Dr. Dambazau TV

Dr. Dambazau TV My name is Dr. Abdurrahman kamilu Dambazau (MBBS BUK/AKTH). Am a medical doctor, hausa health advocate, content creator, and health influencer.
(1)

GARE KU MASU TARA ƘUMBA/FARCE..Iya tsayin farcen ka, iya yawan ƙwayoyin cututtuka da zasu taru aƙasan farcen....Ga wasu ...
15/10/2025

GARE KU MASU TARA ƘUMBA/FARCE..

Iya tsayin farcen ka, iya yawan ƙwayoyin cututtuka da zasu taru aƙasan farcen....

Ga wasu tambayoyi da har yanzu na kasa samun gamsassun amsoshi akai...

-Me yi fa'ida ko amfani na tara farce yayi tsayi irin haka???
-Shin ya dace da al-ada tare da addini na malam bahaushe???
-Me yasa wanna ɗibi'a tafi yawa acikin mata???
-Idan farcen yayi tsayi sosai kamar dai na wannan hoto, ya masu shi suke wajen tsarkin bayan gida????

Kuzo mu tattauna

Allah ya kyauta
Dr Abdurrahman Dambazau fans

Aikin likitan ci a Nigeria ko wahala??Akwana kin nan sabida yanayi na ayyuka komai nawa sai da ya tsaya, wanda hakan yas...
14/10/2025

Aikin likitan ci a Nigeria ko wahala??

Akwana kin nan sabida yanayi na ayyuka komai nawa sai da ya tsaya, wanda hakan yasa kuka daina ganin rubutu ka na.
Da yawa mutane cewa suke banda lafiya sakamakon na rame kuma na ƙara baƙi.

Banda aikin likitan ci banji akwai aikin da zakai awa talatin da uku(33) agurin aiki.

Ka kwana a tsaye kana aiki, kuma washe gari da safe haka zaka ƙara futo wa, maimakon kaje kai bacci.

Amma Alhamdullillah, ku taya ni murna na samu warwarar wannan matsi na ayyuka kuma insha Allahu zan cigaba da kawo muku rubutu ka, kamar yadda na saba....

Ku rubuta mun matsaltsalu na lafiya da kuke so na muku rubutu akai...

Dr Abdurrahman Dambazau fans

TSARKI YA TABBATA GA ALLAH!!Ɗazu aka kawo mana wannan jariri, da aka haifa da fuska guda biyu...ido huɗu, hanci biyu, ba...
26/09/2025

TSARKI YA TABBATA GA ALLAH!!

Ɗazu aka kawo mana wannan jariri, da aka haifa da fuska guda biyu...ido huɗu, hanci biyu, baki biyu.

Tiyata akai ma mahaifiyar don ciro jaririn, a Asibitin Ali ƙwara dake garin azare.

Fatan Allah ya ba mahaifiyar lafiya tare da jaririn.

SHIN AGANIN KU HAKAN DAI DAI NE????‎Wani asibiti ne s**ayi wani tsari cewa duk Wanda ze zo dubiya (Banda masu jinya) to ...
22/09/2025

SHIN AGANIN KU HAKAN DAI DAI NE????

‎Wani asibiti ne s**ayi wani tsari cewa duk Wanda ze zo dubiya (Banda masu jinya) to zai biya kuɗi.

‎Kuɗin idan aka ansa sai asa a asusun mara lafiyan da s**a zo dubawa, da wannan kuɗin ake amfani wajen kulawa dashi mara lafiyan.

‎Idan anzo sallama in sunyi saura se a ba marar lafiyan abunshi.

‎Hakan ya temaka wajen rage yawan ziyara barkatai, kuma ya sauƙaƙa ma mara sa lafiya kashe kashen kuɗin.

‎Meye ra'ayinku akai? Muhaɗu a comment.

Muhammad Isah

KANA IYA ƊAUKAR CIWON HANTA (HEPATITIS-B) AGURIN ASKI MUSAMMAN IDAN BAKAI RIGAKAFI BA..‎‎Saboda haka ku tabbatar masu as...
22/09/2025

KANA IYA ƊAUKAR CIWON HANTA (HEPATITIS-B) AGURIN ASKI MUSAMMAN IDAN BAKAI RIGAKAFI BA..

‎Saboda haka ku tabbatar masu askin ku suna tsaftace abun da zasu muku askin(clipper) ta hanyar daya dace.

‎Sannan Kuma idan kasan kanada ciwon hanta(HEPATITIS 😎 to kasa Ni zaka iya yaɗa ma mutane Koda bakajin wasu Alamomi.

‎Abin da ya fi dacewa idan kasan kana da wannan ciwo shine kasai abin aski(clipper) naka na kanka, wanda za riƙa ma aski don gudun yaɗa ma mutane.

Pls amana sharing dan wasu su amfana.

‎Allah ya tsaremu da tsare war sa.

Muhammad Isah

Wannan motar fa da kuke gani, mace me ciki aka ɗakko daga wani ƙauye.Wanda sakamakon hanya mara kyau, da kuma tafiya me ...
21/09/2025

Wannan motar fa da kuke gani, mace me ciki aka ɗakko daga wani ƙauye.
Wanda sakamakon hanya mara kyau, da kuma tafiya me nisa da zasu yi kan su zo babban asibiti, ta haihu aciki.
Direban yace mun sanda suna tafiya da jaririn ya futo ya yi kuka, amma kan su ƙara so ya mutu.

Mun zauna muna tattaunawa akan anbawa Rarara dakta, maimakon mu maida hankali akan matsaltsalun da ke damun mu, tare da hanyar da zamu samu mafita.....

Allah ya kyauta mana
Dr Abdurrahman Dambazau

ALLAHU AKBAR!!!Waɗan nan yarane ƴan huɗu(4) da aka ciro ma wata mata yanxu da safen nan a Asibitin mu.Wannan baiwar Alla...
18/09/2025

ALLAHU AKBAR!!!

Waɗan nan yarane ƴan huɗu(4) da aka ciro ma wata mata yanxu da safen nan a Asibitin mu.

Wannan baiwar Allah bata san tana ɗauke da yara huɗu acikin ta ba, ita a tunanin ta ɗa ɗaya ne.
A jiya da daddare da tazo Asibiti, likitocin mu s**a mata hoton ciki, s**a faɗa mata cewa tana ɗauke da yara uku acikin ta.
Amma kuma da safen nan da aka mata tiyata yara huɗu(4) aka ciro daga cikin ta, biyu maza, biyu mata.

Muma ta addu'a.
Allah ya raya mata su.

Dr Abdurrahman Dambazau@top fans

06/09/2025

A likitan ce, ana so mutum ya samu baccin awa 7 zuwa 9. awa nawa kake/kike arana? Nidai ina yin aƙalla 7 idan ban da aikin kwana. 👇

Haɗuwa ta dashi ta ƙarshe lokacin ina gida, yake cemun "Doctor wallahi na cire rai da rayuwa, nasan ma mutuwa zanyi".Dan...
05/09/2025

Haɗuwa ta dashi ta ƙarshe lokacin ina gida, yake cemun "Doctor wallahi na cire rai da rayuwa, nasan ma mutuwa zanyi".

Dan Allah, ya ci albarka cin wannan rana mai tarin albarka.
Mu mai addu'a, Allah ya jaddada rahma agare shi.

Ga masu jinya dake ji aransu cewa mutuwa za suyi...

Kusani rashin lafiya bashi ne ticket na mutuwa ba, ticket na mutuwa shine kwana kin da Allah ya ɗiba ma su ƙare, wannan ne ba makawa, sai ka tafi, ko da lafiya ko babu.

Allah ka jiƙan magabatan mu, in tamu tazo kasa mu cika da imani.

Ameeen.

Dr Abdurrahman Dambazau

SHAWARA GARE MU..Kwana biyun nan asibitocin mu cike suke, sakamakon yawai tan rashin lafiya da ake a wannan lokaci...Jiy...
03/09/2025

SHAWARA GARE MU..

Kwana biyun nan asibitocin mu cike suke, sakamakon yawai tan rashin lafiya da ake a wannan lokaci...
Jiya nayi aikin kwana(CALL), wanda saboda yawan ayyuka, yadda muka ga rana haka muka ga dare.

Abu na farko, a wannan yanayi dole kowa sai yayi haƙuri, tunda ga kan mara lafiya, masu jinya da mu ma'aikatan lafiya.
Gadaje da muke dasu a asibitocin mu na arewa sunyi ƙaɗn su ɗauki adadi na mara sa lafiyan mu, ga matsaltsalu na rashin wadatattun kayan aiki, da kuma ƙaran cin ma'aikata.

Abu na biyu ragowar al'umma dake cikin ƙoshin lafiya, dole suma sai sun bada ta su gudun mawar don samun sauƙin wannan yanayi.
Har kar asibiti a nigeria harka ce ta ƙuɗi, don haka da zarar mun ji wani namu ba lafiya muyi ƙoƙari wajen tallafa masa da kuɗi.

Abu na ƙarshe shine matsala na ƙaran cin bayar da jini da ake fama da shi a asibitocin mu, wanda ko akwana kin nan akwai mara lafiya da muka rasa sakamakon rashin irin nau'i na jinin ta da za a ƙara mata.

Don Allah a taimaka aje a bayar da jini, sakamakon wannan jinin da ka bayar sai kaga ka ceci rai.

Marasa lafiyan mu na gida dana asibiti, Allah ya basu lafiya.

Dr Abdurrahman Dambazau

02/09/2025

Da zarar kin samu juna biyu, ki guji wannan abun da zan faɗa miki...👇

01/09/2025

Daga safe zuwa dare, ana so mutum yasha ruwa mafi ƙaranci, kofi huɗu ko pure water ƙwalli huɗu. Guda nawa kasha ko kika sha? Nidai Nasha 3 daƙyar😂

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dr. Dambazau TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Share on Facebook Share on Twitter Share on LinkedIn
Share on Pinterest Share on Reddit Share via Email
Share on WhatsApp Share on Instagram Share on Telegram

Category