07/10/2023
ABUBUWAN DA SUKE JANYO SAURIN LALACEWAR TITUNA
Sau da yawa tituna suna lalacewa ne dalilin yadda mutane ke anfani dasu yau da kullun. Wasu daga cikin dalilan sune:
1. Kona taya akan tituna lokacin zanga-zanga
2. Gobarar abun hawa akan t**i
3. Rashin anfani da tayoyi masu kyau a abun hawa
4. Abun hawa mai zubar da bakin mai (engine oil)
5. Tsere, guje-guje da kwabo akan tituna
6. Diban kaya fiye da kima (overload)
7. Taruwar ruwa akan t**i saboda rashin magudanar ruwa ko toshewarsa
8. Zubar da ledoji ko robobin ruwa da na lemo akan tituna
9. Mayar da tituna ko magudanar ruwa wajen zubar da shara
10. Hakar ramuka don dasa wayoyi ko pipe na ruwa
11. Gine-ginen speed bumps akan tituna
Hanyar Lafiya