02/01/2026
YADDA ZA KA SAMU KA RUFAWA KANKA ASIRI TA HANYAR RAINON KAZAR MAJA WATA UKU ZUWA WATA HUDU✌️
Za muyi lissafin kaza 300 da abinda za ka samu in Allah ya yarda.
Day Old maja tana kaiwa 800 naira a yanzu, guda 300 zai k**a 240,000
Za ka sai musu robar ruwa tin daga day old kana buqatar guda 20 =22,000
Sai babbar robar ruwa wadda za ka buqata guda 10 itama baza ta wuce 26,000 wadannan abubuwan da za ka siya sunan su fixed investment, nan gaba in ka kwashe ta farko za ka zuba ta biyu baza ka siya ba kuma tinda kana da su.
Maja guda dari uku za taci abin 1,650kg a wata hudu.
Za kayi starter ta sati hudu 300kg
Grower ta sati shida 625kg
Sai finisher ta sati shida 725kg
Magana muke da wanda zai hada abincinsa da kansa, a yanzu naira dubu 14 za ta hada maka ingatacciyar starter, ta razani da fita kunya 23-24% Crude protein.
Naira dubu 11 kuma za tayi maka grower ingattaciyya itama.
Dubu 10 kuma za ta hada maka finisher✌️
Gaba daya 733,000 za ta maka abincin su
Glucose
Multivitamin
Antibiotics da allura ka ware musu 70,000
Gaba daya za ka kashe 803,000+240,000 kudin kaji
1,043,000 kenan kudin kaji, abinci,magani da allurai.
A wata na hudu, kazar majar ka za ta kai 2kg zuwa 2.5kg, ba a cika siyan maja akan kilo ba, an fi siyan ta da rai, ta fi daraja in ma siyan kilo din za ayi,duk kilo din kaza yanzu 4k ne, ka ga 8000 duk guda daya, in Allah ya taimake ka ko da 280 s**a kai za ka samu 2,240,000 a hannun ka.
Har 9k duk za ka iya siyar dasu amma kayi mafi qarancin lissafi, ya fi.
Ka ga ka samu ribar 1,197,000
Akwai qananun abubuwa, irin su gawayi, da sauran abinda ba a rasa ba, nan ma ka cire 97k ka ajiye a gefe.
A dunqule dai ka samarwa da kanka albashin 250,000 zuwa 300k kuma kana yi kana scaling ribar tana qaruwa.
Amma baza ka samu wannan result din ba wallahi sai ka yi abinda ya dace,na bin qa'ida, kiyayewa da kuma addua❤️❤️
❤️📌
Ayi sharing 🙏