saurin fushi wani kuma da sanyin zuciya, to haka sha’awa ta bambanta tsakanin mutane ta fuskoki daban-daban. Kamar yadda mai tsananin fushi Allah Ya h**e masa iko da damar dannewa da hadiye fushinsa, to haka ma mai tsananin sha’awa yana da cikakken ikon da zai danne sha’awar.

Wannan shine laba laba magani sanyin Kashi ko radadi ko ciwan gwaiwa, domin samunsa Zaku iya tuntubarmu.Na'Rasulu Islami...
20/10/2023

Wannan shine laba laba magani sanyin Kashi ko radadi ko ciwan gwaiwa, domin samunsa Zaku iya tuntubarmu.Na'Rasulu Islamic Medicine

It's All available at Na'Rasulu Islamic Medicine
14/10/2023

It's All available at Na'Rasulu Islamic Medicine

18/07/2023

Habba & Zuma

15/06/2023

KUSKURE GUDA 50 ALOKACIN BAWA YARO TARBIYYA.

1. Bawa yaro nono a kwance

2. Sawa yaro suna mara kyau

3. Barin yaro da kazanta.

4. Rashin jan yaro a jika.

5. Kin ciki idan ya shiga.

6. Rashin nemawa yara iyaye nagari.

7. Sabawa ka’idojin shari’a a wurin saduwa.

8. Yawan bacin rai da tashin hankali ga uwa yayin da take da ciki.

9. Rashin aikata ladduba da sharia ta shinfida da zarar an haifi yaro.

10. Daukar yaro, ko bashi nono duk lokacin da yayi kuka.

11. Rashin tsara lokacin shayarwa.

12. Wuce ka’idar lokacin daya dace a shayar da yaro.

13. Rashin sawa yaro tsoron Allah a zuci sai na iyaye.

14. Fifita wani a tsakanin ‘yaya.

15. Daurewa yaro gindi in yayi laifi ko tsokana.

16. Bawa yaro ko sayamasa duk abinda yanema.

17. Rashin koyawa yaro shiga irin ta musulunci.

18. Rashin kai zuciya nesa in yaro yayi laifi.

19. Rashin koyawa yaro yanda zaiyi Magana da nagaba dashi.

20. Rashin sanin gurin da yaro yake zuwa idan yafita.

21. Rashin sa yaro a makarantar data dace.

22. Rashin koyawa yaro yadda zai karbi bako.

23. Sayawa yaro kayan wasan da basu daceba.

24. Sawa yaro abinci yai taci ba iyaka.

25. Koyawa yaro mummunar shiga ta hanyar shigar da iyaye sukeyi.

26. Rashin karantar halin yaro dayi masa hukunci da daya daga cikin halayen ‘yan uwansa.

27. Tilastawa yaro yayi abinda bazai iyaba.

28. Zabawa yaro fannin dazai karanta alhali bashi yake soba, ko bazai iya yinsaba.

29. Yawan zagi da iyaye sukeyi a gaban yaro.

30. Hana yaro yin wasa alokacinsa.

31. Sanya fina finai marasa kyau, Yaro yana gani.

32. Yiwa ‘yaya auren dole.

33. Rashin manufa daya tsakanin iyaye.

34. Hora yaro ta hanyar hanashi abinci, ko barinsa da yinwa, bayan da akwai abincin da za’a bashi.

35. Bawa yaro umarni da yabawa juna.

36. Barin yara maza da mata suna cudanyar data sabawa shari’a.

37. Barin yara suna zuwa bukukuwa barkatai.

38. Dorawa yara maza ko mata talla.

39. Rashin yiwa yara bayanin sabon yanayin da zasu fuskanta idan sun kusa balaga.
To be continue

Address

SHEKA DAN DURIMI
Kano

Telephone

+2348069368301

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Na'Rasulu Islamic Medicine posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Practice

Send a message to Na'Rasulu Islamic Medicine:

Share

Share on Facebook Share on Twitter Share on LinkedIn
Share on Pinterest Share on Reddit Share via Email
Share on WhatsApp Share on Instagram Share on Telegram

Category