02/06/2025
SIRRIN DAFA JIJJIBI
,
,
,
,
Ba sai lallai mai jego ke dafa jijjibin saniya ba matuƙar ya dace da buƙatarki zaki iyayi koda kuwa ke budurwa ce,
maganar ace miki yana zazzago da gaban mace wannan kuma saidai idan akwai rashin ƙwarewa a dafuwarki,
misali kiyi amfani da jijjibin tsohuwar saniya, ko kuma ki dafa harda nononta da mahaifarta, irin waɗannan sune suke iya bawa mace matsala amma kamar yanda yake a wannan photon kika sameshi aka gyarashi sosai to hankalinki a kwance zaki ci kuma kiga aikinsa,
WANNE IRIN GYARA AKE MASA?
ana babbakeshi duka gashin jikin fatar ya ƙone akankareshi sosai sannan a wanke, saiki yanyanka shi yanka ƙanana kamar yanda zakiyi farfesu,
DAME AKE DAFASHI?
ana dafa jijjibi da itatuwa zallah sannan ana dafashi da yajin ciccibi, yanda ake dafashi da yajin zamuyi bayani kasancewar yafi sauƙi haka zalika yafi tasiri sosai ajikin mace sannan shi yajin ana iya dafashi da jan nama na saniya ko sa, saidai ba daidai yake da ayishi da naman jijjibi ba, saboda haka muka zaɓi bayani akan wannan yajin wato YAJIN CICCIBI
yajin ciccibi ana haɗashi ne idan zaku haɗu mutum 3 zuwa 5 kuyi ku raba amma idan mutum ɗaya ko biyu zaifi miki sauƙi ki sayi yajin kawai wanda be wuce 1k zuwa 2k ba, saboda yana cin kuɗi haɗashi domin hadashi kai tsaye kina buƙatar matakai guda 3
MATAKI NA 1 shine kayan yajinsa kowanne irin kayan kamshi da yaji ana iya sawa amma a tabbatar akwai
Ɗan kumasa
minanas
kananfari
citta
waɗannan anaso adadinsu ya zama ɗaya dukkansu haɗesu waje daya kiyi yajinsu,
MATAKI NA 2 shine maganin haɗasu wanda shi kuma anaso yawan garin ya ninka na farkon abun nufi idan aka haɗa yajin gwangwani 1 to waɗannan adadinsu ya zama gwangwani 2
sassaken gabaruwa
ƴayan gabaruwa
ƴayan kargo
sassaƙen kanya
dan bashanana
Koda yake shi ba lallai bane ƴayan kargo suna aiki irin nasa, to waɗannan ana buƙatar garinsu duka,
MATAKI NA 3 shine haɗesu garin da yajin waje ɗaya shine zai zama yajin ciccibi wanda kamar mejego tana iya mayar dashi yajin cin abinci na koda yaushe, amma kamar dafa nama ko jijjibi anaso yawansa kamar 120ml wato ƙaramar roban yaji zai ishi mace ɗaya ta dafa,
YAYA AKE DAFASHI?
idan kin samu naman kodai ya zama jan naman saniya tsoka me kyau ko kuma ya zama asalin jijjibi na gaban saniya wanda iya naman wajen akeso harda fatar jikin ba matsala bane, amma kada asaka hantsa ko nono ballantana mahaifa, saiki gyarashi ki ɗora akan wuta ki yanka masa albasa ki barshi yana tafasa kina canja masa ruwa sai kinga ya kusa nuna saiki ɗauko wannan yajin ki zuba sannan ki kawo kayan miya kowanne iri amma banda abu me yaji wannan yajin dayake jikin garin da kika zuba shi kaɗai ya isa bayan ya dafu kina iya kwana2 kinaci idan bazaki iya cinyeshi a rana 1 ba, sannan mutum biyu suna iya cinsa,
MEYE AMFANINSA?
mai jego wanda bata dade da haifuwa ba yafi mata aiki domin yana ciko da naman gaban mace ta ciki, sannan koda mace ta dade da haifuwa koda haifuwa nawa tayi matukar tanason gyara jikinta to wannan yana ɗaya daga cikin hanyoyin gyara, domin mace ta hade ta ciki yafi muhimmanci sama da matse waje, babu wani abu dayake mayarda mace ƙarama sama da matsi ta ciki,
dan haka idan har kinada damar yin hakan kiyi iya kokarinki dan gyara martabar aurenki, akwai bayani akan haɗin dafuwar kaza shima yana nan tafe.