Sunnah Medicine Center

Sunnah Medicine Center Shafin bayar da addu'o'i da magunguna na Musulunci. Don karin bayani a kira wannan lamba 08162600700

TAKOBI MAI KAIFI DON YAƘI DA MUGWAYEN MASIHIRTA, BOKAYE.Darasi na ɗaya (1).Gabatarwar mai fassara.Ni Bashir Halilu ina g...
25/12/2024

TAKOBI MAI KAIFI DON YAƘI DA MUGWAYEN MASIHIRTA, BOKAYE.

Darasi na ɗaya (1).

Gabatarwar mai fassara.

Ni Bashir Halilu ina gabatar muku da wannan littafi wanda na yi alƙawarin da yaddar Allah zan dinga kawo muku fassarar sa a shafina na tiktok da kuma facebook.

Littafin yana magana ne akan sihiri. Marubucin ya bayyana ma’anar sihiri, ya kuma kawo hujjoji daga Alƙur’ani mai girma da Hadisai kan gaskiyar samuwar sihiri tare da maganganun malamai game da yadda sihiri ya ke. Ya bayyana rabe-raben sihiri a fahimtar Malamai da dama, k**ar Fakhruddin Al-Razi da Al-Raghib, sannan ya bayyana hanyoyin da masu sihiri ke bi don kiran Aljannu da yadda ake mallakar Aljanu da saka su ayyuka. Har ila yau, ya bayyana hukuncin sihiri a cikin shari’ar Musulunci da hukuncin Masihirta, Bokaye.

Marubucin wannan littafi "As-Sarimul -Battar Fit -Tasaddi Lis-Saharatil -Ashrar": shi ne Wahid bin Abdussalam Bali, wanda aka haifa a Masar. Ya rubuta littattafai da dama k**ar Fakihatul-Majalis, Bidayatul-Muttafiqah, Arba'in Khata'an Lil-Lisan, Sahihul-Adabul -Islamiyyah, da sauransu.

Abubuwan da ke cikin littafin "As-Sarimul Battar Fit-Tasaddi Lis-Saharatil-Ashrar".

Littafin yana da babi-babi k**ar haka:

Babi na farko: (1)

1- Ma’anar sihiri a harshen Larabci.

2- Ma’anar sihiri a cikin shari’a.

3- Wasu hanyoyin da masu sihiri ke bi don samun kusanci da Shaiɗan.

Babi na biyu: (2)

1- Sihiri a hasken Alƙur’ani da Sunnah .

2- Hujjoji kan tabbacin samuwar Aljannu da shaiɗanu.

a) Hujjoji daga Alƙur’ani.

b) Hujjoji daga Hadisai.

c) Maganganun malamai kan sihiri.

Babi na uku: (3)

1- Rabe-raben sihiri.

Rabe-rabensa bisa fahimtar Al-Razi da Al-Raghib.

2- Bayanin nau’o’in sihiri.

Babi na huɗu:(4)

1- Hanyoyin da masu sihiri ke bi don kiran Aljannu.

2- Yarjejeniya tsakanin masu sihiri da shaiɗanu.

3) Alamomin da za a gane mai sihiri.

Babi na biyar: (5)

1- Hukuncin mai sihiri a shari’ar Musulunci.

2- Hukuncin mai sihiri daga cikin Littafin Allah.

3- Shin ana iya warware sihiri da sihiri?

4- Shin ya halatta mutum ya koyi yadda ake sihiri?

5- Bambanci tsakanin sihiri, karama, da mu’ujiza.

Babi na shida: (6)

1- Warware sihiri:

(a) Sihirin raba aure: Alamomi da hanyoyin warwarewa.

(b) Sihirin soyayya: Alamomi, yadda ake yi, sak**ako mara kyau, da hanyoyin warwarewa.

Babi na bakwai: (7)

1- Magance matsalar rashin sha’awa ga mace ko namiji.

2- Bambanci tsakanin rashin haihuwa ta dabi’a da wanda aljannu s**a jawo.

3- Hanyoyin warkar da matsalar.

Babi na takwas: (8)

1- Kariya daga sihiri:

(a) Yin alwala.

(b) Sallah cikin jam’i.

(c) Tashi tsakar dare yin ibada.

(d) Neman kariya kafin shiga banɗaki da yayin saduwa da iyali.

Babi na tara: (9)

1- Maganin Kambun ido.

(a) Hujjoji daga Alƙur’ani da Hadisai kan tasirin Kambun ido.

(b) Bambanci tsakanin Kambun ido da hassadar zuciya.

Littafin dai ya haɗa da bayanai dalla-dalla da hanyoyin warware matsalolin da s**a shafi sihiri da hassada a rayuwar Musulmai.

Duk mai bukatar sanin amfanin wani magani ko wani ko yadda ake magane wata cuta ko tambaya akan abubuwan da mu ka kawo zai iya rubuta mana a comment, za mu kawo, insha Allah.

Ga ma su bibiyarmu a facebook sunan shafina 'Bashir Halilu'. Masu son kallon video ta tiktok kuma sai duba 'Shafin Bashir Halilu'.
Lambar waya 08162600700, 08134434846.

YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN DA KE KONA AL-JANI DA KASHE SHI.Daga cibiyar Sunnah Medicine, masu yin Ruq'yah da harhada magu...
21/12/2024

YADDA AKE HADA MAGUNGUNAN DA KE KONA AL-JANI DA KASHE SHI.

Daga cibiyar Sunnah Medicine, masu yin Ruq'yah da harhada magunguna na
Musulunci. Lambar waya 08162600700.
1- A samu Kaikayi-koma-kan-mashekiya, tazargade, jema, hiltit da nono. Sai a hada
su waje daya a dafa. Idan an dafa sai a raba biyu, rabi a dinga zubawa a nono ana
sha, rabin kuma a dinga yin wanka da shi. Yana maganin farfadiya da Jinnul katfa masu make mutane, da ciwon 6arin jiki wanda Aljanu su ka haifar.
2- Kwankawatsen mahauta, tsamiyar makiyaya, da bakin bunu. Sai a hada su waje
daya a dinga hayaki da shi a jiki kullum, don maganin bakaken Aljanu. Yana kuma hana Aljanu shiga gida da ra6ar wajen da aka turara saidai yana karya magunguna marasa karfi da suke kusa da shi.
3- Ma'ul wardi, ma'ul khal da kuma alkahauli, sai a hada su waje daya, a hada da ruwa kadan a dinga shafe jiki da shi. Yana toshe hanyoyin da Aljanu suke shiga jikin mutane yana kuma fitar da su cikin gaggawa.
4- Tsakin kuka, bintil sudan, sassaken dogon yaro da kuma furen tumfafiya. Sai a hada su waje daya a daka, a jika a cikin turaren, a dinga shafe jiki da shi. Sariqul jinni, rariyar hannu da namijin dare, duk wannan hadin yana maganinsu.
5- Ma'ul wardi, ma'ul khal, hiltit da zuma. A jada su waje daya, a dinga zubawa a ruwa, ana sha, kullum sau daya. Idan Aljanu s**a rikewa mutum baki ya kasa magana bakin zai bude. Yana maganin ciwin ciki da kirji da mara, wadanda Aljanu s**a haifar.
6- Jan kajiji, bakin kaji, habbatus saudaaa, habbatur rashad, farar wuta da kuma tafarnuwa. A hada su a daka. Sai a raba biyu, rabi a kwa6a da man kadanya a dinga shafe jiki da shi, rabin kuma a dinga yin hayaki da shi. Yana maganin ciwon daji da kansar mama da fatar da Aljanu s**a 6ata. Yana hana Aljanu shiga jikin mutum yana kuma korarsu daga gida.
7- Nonon giwa, jan miski, kustul hidiy, farar wuta, man gelo, da ma'ul khal. A hada su waje daya, sai a dinga shaka, kullum sau uku. Yana fitar da Aljani daga jikin mutum nan take. Yana maganin ciwon kai da ciwon kirji wadanda Aljanu su ka haifar yana kuma saurin kona Aljani da kashe shi.
8- Turaren Ambar, turaren za'afaran, jan miski, bakin miski, da kuma man juda. A hada su waje daya, a dinga shafe jiki kullum idan za a kwanta barci da adaddare. Yana maganin namijin dare da mugwayen mafarkai da figita da rashin barci wanda Aljanu su ka haifar.
9- Man juda, habbatus saudaa, man zaitun, man gelo, zuma da man tafarnuwa, a hada su waje daya, a dinga shan cokali daya kullum. Yana saurin kashe Aljani har lahira, yana magani cututtuka da Aljanu su ka saka a jikin mutum.
10- Bakin hayaki, bakin bunu, da kuma baduhun shuri. A hada su waje daya, a dinga hayaki kullum sau biyu amma hayakin daki da gida ake turarawa. Yana korar Aljanu da suke zaune a gidan mutane ko wajen aiki sannan yana fitar da Aljani daga jikin mutum.
11- Turar ruwa, gashin jima, Fusuhul jinni, da hiltit. A hada su waje daya, a dinga hayaki kullum sau daya. Wannan hadin yana karya sihiri yana maganin yawan faduwar gaba da 6acin rai mara dalili da ciwon kan lokacin magriba da jin haushin mutane ba dalili.
12- Buruku, ganyen raidore, duman rafi da kaikayi-koma-kan-mashekiya. A tafasa a dinga sha da wanka. Maganin Kowace irin lalura ta Aljanu wacce ta shafi cikin jiki.
13- Sassaken gawo, kaikayi koma kan mashekiya, sassaken katsari. A dafa, sha da wanka. Yana magani sammu da maita da baki da kambun ido.
14- Ganyen sarkakiya, ganyen sidr da garin sabara. A dafa su tare, a dinga sha. Maganin kowace cuta ta jinnu wacce take cikin jiki.
15- Sabulun zaitun, sabulun habba, tafarnuwa, ganyen magarya da jan miski. A hada sabulan waje daya, sai a kir6a tafarnuwa a zuba ma ta ruwa a matse, a zuba acikin sabulun da turaren a dinga wanka da shi. Yana gyara fata wacce Aljanu su ka 6ata sannan yana toshe hanyoyin da Aljani ke bi domin shiga jikin mutum.
16- Bakin magani, sanamakiy, garin sabara, da kuma garin rawaya kadan. Sai a tafasa da lemon tsami ko tsamiya, idan ya huce a dinga sha. Maganin kowacce laurara wacce Aljani ya saka a cikin jiki.
17- Ganyen kaba da kuma jema. A jika su a sabuwar tukunyar kasa a dinga sha. Yana maganin fitsarin kwance na manya da yara, yana maganin maita da Aljanu mazauna cikin gida.
18- Shuhurul jinni, du'a'ul jannnah da muhriqul jinni. A daka muhriqul jinnin a jika shi acikin turarukan, a dinga shafe jiki da shi. Yana maganin Aljani mai taurin naci, yana hana shi shiga jikin mutum.
19- Azfarul jinni da shajaratu Maryam. A jika su tare a dinga sha. Magani ciwon ciki, matsalar nakuda, kwanciyar ciki da yawan 6ari. Tana bin Aljani duk inda ya shiga ajikin mutum ta fitar da shi cikin sauki da yaddar Allah.
20- Kanwa, gishiri da albasa. A hada su waje daya, a jika a cikin kwarya, a dinga sha. Yana magani cutar Aljani tare da karya sihiri cikin sauki.
21- Farin hayaki, tazargade, ganyen kaba, da habbatussauda. A hada a dinga hayaki da su. Maganin namijin dare, maita da sauran cututtukan Aljanu.
22- Ganyen na'ana'a, raihan, jema, zuma da kuma garin bakin bunu. A dinga dafawa ana yin shayi da su. Yana maganin rashin gane karatu, shirita da fitar da sihiri daga jikin mutum.
23- Kamfani, bintil sudan, jan miski, shuhurul jinni, ma'ul jinni. A hade su waje daya, a dinga shafe jiki da shi. Yana hana Aljani shiga shiga mutum yana kuma fitar da wanda yake ciki.
24- Kafoor mash'hoor, gadali, man kadanya a hada waje daya a dinga shafawa a hannu da kafafuwa. Yana toshe hanyoyin da Aljani yake bi domin shiga jikin mutum.
25- Ganyen aduwa, ganyen magarya, ganyen dinya da ganyen sarkakiya. A dinga dafawa, sha da wanka. Maganin kowace irin cutar Aljani ta cikin jiki.
26- Garin sanya, hannu, fasakwari, sassaken 6aure, bakin magani. A dafa a dinga sha amma sanyar kadan ake zuba ta. Maganin fitsarin kwance, firgita da mugwayen mafarkai.
27- `Ya`yan zurman, bakin algaru, jan algaru ganyen tumfafiya. A hada waje daya a dinga turarawa acikin gida da cikin dakuna. Yana korar Aljanu daga gida kuma yana hana Aljanu shiga gidan.
28- Jan miski. `ya`yan zurman, man juda, Kafoor mash'shoor. A hada su waje daya a dinga shafawa a ga6o6in jiki guda talatin. Yana toshewa Aljani hanyar shiga jikin dan'Adam.
Daga cibiyar Sunnah Medicine, masu yin rukiyyah da harhada magungunan musulunci. Lambar waya 08162600700.
AMMA A KULA
Ya k**ata duk wanda zai yi amfani da wadannan magunguna to ka tuntu6i masani akan fannin magani domin yay maka bayanin gwargwadon yadda za kay amfani da kowanne sannan a ware ma ka maganin da mace mai ciki ba ta sha da wanda ba a baiwa kananan yara da dai sauran dokoki da su ka danganci magani.
Ga wanda yake bukatar wadanda muke hadawa.
Muna sayarda dukkan magungunan da mu ka ambata, muna sayarda wadanda aka riga aka hada su, amfani kawai za kay da su. Kamar Magungunan sha, da na shafawa dana hayaki dana fesawa a cikin gida da dai sauransu. Za a iya tuntu6armu a lambobin waya 08162600700
Muna yin rukiyyah tare da hada magungunan musulunci.

Daga shafin Sunnah Medicine, masu yin Ruq'yah da harhada magunguna na musulunci.
Lambar waya 08162600700.
YADDA ZA KA GANE KANA DA ALJANI KO KUMA AN YI MA KA ASIRI. Daga shafin Sunnah Medicine

1. Mutum ya zama ba ya son karatun Alkur'ani ko saurarensa

2. Rashin son yin ibada k**ar sallah, ko a yi ta cikin bacin rai da kasala.

3. Yawan ciwon kai mai tsanani ko 6arin kai ko kuma jiri.

4. Yawan ciwon mara ko baya ko kwankwaso ko kuma ciki wanda ba ya jin magana kuma an rasa me ke kawo shi.

5. Yawan jin tafiyar wani abu a jiki k**ar kiyashi ko tsutsa ko kwarkwata tana yawo a kai amma idan an duba ba za a ga komai ba.

6. Yawan mafarke mafarke na abun tsoro ko firgirta da surutai a cikin bacci ko kuma mutum ya ji wani abu mai nauyi ya danne shi ko ya shake masa wuya.

7. Yawan jin tsoro ko faduwar gaba ko wani abu ya dinga yi ma ka gizo ko kuma ka ji k**ar ana kiran sunan ki amma ba za ka mai kiran ba.

8. Yawan jin sanyi ko zafi ko rikewar kafa ko wani sashe na jiki ba tare da wani sanannen dalili ba.

9. Rashin iya bacci da daddare ko yawan jin motsin wani abu ko surutai ko kuma takun tafiya.

10. Rashin son yin kitso ko aski kuma a taba m ka/ki kai.

11. Yawan bacin rai ko jin haushin mutane ba tare da wani dalili ba.

12. Rashin son shiga cikin mutane ko yawan zargin su ko kuma yawa rigima da su.

13. Yawan kuka ko dariya ko murmushi ba tare da wani dalili ba.

14. Yawan jin k**ar ana yi ma ka rada a kunne ko a ringa raya ma ka zuciya akan ka aikata wani lefin k**ar kisan kai ko zina ko kuma sata

15. Rashin son yin Aure ko korar samari ko kasa tsayar da guda daya kwakwara. Haka ma ga namiji abun ya ke.

16. Daukewar Sha'awa ko rashin jin dadin saduwa da muji ko kuma tsanar sa da wulakan tashi ba tare da wani dalili ba. Shi ma namiji haka zai dinga ji.

17. Yawan kallon mudubi ko Sha'awar kallon tsiraici.

18. Yawan son kade-kade da raye-raye.

19. Yawan son dare ko cikin duhu ko yin shuru k**ar ba ka gurin.

20. Rikicewar Jinin Al'da ko na Nifasi ga mace.

21. Rashin Haihuwa ko yawan Bari ko Haihuwar dan babu rai ko kuma wasu matsaloli su biyo bayan Haihuwa k**ar jijjiga.

22. Aikata wani abu ba a cikin hankalinka ba, sai daga baya ka ringa nadama ko mamakin yadda akayi ka aikata.

23 Yankewar jiki a fadi kasa ba a cikin hayyaci ba ko kuma ihu da rugawa a guje ba tare da ka san inda za ka ba.

24. Yawan wasuwasi ko mantuwa acikin dukkanin Al'amura musamman a lokacin ibada.

25. Tabuwar kwakwalwa ko kasa fahimtar ko wane irin abu.

26. Rashin tsafta da son zama cikin kazanta da dauda.

27. Yawan fita waje mara dalili ko tarewa a wani wuri k**ar karkashin bishiya, kan bola, bandaki, jeji, bakin ruwa, da sauran su.

28. Rashin lafiyar da za'a kasa gane kanta.

29. Rashin son Wa'azi ko zama da mutanen kirki.

30. Yawan jin tsoron Rukuya ko masu yinta. Allahu Ta'ala A'alam

Daga cibiyar Sunnah Medicine, masu yin Ruq'yah da harhada magunguna na musulunci da na gargajiya.
Lambar waya 08162600700

ILLOLIN MA********ON DA HANYOYIN MAGANCE SUMa********on ko kuma Istimna'i a Larabce,  shi ne wasa da tsaraici don biyawa...
20/12/2024

ILLOLIN MA********ON DA HANYOYIN MAGANCE SU

Ma********on ko kuma Istimna'i a Larabce, shi ne wasa da tsaraici don biyawa kai bukatar sha'awar jima'i.

Bayan Addinin Musulunci ya haramta Istimna'i wato Ma********on, to kuma yana da illoli da cututtuka da yake haddasawa a jikin mutum.

Yana janyo:-

1- Yawan mantuwa. Duk mai wannan aiki zai gamu da yawan mantuwa da shiririta.

2-Yana rage hazaqar kwalwa. Duk karatun da mutum yake ganewa zai dawo ya dena fahimta.

3- Kankancewar gaba da
maraina ya koma k**ar na yaro karami ko ya tattare ya dinga komawa ciki.

4-Saurin kawowa yayin jima'i. Wani ko minti daya ba ya iya yi, yayin tarawa da iyalinsa sai ya ji ya kawo kuma ba zai iya komawa ba.

5-Ramewa. Mutum zai ta ramewa, komai cin abincinsa da shan magunguna kara kiba.

6-Rashin karfin mazakuta har ta kai in yay aure ba ya iya gamsar da iyalinsa.

7- Mazakutar namiji tana iya karyewa, ya zama kwata-kwata ya dena tashi, sedai ya dinga dan motsawa kadan.

8- 'Karancin sha'awa bayan aure.

9-Karancin maniyy. Wanda hakan yake da illoli da yawa, k**ar haifar da rashin gamsar da iyali, rashin iya haihuwa da dai sauransu.

10-Raunin jiki, duk mai yin ma********on yanay wa jikinsa asarar wasu sinadarai masu kara kuzari. Don haka zai zama mai raunin jiki.

11-bushewar fatar kan zakari ya dinga wani abu k**ar 6awo ko `kanzo.

12- Tsargiya, fitsarin jini. Yin ma********on kan sa mutum ya ga yana fitsarin jini, ko in yay ma********on din ya ga ya taho har da jini.

13- Watery s***m. Yana sa maniyyin mutum ya tsinke ya zama k**ar ruwa kuma mara kauri, wanda hakan ke nuna dakyar in mutum zai iya haihuwa.

14- Yana sa mutum haka kawai ya ji yauqi yana fito masa koda bai yi ma********on din ba.

15- Idan ma********on ya ratsa mutum, to in bai yi ba ba zai iya bacci ba.

16- In ya sarqi mutum to in ya kwana biyu bai yi ba sai ya yi ciwon ciki k**ar zai mutu.

17-Mace mai yin ma********on yana jawo mata doyin farji. Wato jin wari yana fitowa ta gabanta.

18- Ganin wani farin ruwa yana fitowa.

19- Kaikayi da kurajen gaba.

20- Yana kawarwa da mace budurcinta.

21- Yana kawo zubewar nono ga mace.

22- Yana sa mace ta dena sha'awar namiji samsam.

23-Koda mutum yay aure in ya tara da iyalinsa to se ya kara da ma********on sannan yake samun cikakkiyar gamsuwa. Idan mace ce ma haka.

24- Yana iya sa wa idan mutum ya girma ya kasa rike fitsari.

25- Ma********on hanya ce ta afkawa cikin zina da madigo da mak**antansu.

26- Yana rage lafiyar idanu.

SHAWARA.
Dole mutum ya yi kokari ya dena Istimna'i sannan ya yi amfani da magunguna da za su dawo masa da abubuwan da ya rasa a jikinsa.

Ga wani magani mun hada shi musamman saboda wadanda su ka dauki lokaci suna yin Istimna'iy suyi amfani da shi don dawo musu da lafiyarsu amma wannan maganin ba wai yana hana mutum yin ma********on bane, a'a, yana dai dawowa mutum da abubuwan da ya rasa ajikinsa da kuma inganta masa lafiyarsa. Mata da maza za su yi amfani da shi, masu aure da marasa aure.

Lambar waya don samnun wannan magani 08162600700.

SARIQUL JINNI سارق الجن `Barawon Aljani.Aljanu masu satar kayan mutane.Galibin wadannan Aljanu a gidajen mutane suke zau...
09/01/2024

SARIQUL JINNI سارق الجن

`Barawon Aljani.

Aljanu masu satar kayan mutane.

Galibin wadannan Aljanu a gidajen mutane suke zaune da kuma kasuwanni.

Suna iya satarwa mutane kudi, abinci da kuma sauran kayan amfani.

Waddannan Aljanu wato Sariqul Jinni s**an iya sato kayan mutane su kawo gidanka su ajjiye ko su ajjiye a aljihun mutum ko cikin kayansa.

Sannan suna aron kayan mutane daga baya su dawo musu da shi.

Sariqul Jinni suna da hadari sosai domin suna hada gaba da zargi a tsakanin mutane.

Hakanan suna da taurin kai sosai, ba sa rabuwa da mutum ko gidan mutane ta dadi.

Irin wadannan Aljanu su ne Bokaye masu buga kudi suke yin amfani da su ta hanyar saka su su sato musu kudaden jama'a.

Ashararain mutane suna iya yin Sihiri su tura Sariqul Jinni jikin wani mutum ko gidan wani mutum don su dinga satar masa dukiya suna 6atar masa.

Hakai dai Bokaye suna iya tura su jikin mutum, sai mutum ya zama tantirin 6arawo kuma yana yin satar ne ba a son ransa ba. Suna kuma iya shiga jikin mutum ta hanyar tsautsayi.

Sariqul Jinni sun dade a duniya. Domin Allah madaukakin Sarki ya yi bayani akan Aljanu masu satar ji a cikin Suratul Hijri da Suratus Saffati da Suratul Jinni da dai wasu surori na Alqur'ani.

SAHABIN MANZON ALLAH صلى الله عليه وسلم
YA K**A `BARAWON ALJANI

Aba Hurairata (RA) ya k**a Sariqul Jinni hannu da hannu.

An kar6o daga Aba Hurairata Allah ya kara yarda a gareshi, ya ce " Manzzon Allah صلى الله عليه وسلم
Ya wakiltani in kula da zakkar watan Azumin Ramadana. Sai ga wani ya zo yana satar abincin (da nake gadi).

Sai na k**a shi, na ce Sai na kai ka wajen Manzon Allah صلى الله عليه وسلم.

Sai ya ce min "WAllahi ni mabukaci ne kuma ina da iyali da yawa ga kuma tsananin bukata"

Sai na rabu da shi.

Da gari ya waye sai Manzon Allah صلى الله عليه وسلم
Ya ce "Ya kukai da bakonka na jiya?"

Sai na ce Ya Ma'aikin Allah, ya koka min tsananin bukata da kuma yawan iyali. Sai na tausaya masa na kyale shi.

Sai Manzon Allah صلى الله عليه وسلم
Ya ce "Karya yake kuma zai dawo"

Saboda haka sai nay tarkonsa.

Sai kuwa gashi ya dawo yana satar abincin. Sai na k**a shi, na ce to wAllahi sai na kai ka wajen Manzon Allah صلى الله عليه وسلم
Domin karo uku kenan ina k**a ka. Se kay rantsuwa ba za ka dawo ba sai kuma ka dawo.

Sai ya ce "To ka kyale ni se in koya maka wasu kalmomi wadanda Allah zai sa ka amfana da su".

Sai na ce Wadanne ne?

Sai ya ce "Idan ka je wajen kwanciyarka, ka karanta Ayatal Kursiyyu har karshen ayar. To Akwai me gadi da Allah zai saka maka kuma Shaidan ba zai iya kusantarkaba har sai ka wayi gari".

(Da Manzon Allah صلى الله علي وسلم
Ya ji haka sai ya ce "Amma fa shi (wannan mai zuwar maka da daddaren) makaryaci ne, sai dai gaskiya ya gaya maka. Ya Aba Hurairata ka san ko da wa kake gamuwa har sau ukun nan?"

Sai na ce A'a.
Sai ya ce "Shaidan ne"

Daga wannan hadisi za mu fahimci cewa lallai Shaidanun Aljanu suna zuwa su saci kayan mutane.

YADDA MUTUM ZAI GANE SARIQUL JINNI YA SHAFE SHI.

Kalli bidiyoyinmu acikin wannan shuɗin rubutun
https://www.youtube.com/
Lambar waya 08162600700, 08134434846.

1- yawan 6atan kudi da kayan amfani kuma a rasa wanda ya dauka.

2- yanzunnan za ka ‘kirga kudi ka sa a aljihu ko wani abu amma in ka sake ‘kirgawa sai ka ga sun ragu.

3- duk irin 6oyewar da kay wa kudin ka sai ka ga an ta6a ma ka ko an dauke gaba daya.

4- zaka dinga yawan ganin an yi ma kaca-kaca dakayan ka, an yi ma bincike kuma ba ka san kowaye ba.

5- za ka ajjiye kayanka ko kudi sai ka ga an canja musu waje.

6- wani abinka zai 6ata, sai ka gaji da nema kaha‘kura sai kuma ka gan shi daga baya .

7- za ka ji kana da sha‘awar ka dauki kudin da bana ka ba ko wasu kaya koda kuwa ba abinda za kai da shi.

8- idan yaro yana da Sariqul jinni zai dinga yawan dauke-dauke kayan mutane da kudinsu kuma in an caje shi ba za a ga komai ba.

9- Za a dinga ganin yaro da kudi, in an tambaye shi a ina ya samu zai ce shi ma bai sani ba domin Aljanin ne ya sato ya saka masa.

10- Mai Sariqul jinni za a dinga yawan ‘kala masasatar da bai ji ba bai gani ba: don kuwa Aljanin nezai yi satar sai a ce kai ne.

11-Mutum zai ajjiye kudinsa amma sai ya tashi dauka sai ya ga sun zama takardu ko qasa ko kuma ganye.

SARIQUL JINNI TA HANYAR SIHIRI

Wani lokacin ana iya hada baki da Boka ya tura wa mutum Sariqul jinni don ya dinga yi ma sa 6arna acikin dukiyar sa.Shi kuma bayan alamomin da mu ka ambata asama to zai dinga fama da wadannan:-

1- karyewar kudin mutane a ka.

2- zai kasa kaya ai ta siyan na kowa amma a ‘kikallon na sa (don kuwa Aljanin ne zai lullu6e ma kayan ba wanda zai gan su)

3- ta6ar6arewar harkar ciniki.

4- kudi za su lalace amma ka rasa abinda ka siya dasu.

5- fama da matsanancin ciwon kai musamman dab da Magriba.

6-yawan faduwar gaba.

7- 6acin rai mara dalili.

7- za ka dinga mafarkin ana bin ka a guje ko anakokawa da kai.

8- za ka ji sam ba ka son fita kasuwa.

9- in kana kasuwa sai hankalin ka yai ta tashi,amma da ka dawo gida ko ka tafi wani wajen shikenan sai ka dena.

10-fada da abokan ciniki

11- za ka ji k**ar ana kiran sunan ka amma ba kaga kowa ba.

12- ko wani ka ba wa kudi indai na ka ne sai an yima sa sata.

Daga shafin Bashir Halilu mai Rukiyyah da bayarda magunguna na Musulunci dana gargajiya. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

Kalli bidiyoyinmu acikin wannan shudin rubutun
https://www.youtube.com/

YADDA ALJANU SUKE HAWA SAMA DOMIN SATO MAGANAR MALA'IKUhttps://www.youtube.com/A cikin Alqur'ani mai tsarki, Allah Maɗau...
03/01/2024

YADDA ALJANU SUKE HAWA SAMA DOMIN SATO MAGANAR MALA'IKU

https://www.youtube.com/

A cikin Alqur'ani mai tsarki, Allah Maɗaukakin Sarki Ya yi magana akan masu hawa sama ko ƙoƙarin hawa sama, domin su saurari irin maganganu da Mala'iku suke yi, don su dawo ƙasa su dinga sanar da Bokaye da kuma yadda Allah Maɗaukaki Ya tanadi wasu taurari a sama masu jefe irin waɗannan Shaiɗanun masu yiwa Mala'iku laɓe.

Ka duba tafsirin Aya ta 23 cikin Suratu Saba'i da Ayah ta 7 cikin Suratus saffati da Ayah ta 18 cikin Suratul Hijri da dai wasu gurare da dama a Alƙur'ani, domin ganin yadda Allah Mai girma da ɗaukaka Yai bayani akan satar bayani da wasu Shaiɗanu suke yi daga Mala'iku domin su sanar da Bokayae, su kuma Bokaye su dinga taƙamar cewa sun san gaibu.

Yanzu ga wani Hadisi wanda bayani ya zo daga bakin Manzon Allah (SAW) game da yadda Aljanu suke hawa sama domin satar maganar Mala'iku da kuma abinda ya ke kasancewa.

روى البخاري عن أبي هريرة رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال:

إذا قضى الله الأمر في السماء ضربت الملائكة بأجنحتها خضعاناً لقوله، كأنه سلسلة على صفوان ينفذهم ذلك. حتى إذا فُزِّع عن قلوبهم قالوا: ماذا قال ربكم؟ قالوا: الحق وهو العلي الكبير فيسمعها مسترق السمع ـ ومسترق السمع هكذا بعضه فوق بعض ـ وصفه سفيان بكفه فحرفها وبدد بين أصابعه ـ فيسمع الكلمة فيلقيها إلى من تحته، ثم يلقيها الآخر إلى من تحته، حتى يلقيها عن لسان الساحر أو الكاهن فربما أدركه الشهاب قبل أن يلقيها، وربما ألقاها قبل أن يدركه، فيكذب معها مائة كذبة فيقال: أليس قد قال لنا يوم كذا وكذا: كذا وكذا فيصدق بتلك الكلمة التي سمعت من السماء.
صحيح.

Daga shafin Bashir Halilu mai Ruq'yah da bayarda magunguna na musulunci da na gargajiya. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
Kalli cikakken wannan bayani acikin bidiyo acikin wannan shuɗin rubutun
https://www.youtube.com/.
Wannan hadisi ya zo da ruwayoyi daban-daban amma za mu yi bayanin ma'anarsa tare da shigar da bayanin sauran ruwayoyin acikin fassarar.

Acikin wannan sahihin Hadisi da Bukhari ya ruwaito, Manzon Allah SallAllahu alaihi wa sallama ya ce

"Idan Allah Ta'ala Ya yanke wani hukunci a sama, wato acikin fadarsa, sai sama ta k**a girgiza mai ƙarfi ko ko kuma tsawa mai ƙarfi, sai kuma Mala'iku su dinga bubbuga fuka-fukansu, don nuna girmamawa ga umarnin Allah Maɗaukakin Sarki, kai ka ce sarƙa ake bugawa akan fan dutse kuma su faɗi suyi sujjada. Har sai sun samu nutsuwa tukuna, sai ya zamanto Mala'ika Jibrilu shi zai fara ɗago kansa, sai Allah Maɗaukakin Sarki Ya sanar da shi abinda ya nufa. Daga nan sai sauran Mala'iku su dinga cewa "Me Ubangijinmu ya ce ya Jibrilu?". (Ma'ana wane umarni Allah Ya bayar?). Sai ya ce "Allah Ya yi umarni na gaskiya ne, kuma shi ne Maɗaukaki mai girma.
Dukkan saman da Mala'ika Jibrilu ya wuce sai Mala'iku su ce masa" "Me Ubangijinmu ya ce Ya Jibrilu? ". Shi kuma sai ya ce gaya musu abinda Allah Ya sanar da shi.

Sai Mala'iku su dinga gayawa ƴan uwansu Mala'iku cewa Allah Ya ce za a yi kaza da kaza a duniya. Suna cikin wannan magana ne sai Aljanu masu sauraron maganar Mala'iku su ji wannan zance da Mala'iku suke yi, sai Aljanin da ke can kusa da sama ya gayawa Aljanin da ke ƙasansa abinda ya ji, shi ma ya gayawa na ƙasansa. Kowane in ya tashi sai ya ƙara ƙarya ɗari cikin abinda ya ji, sannan ya gayawa na ƙasa da shi. Sun kasance suna hawa sama ta hanyar wani ya taka kafaɗar wani, shi ma wani ya hau kan kafarsa har izuwa sama. Haka za su yi ta gayawa junansu wannan magana da su ka jiyo daga sama, har zuwa na ƙasansu, wanda shi kuma zai je ya gayawa Boka cewa abu kaza zai faru a duniya rana kaza a waje kaza. To wani sa'in Aljanin ya kan samu dama ya faɗawa ɗan uwansa zancen da ya jiyo, wani sa'in kuma kafin ya faɗa sai tauraro ya jefe shi, ya kashe shi.
To daga nan sai Bokan ya dinga gayawa mutane cewa abu kaza zai faru rana kaza, sai kuma a ga abun ya faru. Sai ka ji mutane suna cewa 'Ai rannan ya ce da mu abu kaza zai faru, kuma abun ya faru da gaske'. Sai su dinga gasgata shi saboda wannan kalma da aka jiyo daga bakin Mala'iku a sama.
Bukhari ne ya ruwaito shi, wasu sassansa kuma daga wasu Malaman ne.

https://www.youtube.com/

Acikin wanna ƙissa za mu fahimci cewa

1) Aljanu suna iya zuwa wani waje mai nisan gaske acikin sararin samaniya, ta yadda suke iya jin maganganun da Mala'iku suke tattaunawa akan abubuwan da za su faru a duniya.

2) Aljanu ba sa iya tunkarar Mala'iku domin su samo labarin abinda zai faru a duniya, sai dai suyi masu laɓe, su sato wata kalma ba tare da Mala'ikun sun sani ba.

3) Aljanu da Mala'iku dukkansu ba su san gaibu ba, har sai Allah Ya kira Mala'ika Jibrilu Ya sanar da shi, sannan su sani.

4) Aljanu suna iya kaiwa inda za su ji maganar Mala'iku ne ta hanyar taka kafaɗun junansu, wannan ya hau kan wannan, wannan ya hau kan wannan, har su isa zuwa sama.

5) Ba kowane lokaci ne Aljanu suke samun damar satar maganar Mala'iku ba, domin wani lokacin tauraro yana jifansu, ya kashe su kafin su kawo zancen zuwa duniya.

6) Ainihin maganar da Aljanu su ka jiyo a sama ba ita suke kawowa ƙasa ba, sai sun ƙara ƙarerayinsu aciki sannan su kawowa Boka, shi ma ya ƙara ƙaryarsa sannan ya sanar da mutanensa.

7) Abinda Bokaye suke gayawa mutane yawanci ƙarya ne, sama da 99% ƙarya ne, sauran kuma irin maganar da aka sato daga Mala'iku ce, sai ka ga sun faɗi abu kuma ya faru. Shi ne dalilin da ya sa wasu suke gasgata Bokaye.



8) Malamai sun yi bayanin cewa ba kowace magana ce ake barin Aljanu su jiyo ta daga sama ba, misali wahayin da ake kaiwa Annabawa, ba a bari wani Aljani ya san da wannan magana kafin ta je ga Annabin Allah.

Kalli cikakken wannan bayani acikin bidiyo acikin wannan shuɗin rubutun
https://www.youtube.com/.

Daga shafin Bashir Halilu mai Ruq'yah da bayarda magunguna na musulunci da na gargajiya. Lambar waya 08162600700, 08134434846.

24/12/2023

AYATUSH SHUFA'I

بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمَـٰنِ الرَّحِيمِ
• « قَاتِلُوهُمْ يُعَذِّبْهُمُ اللَّهُ بِأَيْدِيكُمْ وَيُخْزِهِمْ وَيَنْصُرْكُمْ عَلَيْهِمْ وَيَشْفِ صُدُورَ قَوْمٍ مُؤْمِنِينَ» الآية 14 من سورة التوبة.

• «وَإِذَا مَرِضْتُ فَهُوَ يَشْفِينِ» الآية 80 من سورة الشعراء.

• « يَا أَيُّهَا النَّاسُ قَدْ جَاءَتْكُمْ مَوْعِظَةٌ مِنْ رَبِّكُمْ وَشِفَاءٌ لِمَا فِي الصُّدُورِ وَهُدًى وَرَحْمَةٌ لِلْمُؤْمِنِينَ » الآية 57 من سورة يونس.

• « ثُمَّ كُلِي مِنْ كُلِّ الثَّمَرَاتِ فَاسْلُكِي سُبُلَ رَبِّكِ ذُلُلًا يَخْرُجُ مِنْ بُطُونِهَا شَرَابٌ مُخْتَلِفٌ أَلْوَانُهُ فِيهِ شِفَاءٌ لِلنَّاسِ إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَةً لِقَوْمٍ يَتَفَكَّرُونَ » الآية 69 من سورة النحل.

• « وَنُنَزِّلُ مِنَ الْقُرْآنِ مَا هُوَ شِفَاءٌ وَرَحْمَةٌ لِلْمُؤْمِنِينَ وَلَا يَزِيدُ الظَّالِمِينَ إِلَّا خَسَارًا » الآية 82 من سورة الإسراء.

• « وَلَوْ جَعَلْنَاهُ قُرْآنًا أَعْجَمِيًّا لَقَالُوا لَوْلَا فُصِّلَتْ آيَاتُهُ أَأَعْجَمِيٌّ وَعَرَبِيٌّ قُلْ هُوَ لِلَّذِينَ آمَنُوا هُدًى وَشِفَاءٌ وَالَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ فِي آذَانِهِمْ وَقْرٌ وَهُوَ عَلَيْهِمْ عَمًى أُولَئِكَ يُنَادَوْنَ مِنْ مَكَانٍ بَعِيدٍ » الآية 44 من سورة فصلت.

AMFANIN ZA'AFARAN DA AMBAR DA KUMA ALMISKI WAJEN KYAUTATA LAFIYA.Daga Shafin Sunnah Medicine, masu yin Ruq'yah da harhad...
22/12/2023

AMFANIN ZA'AFARAN DA AMBAR DA KUMA ALMISKI WAJEN KYAUTATA LAFIYA.

Daga Shafin Sunnah Medicine, masu yin Ruq'yah da harhada Magunguna na Musulunci. Lambar waya 08162600700.

1) ZA'AFRAN.
Shi Za'afaran wata ciyawa ce ko kuma tsiro mai dauke da launi mai abin sha'awa, galibi jar ciyawa ce ko yaluwa. Da akwai man Za'afran, da akwai turarensa kuma ana samun ciyawar tasa ma.
Ana amfani da shi wajen sinadarin girki kuma yana maganin cututtuka da dama yana kuma kyautata lafiya.

An fara noman Za'afaran ne a wajejen Greece. Sannan akay Safararsa zuwa Yammacin Amurka da kuma kasashenmu na Afrika.

Za'afaran yana maganin cututtuka k**ar:

★Zubewar Gashi.
Shafa Man Za'afaran a fatar kai yana maganin sanqo. Hada Za'afaran da madara a shafa a kai yana maganin zubewar gashi kuma yana kara yawan gashi.

★Gyaran Fuska
Hada Za'afaran da madara a shafa a fuska a hankali amma a kaucewa ido. A bar shi tsawon minti goma sha biyar sannan a wanke da ruwa yana sa fuska tay kyau da sheqi. Ana yin wannan hadin sau daya a sati.

★Matsalolin fata.
A jika ciyawar Za'afaran a ruwa tsawon awa biyu zuwa uku. Sai a shafe fatar jiki da shi. Yana bada fata mai laushi da taushi. Ana yin haka sau biyu zuwa uku a sati.

★Maganin kuraje.
A hada Za'afaran da Ray'han a kir6a a shafa akan fata sai a wanke bayan minti goma. Wannan hadin yana maganin kuraje, kyasbi, makero da tabo da kuma sauran cututtukan fata.

★Kwayoyin Cuta.
Zuba ko fesa Za'afaran a waje yana maganin kwayoyin cututtuka da ba'a iya ganinsu kuma yana kyautata lafiya.

★Kyautata Bugun Zuciya.
Za'afaran yana da sinadarin potassium wanda ke kyautata bugawar zuciya da kuma bata damar yin aikinta yadda ya k**ata.

★Zagayawar jini.
Za'afaran yana da sinadarai irinsu coper, potassaium, calcium, manganese, iron, magnesium, da zinc da kuma selenium. Wasu daga cikin wadannan sinadarai suna taimakawa wajen daidaita yanayin jini a jikin mutum.

★Rigakafin Cutar Kansa (cancer).
Za'afaran yana dauke da wasu kananan sinadarai k**ar zea-xanthin da lycopene wadanda ke kare jikin mutum daga kamuwa da cutar Kansa wato Daji.

★Saukaka Narkewar Abinci.
Za'afaran yana da muhimmanci wajen saukake narkewar abinci a jikin mutum saboda sinadarin anti-cinvulsant da sauran sinadarai dake cikinsa.

★Ciwon Hakori.
Shafa Za'afaran hade da Zuma yana taimakawa wajen maganin cututtukan dasashi da hakori.

★Cututtukan Cikin Baki.
Idan aka hada Za'afaran da Zuma da Graceline ana shafawa a cikin baki yana maganin kuraje da sauran cututtukan da kan iya samuwa a cikin baki.

★Gyaran le6e.
Za'afaran yana cikin tsirrai kadan wadanda ke samar da sinadarin vitamin B2 mai yawa. Amfani da shi yana gyara la66a da kuma kyautata hadiyar abinci daga baki zuwa makogwaro.

★Maganin Sanyi da Tari.
Idan aka hada Za'afaran 1grm da ruwa 1ltr aka sha yana maganin Sanyi da kuma Tari.

★Jini lokacin Al'ada.
Za'afaran yana da kyau wajen daidaita zuwan jini yayin al'ada.

★Maganin Maza.
Amfani da Za'afaran yana taimakawa mazaje su dawo da karfinsu. Hatta tsofaffi yana ba su kuzari sosai.

★Maganin Aljanu da Sihiri.
Hada Za'afran da Jan Almiski da Ambar, a dinga shafawa a fata, yana maganin cututtukan Aljanu kuma yana taimaka wajen 6ata sihiri da ke jikin mutum.

★ Amma a kula ★

☆Yin amfani da Za'afaran ba bisa ka'ida ba zai iya sawa mutum:-

* Mura
*Ciwon Kai
da kuma
*Daukewar Miyau a baki.

★ Masana harkar lafiya ba suy bayanin illar Za'afaran ga mace mai ciki ba, sun ma dai ce yana taimaka mata.

Daga shafin Sunnah Medicine, Masu yin Ruq'yah da harhada Magunguna na Musulunci. Lambar waya 08162600700.

2)AMFANIN AMBAR GA LAFIYAR AL'UMA.

Ambar wani magani ne da ake samun sa daga jikin wata bishiya. Wato k**ar irin farin ruwan nan dake fita daga jikin bishiya. Shi ne ake hada
shi da wasu sinadarai a samar da Ambar. Kuma ana samunsa a jikin bishiyoyi da dama. Idan ku ka duba wannan hoton za ku ga hoton Ambar k**ar Qaro.

Bayan amfanin da Ambar yake da shi wajen kiwon lafiya, haka ma yana taimakawa wajen magance cututtukan jiki da na jinnu ko sihiri.

Ana iya hada Ambar da wasu magunguna k**ar zuma, miski, habba, zaitun, da dai sauransu, ayi amfani da shi don samun ingantacciyar lafiya

Yi amfani da Ambar kadan ka samu lafiya mai yawa da yaddar Allah.

Ana samun Anbar na gari, ana samun na ruwa, ana samun na turare, ana
samun kwa6a66e na shafawa .

★ Sanya nishadi.
Ambar yana sanya nishadi idan aka sha kilogram daya tare da zuma cokali daya.

★Kara karfin hakora.
Ambar yana kara karfin hakori idan ana goge hakora da man sa, wato Amber oil.

★Gyara kwakwalwa.
Man Ambar yana maganin cututtukan kwakwalwa idan ana shan sa tare da Man zaitun
da Habbatussaudaa.

★Maganin ciwon Hauka.
Ga mai lalurar hauka sai adinga tofa ayoyin Ruq'yah a cikin Ambar, a zuba a ruwa, a ba shi, ya sha kuma a dinga yi masa hayaki da shi musamman a
hada da miski wajen hayakin.

★Ciwon kai.
Ciwon kai bari guda sai a hada Ambar da jan miski da Man juda a kwa6a, a dinga shafawa a kan kuma ana yin hayakin sa.

★Lalata sihiri.
Ana amfani da Ambar ta hanyoyi da dama wajen 6ata sihiri wanda mutum ya ci ko ya sha.

★Hawan jini.
Masu hawan jini su sha Ambar kadan a cikin ruwa.

★Gyaran fata.
Don gyaran fata da jin dadin jiki, sai a diga Ambar kadan a cikin ruwan wanka ay wanka da shi.

★Dadin bacci.
Mai son yin bacci mai dadi shi ma sai ya zuba Ambar kadan a ruwan wankansa.

★Hutawar kwakwalwa.
Ambar yana taimakawa kwakwalwa wajen samun hutu mai dadi.

★Lafiyar zuciya.
Amfani da Ambar yana kara kyautata karfin zuciya.

★Asthma.
Masu cutar Asthma su ma Ambar yana taimaka musu idan suna amfani da shi.

★Gudanawar jini.
Amfani da Ambar yana kara kyautata gudanawar jini a jikin mutum.

★Karfin jima'i.
Yin amfani da Ambar yana kuma kara karfin jima'i ga maza da mata.

★Narkewar abinci.
Amfani da Ambar na saukaka narkewar abinci a cikin ciki, yana hana kumburin ciki, tusa da sauran matsalolin ciki.

★Dadin jiki.
Yana kara soyayya tsakanin miji da mata, idan dayan su yana amfani da
shi.

★ Warkewar ciwo da kashe kwayoyin cuta.
Sai a zuba man Ambar a kan
ciwon bayan an wanke shi. To zai warke cikin sauki insha Allah.

★ Amma a kula ★
Duk da amfanin Ambar kuma zai iya cutarwa .

★Mata masu ciki su guji amfani da Ambar, musamman sha a ciki.

★Ambar din da ba a gauraya shi da wani abu ba k**ar ruwa da mak**antansu, to a guji shan sa kai tsaye.

★Ba'a sa Ambar a cikin ido.

★A guji ajjiye Ambar kusa da yara.

Daga cibiyar sunnah medicine, masu yin Ruq'yah da harhada Magunguna na Musulunci. Lambar waya 08162600700.

3) AMFANIN ALMISKI

Shi Miski ba tsiro ba ne, ana samar da shi ne daga jikin Barewa, kuma Allah ya fade shi a Alqur‘ani.

Amfanin sa.

★ Yana maganin dafi kowane iri.

★ Yana kara karfin jiki.

★ Yana maganin hawan jini idan an sheka.

★Yana maganin Aljanu, ya kan ma iya kashe Aljani idan an hada shi da Za‘afaran ana shafawa, ana kuma iya zuba shi a garwashi a dinga hayaki.

★Yana maganin warin gaba idan ana shafawa.

★Yana maganin namijin dare.

★Yana taimakawa masu matsalar haihuwa idan suna matsi da shi bayan gma al'ada.

Akwai jan Miski akwai baki kuma akwai farin Almiski akwai kuma miski na ruwa.

Daga cibiyar Sunnah Medicine, masu yin Ruq'yah da harhada Magunguna na Musulunci.

Lambar waya 08162600700.

Address

Kano
Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sunnah Medicine Center posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Share on Facebook Share on Twitter Share on LinkedIn
Share on Pinterest Share on Reddit Share via Email
Share on WhatsApp Share on Instagram Share on Telegram