Kano Pillars Fans Club Dala Chapter

Kano Pillars Fans Club Dala Chapter Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Kano Pillars Fans Club Dala Chapter, Goron Dutse, Kano.

03/06/2023

Wan nan shine gaskiyar batu, Al'uma sunsan manufar mu tunkafin ma su zaɓe mu, kuma saboda suna so muyi rusau ɗin nema s**a zaɓemu.

04/03/2023

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN

Fitattcen Alaramma malamin tsangaya malam Auwal mai risala wanda yake garin Mubi a Adamawa ya rasu.

Babban malamin addinin musulinci malam Auwal waliyi wanda aka fi sani da malam auwal mai risala ya rasu.

Shehin malamin ya rasu ne da Safiyar yau Talata bayan doguwar rashin lafiya da yayi kuma za a ayi jana'izar sa da misalin karfe 2 na rana a gidansa da ke unguwar sabon layi ƴan kafintoci Mubi ta Arewa, kamar yadda dalibansa s**a shai dawa jaridar Yola 24.

Marigayi malam Auwal wanda khalifa ne ga marigayi Sheikh Ahmed mai risala wanda ya rasu a shekarar 2007.

Marigayi ya rasu ya bar mata biyu da jikoki da ƴaƴa da dama.

Allah yajikansa da rahama Allah yasa ya huta.

Daga: Mu Koma Tsangaya

04/03/2023

Good Morning Freinds And Family!

Happy Week End!!

03/02/2023

Ya Ubangiji a wannan rayuwa da ake ciki ta matsi ka kallemu da rahmar KA, Ka bamu mafita a ko wanne irin Yanayi.
Tabbas babu wani abu mai sauki sai abin da ka sawwake, kuma Kai kadai ne mai iya sauwake damuwa da matsi lokacin da kake so.

Ya Allah Ka bude mana kofofin alkairi su zamo abude duk lokacin muka bukace su daga gareKa, kofofin Albarka, Hankali, Farin ciki, Arziki, da wadatar zuci, Ka tsaremu da tazarci, Cin Amana da Hassada,

Ubangiji ka shiryar damu ka h**e mana shiriya. A zabe mai zuwa ka bamu Shugabanni mafiya alkairi a garemu cikin Jahohinmu da kasa baki daya. Amin.

Barkanmu da Juma’a &

04/01/2023
Innalillahi Wainna Ilaihirraji'un! Kullu Nafsin Zaik'atil Maut!Allah Yayiwa Abokan  Arzik'a Na Rasuwa A Daren Jiya Talat...
04/01/2023

Innalillahi Wainna Ilaihirraji'un! Kullu Nafsin Zaik'atil Maut!

Allah Yayiwa Abokan Arzik'a Na Rasuwa A Daren Jiya Talata Kuma Anyi Jana'izasu Yau Laraba Da Safe,

Allah Ya Jaddada Rahama A Garesu, Allah Kabawa 'Yan Uwa Da Iyalai Jure Wannan Babban Rashi!!
Mukuma Idan Tamu Tazo Kasa Mucika Dakyau Da Imani Amin Ya Hayyu Ya Qayyum!!!

03/01/2023

A cìkìn littafin "Rayúwa Bayan Mútúwa" bugú na biyu, shafi na 78, marigayi Dr Bashir Usman Tofa yana cewa: "Ni kaina na taɓa yin mafarkin na mutú, kuma babu shakka na ga gawata a cikin likkafani ana tafiya da ni izuwa maƙabarta.''

Allahu Akbar! Sai bayan shekaru 25 da bayar da labarin wannan mafarki na sa acikin littafin sa, sannan sai Allah Maɗaukakin Sarki Ya karɓi ransa, a Rana irin ta yau, 3 ga watan Janairu na shekarar da ta gabata ta 2022, wanda a wannan Rana ta yau yake da shekara ɗaya daidai da komawa zuwa ga mahaliccin sa.

Haƙiƙa daga cikin rayuwar wannan bawan Allah, na koyi abubuwa masu tarin yawa, musamman akan abun da ya shafi ƙara mayar da hankali wajen yin takatsantsan, tare da ƙara kiyayewa wajen sabawa Ubangiji na, da kuma tunanin yadda zan kasance bayan na mutu. Wato a duk lokacin da na zauna ina karanta wani littafi na Marigayi Dr Bashir Tofa, na kanji kamar muna tare da shi ne ina yi masa tambayoyi yana bani amsa, saboda tsabar tarin ilimi, da tarin basirar da yake zubawa acikin dukkanin maganganun sa. Tabbas anyi babban rashi a jihar Kano, Arewa, da ma Najeriya baki ɗaya.

Ina addu'a da roƙon Allah Maɗaukakin Sarki da Ya gafartawa Dr Bashir Usman Tofa, Ya karɓi ayyukan sa na alkhairi, Ya sanya rahama a rayuwar sa ta bayan mutuwar sa, Yasa Al-Jannah ce makoma a gare shi, Amin.

DÁGA Adamu Kazaure!
Ɗan Almajiri.

Address

Goron Dutse
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kano Pillars Fans Club Dala Chapter posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share