04/01/2025
RIBAR DEMOKRADIYYA A GOBIRAWA WARD
WANDA DAN MAJALISAR JAHA MAI WAKILTAR ƘARAMAR HUKUMAR DALA HON LAWAN USAINI YA KAWOWA YAN KINMU NA GOBIRAWA,
Aiyukan raya kasa kenan da Hon. Lawan Hussaini Chediyar Yan Gurasa (Majority Leader Kano State House of Assembly) ya kammala su, a kasa da sheka biyu a mazabar GOBIRAWA, tabbas member ya cancanci yabo da godiya bisa wannan namijin kokarin.
Gina-gina ne na Asibitutuka har guda 3, a mabam-banta unguwani aka yi su, sun lashe milyoyin kudi, aiki akai na Mahadi ka ture domin muna kyautata zaton nan da shekaru masu yawa babu abinda zai same su, In-sha-Allahu.
Ga bayanin yanda su yake, da kuma inda aka gina su.
1. Block na farko anyi gina shi ne a Dan-Asibiti Chapter Mazabar Gobirawa a cikin Asibitin Shakatafi mai Suna TUDUN-BOJUWA PRIMARY HOSPITAL, yana dauke da dakunan kwanciya da ofishoshi da Ban-Dakuna, girman sa yakai wani Asibitin Kauyen.
2. Block na biyu anyi gina shi ne a Dorawar-Megemu Chapter Mazabar Gobirawa a cikin Asibitin Haihuwa Mai Suna GIDAN-DAGACI HOSPITAL, yana dauke da dakunan da Ofis baya ga haka har katangar Asibitin sai da aka sabunta.
3. Block na uku anyi gina shi ne a Filin-Durumi Chapter Mazabar Gobirawa a cikin Asibitin Shakatafi mai Suna UMMA-ZARIYA PRIMARY HOSPITAL, yana dauke da dakuna Da Kuma Rumfar da'ake yiwa Mata Awo (Scanning) tare Ban-dakuna.
Don haka masu neman ina member yayi aiki a GOBIRAWA-WARD ga amsar ku nan, kuma In-sha-Allahu zamu kawo wasu Aiyukan na Alheri a GOBIRAWA, Muna yuwa mai girma member Fatan Alheri Da kuma Fatan ALLAH YA MAIDA JIHA TARAYYA 2027
Lawan Hussain MEDIA TEAM 📷
Saturday 04_01_2025