11/05/2020
COVID-19; AKWAI SIRRIN ACIKIN NAMIJIN GORO (KOLA BITTER).
Yana daga cikin matsalolin da suke dakushe fannin bincike a duniya, rashin alkinta binciken da akayi tare da rashin bitar su, da kuma rashin samar da data-base na binciken da akayi a fannoni da dama, hakan ba qaramin matsala bane ga ci gaban al’umma, domin akwai matsalolin da dayawansu anyi bincike akai amma saboda an jibge kuma ba’a waiwayarsu sai asamu an tafi neman mafitar wata matsala bayan kuma tuntuni anyi bincike kuma an warwareta.
Duk da tsarukan kimiyya da a yanzu masana da masu bincike a fannin magunnguna na itatuwa da ganyeyyaki (wanda akafi sani da maganin gargajiya) suke bi wajen tabbatar da ingancin magungunan, wanda a yanzu za’a iya cewa kusan bai ma kamata a kirashi da maganin gargajiya ba (duk da dole hakan ake kiranshi), har yanzu hukumar lafiya na duniya,Sunqi su ayyana maganin gargajiyar a matsayin maganin da za’a iya shawo kan cutar COVID-19 da shi. Amma kasashe masu dabara tuni s**a zame kansu s**a nemawa kansu mafita s**a koma magungunan gargajiya wanda a yanzu da yawansu sun shawo kan annobar covid-19 wasu kuma suna kan shawowa, misali sune; kasashen Madagascar, China, Korea, Japan da sauransu.
Sakamakon tasirin da magungunan gargajiya s**ayi a wasu kasashe kamar yanda rahotanni s**a fita a kafafen yada labarai na duniya, lokaci yayi da zamu farka mu a gwamnatance ko a daidaikunmu, muyi amfani da tsirrai (itatuwa da ganye) da bincike ya tabbatar da suna da tasiri, ko kuma akwai yiwuwar suyi tasiri wajen kawar da wannan annoba ta covid-19.
Ɗaya daga cikin waɗannan tsirrai da bincike na kimiyya ya tabbatar zasu iya tasiri wajen kawar da cutar COVID19, shine Namijin goro saboda wasu sinadarai da yajr dauke dasu.Najimin tsiro ne mai sirrin gaske, wanda binciken kimiyyar tsirrai masu magani (medicinal plants) ya tabbatar yana dauke da sinadarai da suke kawar da qwayar cutar virus ko wace irice (kamar yadda yayi akan influenza, ebola, AIDs dasauransu), su qarfafi Garkuwar jiki, sannan suyi maganin cutuka da s**a shafi kofofin shigar iska da fitarta (respiratory tract infections; bronchitis, laryngitis etc) da wadanda s**a shafi numfashi (kamar Asthma). Sakamakon wadannan bincike, babu kokonto cewa tabbas namijin goro yana dauke da sinadaran da zasu iya fatattakar qwayar cutar covid-19.
NAMIJIN GORO
A kimiyyance ana kiran goron da Garcinia Kola, kuma a turance ana kiranshi da “Bitter Kola”, Agbilu a yaren Igbo, Orogbo da yarabanci, Namijin goro a yaren Hausa. Namijin goro, goro ne mai sirrin gaske na magungunan cututtuka masu yawa, wanda har takai masu binciken kimiyyar amfaninsa suna kiranshi da “tsiro mai ban mamaki” (Wonderful plant). Anyi bincike kala-kala kuma har yanzu anayi agame da goron, kuma an tabbbatar yana dauke da sinadarai, masu tasiri da qarfin kawar da cututtukan da s**a shafi qwayar cuta ta bacteria da qwayar cuta ta virus, har wasu masu binciken suna kiranshi da mai kawar da duk wata guba daga jiki (General antidotes).
Bincike ya tabbatar da Goron yana dauke da sinadaran Kolaviron da Kolanone wadanda duka nau’ikane daga nau’o’in wani sinadari mai suna flavonoids. Wadannan sinadarai, bincike ya tabbatar da suna kawar da duk wasu cututtika da s**a shafi kofofin da iska ke shiga huhu da numfashi (Bronchitis, laryngitis, ) da matsalolinn maqogoro (throat infections), asthma, ciwon kai, tari, wadanda sune matsalolin da mai dauke da cutar covid-19 yake kamuwa dasu, sai kuma uwa uba bincike ya tabbatar sinadaran suna da tasirin gaske wajen kawar da qwayar cuta ta virus wanda ba’a iyakance adadinsu ba (A duba bincike mai taken “safe african medicinal plants for chemical studies” wanda wani mai bincike mai suna Theophine Chinwuba da team dinsa s**ayi, aka wallafa a mujalla mai taken “Toxicological survey of africa medicinal plants” a shekarar 2014) .
Kusan duk wani qwayar cuta na virus da ya bulla a duniya idan an gwada namijin goro a kanshi ana samu yana da tasirin gaske wajen kawar da wannan virus. Hatta ebola virus da ya bulla an gwada goron akansa kuma aka tabbatar yana da tasirin kawar da virus din. Har saida takai an daina inkarin Aikin goron wajen kawar da qwayar cutar virus a duniyar bincike a yau.
Akwai wani masanin binciken kimiyya (scientist) dan Najeriya mai suna Maurice Iwu, wanda senior research associate ne a therapeutic department of water reed, Army Institute of Research, Washington DC, ya bayyana cewa abinciken da yayi ya tabbatar cewa, namijin goro yana kawar da qwayoyin cutar virus da s**a hadar da; Pinta toro, influenza, venezuelan Equine encephalomyelitis, Ebola virus, da kuma common cold virus.
A shekarar 1995 akwai wani mai binciken kimiyya mai suna Madubinyi, a bincikensa da ya buga a jonal din “Pharmaceutical Biology” ya ciro wani sinadari mai suna “Kolanone (polyisoprenylbenzophonone)daga namijin goro, wanda kai tsaye yake kawar da qwayar cutar virus.
Haka a wani bincike da wani mai binciken kimiyya daga jami’ar Ibadan mai suna Olatunde Farombi a shekarar 2011, daga department of Biochemistry, college of medicine, university of Ibadan, mai taken “Nuts and Seeds in health and diseases” ya bayyana cewa goron yana dauke da sinadarai da suke da tasirin gaske wajen kawar da cututtukan da qwayar cuta ta virus take haddasawa. Binciken farombi ya qarfafi wani bincike da professor Iwu yayi mai taken “Garcinia kola; Anew look at an old adaptogenic agent, antiviral efficacy of Bitter kola”.
Nigeria based Drug Research and Development Firm, sun samar da wani magani mai suna “Darcinia IHP” daga namijin goro, wanda har hukumar lura da abinci da magunguna ta Najeriya (NAFDAC) ta sashi a jerin magungunan da ta yarda dasu, sunyi wani bincike da s**a tabbatar namijin goron yana maganin qwayar cutar virus sannan yana qarfafar matakan tsaro na jikin Dan adam.
A lokacin da aka gudar da 16th International Botanical Conference a Saint Louis, dake USA, masana sun kara tabbatar da tasirin namijin goro wajen magance cututtukan da qwayar cuta ta virus ke haddasawa.
Botanical society of Nigeria dake da hedkwata a Abuja, yayinda Ebola virus ya bayyana, itama ta bayyana cewa, babu wani dan itaciya da yake dauke da sinadaran da zasu iya kashe Ebola virus sai namijin goro. Wanda bayan bincike da Iwu s**ayi da team dinsa sun fitar da cewa tauna namijin goro yana kawar da qwayar cutar Ebola virus saboda sinadarin kolaviron da yake dauke dashi.
A wani binciken kuma da Anna da team dinsa s**ayi, a shekarar 2019 mai taken “Medicinal Potential, Utilization, and Domestication status of Bitter kola in West Africa”, sun tabbatar da cewa sinadarin kolaviron da yake cikin namijin goro, yana daidaita garkuwar jiki(immunomodulatory), sannan yana qarfafar rarraunar garkuwar jiki (weak immune system), sannan yana da tasiri wurin kawar da qwayar cutar AIDs (Acquired Immunodeficiency Syndrome) da qwayar cutar Ebola virus bayan gwaje-gwaje da akayi a laboratory.
Daga wadannan bincike da akayi zamu iya ciro abubuwa kamar haka;
1) Namijin goro yana maganin cutukan da s**a shafi kofofin numfashi da iska ke shiga hunhu (Bronchitis, laryngitis) da matsalolin maqogoro (throat infections), Asthma, ciwon kai da tari (wadanda sune abubuwan da suke jigata mai dauke da covid-19).
2) Namijin goro yana dauke da sinadaran kolaviron da kolanone wadanda bincike daban-daban da akayi a cibiyoyin bincike kala-kala sun tabbatar da suna kawar da qwayar cuta ta virus da aka gwada goron akai.
3) Sinadarin kolaviron da yake cikin namijin goro,
yana da tasirin daidaita garkuwar jiki (immunomodulatory), sannan yana qarfafa garkuwar jiki mai rauni (weak immune system).
Da wadannan abubuwa guda uku da bincike maban-banta s**a tabbatar namijin goro yanayi, zamu iya cewa babu kokonto tabbas zaiyi tasiri wajen kawar da qwayar cutar covid-19.
A dakace mu..
Allah ya bamu lafiya.