04/01/2026
innalillahi wa inna ilaihi raji'un ðŸ˜
TABBAS YA KAMATA MU KULA!!!!
Wani lokaci ina ɓangaren bada agajin gaggawa (Emergency) aka shigo da wata yarinya a hannu, sanye da uniform na islamiyya jikin ta, wanda bana ji yarinyar ta wuce shekara sha biyar.
Tun kan a sauke yarinyar kan gado jikina ya bani ba lallai yarinyar na da rai ba.
Ina taƙaice muku labari mukai duk wani dube dube da zamuyi, yarinya dai babu rai, ta rasu.
Da mu ka tambayi me ya faru da yarinyar sai ake cema, sun fito sallah ne wajen ƙarfe huɗu a makarantar islamiyyar su, sai yarinyar ta yanke jiki ta faɗi ƙasa, malamin su da yazo sai yace ai Aljanune, agurin ya fara karanta mata addu'o'i, bayan ya ɗau lokaci yana mata, sai yasa aka ajjiye ta awani aji, yace da aljanun sun cika ta zata farfaɗo.
Dab da za atashi Islamiyya malami ya tura aje a taso ta, wanda anan ne aka ga alamun bata numfashi, kuma aka rugo da ita asibiti.
Ko da ace lokacin da ta faɗi ƙasan aka kawo ta asitibin, tabbas tunda kwanan ta ya ƙare sai ta rasu. Amma dai darasin da nake so mu ɗauka shine "Bakomai ne fa aljanu ba".
Allah ya jiƙan musulmai
Pls ayi sharing don wasu ma su amfana.
Dr Abdurrahman Dambazau