17/03/2024
CIWON GWIWA DA YADDA AKE MAGANCESHI
DAGA. DR. SALIHANNUR
SHI CIWON GWIWA??
wata gaɓa ce da ta haɗa ƙashin gwiwa da ƙashin ƙwabri a wuri ɗaya, sannan take bada damar motsi a tsakanin ƙasusuwan. Irin wannan ciwon gwiwa wanda ake kira Osteoarthritis yana faruwa ne sak**akon zaizayewar gurunguntsin gaɓa wanda wani matashi ne da ke cikin gaɓar gwiwa tsakanin ƙashin cinya da ƙashin ƙwabri domin bada damar ƙasusuwan gwiwar su riƙa gogayya da juna cikin sauƙi ba tare da tirjiya ba.
GABAR GWIWA???
gaɓa ce da ke ɗawainiyar dakon nauyin jiki tun daga kai har zuwa gwiwa a lokutan tsayuwa ko tafiya da kuma buƙatar motsawarta a mafi yawan lokuta yayin zirga-zirga da kuma ayyukan yau da kullum.
Hakan shi ya sa ciwon ke k**a gwiwowi duka guda biyu duka duk da cewa ciwon gwiwa ɗaya na iya fin na ɗayar, watarana kuma gwiwa ɗaya kawai ciwon zai yiwa illah. Wannan aikin da gwiwa ke yi kulli yaumin, shi yasa tsananin ciwon yana ƙaruwa ne a lokacin da shekarun mutum ke ƙaruwa, haka kuma ciwom yafi damuwar mutane masu nauyi da kuma tsofaffi.
BINCIKE YA NUNA ????
cewa wannan ciwon gwiwa na kan-gaba a jerin larurorin da ke iya nakasa mutum sannan kuma ya tsugunar da mutum ɗungurugum! Saboda haka, tasirin wannan ciwon yana da babbar illah ga ingancin rayuwa, walwala da tattalin arzikin masu fama dashi.
ALAMOMIN CIWON AMOSANIN GWIWA???
wannan ciwon gwiwa suna fama da wasu alamomi da s**a ƙunshi:
1) Ciwo mai ɗabi’ar s**a a cikin gwiwa, musamman da daddare ko da safe kamin a fara tafiya.
2) Kumburin gwiwa.
3) Riƙewar gwiwa.
4. Tirjiya a lokacin tafiya ko motsa gwiwa
5) Idan ma ciwon ya ta'azzara a kan ji sautin gugar ƙasusuwan akan juna — ƙurus-ƙurus yayin lanƙwasa ko miƙar da ƙafa ko kuma yayin tafiya.
SAUYE SAUYEN GABA??
Haka kuma, yau da gobe ciwon gwiwar kan iya haifar da sauye-sauye a kan gaɓar gwiwa tun daga ƙasusuwa, gurunguntsi, har zuwa tantanai da kuma tsokokin da ke aiki a kan gwiwar. Misali, raguwar tazarar da ke tsakanin ƙasusuwan gwiwa (sak**akon zaizayewar gurunguntsin gaɓa), ɗaurewar tsokokin cinya na baya, da kuma raunin tsokokin cinya na gaba, da dai sauransu.
Masu haɗarin kamuwa da ciwon amosanin gwiwa Mutane da s**a fi yawan kamuwa da wannan amosanin gwiwa sun haɗa da:
NA FARKO??
1. Tsofaffi waɗanda shekarunsu s**a miƙa, 45 zuwa sama.
2. Mutane masu ƙiba (taiɓa)
3. Masu haɗarin samun rauni ko buguwa a gwiwa, misali masu wasannin guje-guje da tsalle-tsalle, masu wasan ƙwallon ƙafa.
4) waɗanda sana'o'insu ke buƙatar ɗaukan nauyi tare da daɗewa a tsaye ko ana tafiya, misali, yan dako.
5) Masu wasu nau'o'in tawayar gwiwa
6) Gado: Ana iya gadon wannan ciwon gwiwa, ma'ana idan cikin iyayen mutum wani yana fama da ciwon, akwai yiwuwar wani cikin ƴaƴan sa yayi fama dashi idan lokaci yayi.
Kasancewar wannan ciwo yana farawa ne sannu-sannu, yana da matakan ciwo da naƙasu hawa-hawa k**ar haka
1) Mataki na farko shi ke da mafi ƙarancin ciwo da nakasu.
2) Mataki na biyu shi ke da matsakaicin ciwo da matsakaicin nakasu.
3) Sai mataki na uku shi ne lokacin da zaizayewar ta kai maƙura kuma shi ne yake da mafi tsananin ciwo da mafi tsananin nakasu.
Yadda ake maganin ciwon amosanin gwiwa (Osteoarthritis)
Samun sauƙin wannan ciwon gwiwa yana da alaƙa da ɗaukar mataki da gaggawa tun da wuri domin fara shawo kan ciwon tun kamin ya ta'azzara. Misali, matakin farko na ciwon zai fi sauƙin magani a kan mataki na biyu, na biyu zai fi sauki a kan na uku. Saboda haka, ya wajaba ga mutum ya garzaya a asibiti cikin sauri da zarar an fara jin ciwon gwiwa domin shawo kan ciwon cikin sauki da kuma kaucewa nakasun da yake kawowa.
Sai dai, mafi yawancin masu fama da wannan ciwo na ɗaukar ɗabi'ar nan ta amfani da magungunan rage ciwo barkatai domin rage raɗaɗin ciwon gwiwa. Amma waɗannan magunguna ba sa iya warkar da wannan ciwo, sai dai suna rage raɗaɗin ciwon na wani ɗan lokaci.l ƙayyadadde. Saboda magungunan rage ciwo suna da wani ƙayyadajjen lokaci da suke ɗauka suna aiki a jikin ɗan adam, idan lokacin aikinsu ya ƙare, toh ciwo zai dawo har sai an sake shan wani magani, gashi kuma yawan shan irin magungunan yana da illar haifarwa mutune da cutar ulcer.
To ko mutum zai daina shan maganin rage raɗaɗi? A haƙiƙanin gaskiya babu lokacin daina shan maganin rage ciwo idan ba a je wurin ƙwararrun likitocin da ya k**ata ba.
Likitocin fisiyo (Physiotherapists) ne ke kula da masu irin wannan ciwo. Waɗannan likitoci ƙwararri ne a wannan fanni, suna duba marar lafiya sannan su rage masa ciwon a sauƙaƙe ta hanyar amfani da wasu na'urorin rage ciwo na zamani ba tare da dogaro da magani kullum ba.
Bayan haka, za su bayar da keɓaɓɓun atisaye da motsa jiki na musamman na ciwon gwiwa domin tsokokin da ke kula da motsin gwiwa su sami ƙarfin iya riƙe ƙasusuwan gwiwar yadda ya k**ata ba tare da ƙasusuwan na gugar juna ba.
Sannan suna koyar da wasu dabarun motsa jiki a cikin ayyukan yau da kullum domin kiyaye ire-iren motsin da ka iya sa ciwon ya ta'azzara.
Daga ƙarshe, idan an gwada duk waɗannan hanyoyi amma ba su yi nasarar shawo kan wannan ciwo ba,
DR. SALIHANNUR yatanadar Muku Da Magani Cikin Sauki Tare Da Turo Muku Da Magani Har Inda Kuke
Tell:
0809 235 8776