Sa'ad bin abi wakas islamic medicine

Sa'ad bin abi wakas islamic medicine its so easy to find us in every were in the world every disease has a cure

29/06/2023

[Ko wace Cuta da maganinta part14]
———————————————————
A Darasin da ya gabata mun tsaya inda muke bayani akan magunguna na ciwon kai wanda inshallahu yanzu zamu dora a inda muka tsaya

To bayan haka k*ma akwai wani ruwa da ake ce masa [ma’uzzahara] shima yana kwantar da ciwon kai mai hauhawa irin wanda zakaga yana farawa kadan sai yaji lokaci guda k*ma ya rikita mutum har ya kwanta, to in Allah ya yarda in akai amfani da wannan yana maganin ciwon kai mai hauhawa,
Akan samu (jan miski) a hadashi da (za’afaran) Wajen shafe goshi da zagaye kai wuya da k*ma kai gaba daya har zuwa makogaro.
in Allah ya yarda shima wannan mujarrab ne, a jarraba za’aga ikon Allah
( Duhnul jauz) Akwai wani mai da ake ce masa duhnul jauz idan aka hadashi da man habbatussaudah ana shafawa sau uku a jiki, ko wace irin mura ce, da mai kashe jikin, Da mai sa zubar da ruwan in Allah ya yarda za’a sha mamaki, tana saurin sauke mura da take bada matsala da ikon Allah.
Sa’anna akwai lokacin da ake samun man madaci idan mura ta zamto mai matsala ce, irin wadda take sa ciwon jiki a rasa yadda za’ayi dashi to babu laifi da farko a samu ruwan safi a sa cokali biyu na zaitun a bashi yasha a sa masa zuma, To bayan ya samu lafiya to sai k*ma a sami shi wannan man madacin a hadashi da man (wardi) a shafe goshinsa gaba daya, to da ikon Allah ko a kwance yake zai samu ya tashi ya cigaba da abinda yake,
Akwai wani bawo da ake ce mishi (Assimak) akan daka shi a w**ke kai yana kara bakin gashi sosai wannan wajen gyaran gashi ne, Assimak in aka daka shi aka kwaba shi, in ana son a kara mashi karfi a kwabshi da man zaitun,
Sa’anna wani lokacin k*ma mura takan haifar wa mutum wata matsala ta daban ta inda zaiji bayajin dadin rayuwarsa gabadaya ta hanyar ciwon kai da ciwon jiki yaji jikinsa k**ar ana sassakawa, To wannan abu biyu akeyi in aka dauki hanya biyu za’a warke da iznin Allah,
Nafarko dai wancan man zaitun din cokali biyu a zuba a ruwan zafi yasha sau. uku a yini cikin gaggawa da ikon Allah zazzabin zai sauka, To sa’annan k*ma shafe jiki da man habbatussaudah da hadata da man zaitun da man kanunfari sannan aka sa masa na’na, to shafe jiki dashi da ikon Allah mutum zai dawo k**ar bai samu matsalar ba,
Wadannan sune kadan daga cikin abubuwan da zamu bayar dangane da matsaloli na mura daga cikin rabe-raben ciwon kai da muka bayar, Dan haka k*ma sai mu tara gaba muga mai zamu kara dubawa dangane da rabe-raben ciwon kai. Wassalamu Alaik*m wa rahmatullahi wa barakatuh.

(c) Sa’ad bin Abin wakas islamic medicine

26/06/2023

[ Ko wace cuta Da maganinta part 13]
_________________________________
Assalamu Alaik*m wa Rahmatullahi wa barakatuhu
Masu bibiyar ta wannan shafi na mu mai albarka shafin ko wace cuta da maganinta Ina muku barka da rana tare da neman afuwarku kwana biyu bamu dan hadu bah To Alhamdulillah k**ar yanda nayi bayani a baya cewa zamu fadi Wasu kadan daga cikin magunguna na ciwukan kai, bayan mun fadi rabe rabensu mun fadi mafi illah mafi muni, na kwakwalwa na fatar kwakwalwa, Na hawan jini da na shafinn shedanu,
To k**ar yadda na fada a can baya dukkan wata cuta da ta kan kawo ta ciwon kai mai sababi to idan aka kauda sababin za’a samu lafiya wanda na buga misali k**ar ciwon ido to idan idon ya warke ciwon kai din zai sauka, k**an duka idan akai bacci sai ciwon kan ya sauka k**an yunwa idan akaci abinci sai ciwon kan ya sauka wannan bama magana akansu sababi ne ya kawo su to a kawar da sababbin da ya kawo su za’a sami lafia da ikon Allah,
Bari mu dauki matsala ta mura, yak**ata mai karatu ya sani cuta ta mura ba karamar cuta bace, cuta ce mai illah, wanda k*ma idan tazo da kaarar kwana ta kan kawo ajali. sai dai abu ne sananne duk sanda akai mura kusan samun lafiya akeyi akan waccce ake da ita domin wata cuta ce take fita a sak**akon ruwan sanyi da aka sha, Ko aka shiga..
Dan haka abinda ya k**ata mu kula da shi idan mutum yana mura yagani miye musabbabin abinda ya kawo masa mura sannn murar k*ma me take saka shi.
Misali akwai wanda hancinsa ne yake yoyo Ana kiranta da danyar mura, Akwai wanda makogaronsa ne yake kaikayi, Akwai wanda tar yake yi, Akwai wanda jikinsa ke mutuwa, Akwao wanda gabbansa ke ciwo, Akwai wanda bacci take saka shi, Akwai wanda ke zubar da majina yaita kakinnta yaji gabadaya kansa ya daure, Duk wadannan kadan ne daga cikin na’u’in mura dan haka, Abinda ya sabbabad dashi yak**ata a gano, wani ruwan sanyi ya sha, wani Ruwan sama ne ya dake shi wani a Tiles ya kwanta, wani mota ya shiga aka kunna masa ac Alhalin bai saba shan Acn bah to sai ta haifar masa da matsala wani irin mai aikata ne na rafi, Gwargwadon yanda muka fadi matsalar a can haka ma cututukan suke da rabe-rabe, Shi mara lafian yasan mai ya haifar masa da matsalar to. abinda ya k**ata mu sani ko ma dai meye daga cikinsu, wannan abin da ka samu kanka na canji na rayuwa abinda kake fitarwa ko yake ciwo lafiya ce karka damu rashin fitarsa shine cutar, Sannan akwai wanda. jininsa yake da karfi sanyin ma baya fita sai dai ya zame masa matsla ya rike masa wata gaba daga cikin gabobi,
Wani lokacin k*ma mutum ne yake fada da matsala sai kaga bayansa yana rikewa shima na’uin sanyi ne, wani lokacin kafa, To k**ar yanda na fada mutum zai duba yaga meye ya haifar masa da matsala dangane da mu’amalantar sanyin
To idan aka samu mai ciwon jiki ce k*ma tana sa yoyon hanci to akwai sanya wadda akw ce mata kusdul hindi
A samu cokali biyar a dafa a ruwa kwanon sha ta sai ayi rurace da ruwan,bayan anyi sirace a tace ayi w**ka da dumin, inshallah idan akai sau uku a kwana daya zata dena wannan zubda wannan kaki ko ciwon ciki da yake saka shi
Hanya ta Biyu, Babu laifi idan akai waccan hanya ba’a dace ba to sai a gwada hanya ta biyu. a sami
Kaki na zuma amma wannan ga wanda bayajin dadin makogaronsa mura ta rike masa bayajin dadi Sai a zuba garin habbatussaudah sai a bashi ya dinga taunawa k**an cingan da ikon Allah yin hakan yana kawo saukin wanna da k*ma rashin jin dadin baki da ya kauda masa,
Akwai. wata saiwa da ake ce mata (Albarnuf) idan aka samet aka shaka yauin da ake mura irin wacce ba’ajin kamshi to da ikon Allah akai hakan a yini sau uku to kafin washe gari za’a samu sauki insha’allah zai dawo maka da jin dadi.
Sannan akwai wata saiwa da ake cemata (bazrul kitan) itama idan aka same ta aka hadata da ruwan zafi, bayan ya dahu ya tafasa to sai ayi sirace to inshallah wannan hayakin idan ya hau kai za’a samu saukin wannan mura
Babu laifi a samu ruwan albasa a matse ruwanta in aka matsi ruwnta sai a hadashi da gishiri dan kadan sai a zuba kahltuffah dan kadan, babu laifi idan kan ne yake yawan hauhawa idan an tabbatar da cewa na mura ne, sai a masa aski ya shafa akan wannan mujarabbi ne da anshafa da ikon Allah za’a samu sauki,
Akwai ( Assandarus) shima wata saiwa ce k*ma ana samun na ruwansa yana maganin mura sosai mai zubar da ruwa indai za’ayi amfani dashi wajen shansa kadan shima sauketa da iznin Allah. Sa’annan babu laifi mai matsala irin wannan ta mura mai sa ciwon jiki da zubar da ruwa to wani lokacin ana son ya samu habbatussauda mai kyau ya hada ta da man kanunfari sai ya zuba a shayi rabin chokali yana sha sau uku in Allah ya yarda zai sauke masa wannan matsala ta mura ta kashe jiki da majina,
Akan samu mura mai kaikayi ta kaogaro akan samu tafarnuwa a kirbata sai a matsi ruwan k**ar chokali uku ko biyu ahada da ruwa k**ar chokali uku sai a tafasa to sai a bashi ya dinga zubawa a makogaronsa yana wasa dashi k**ar yanda yara suke wasa da ruwa haka dinnan yana shiga yana dawoawa in ya dade yana yi sai ya hadiye, in ya juri yi k*ma da ikon Allah zai dena samun kaikayin
Ana samun mura da take dashe makogaron gabadaya aji ba’ajin mutyan mutum To in an samu wannan murar babu laifi a samu lemon tsami guda daya sai a samu tsamiya a hadashi a samusu ruwa rabin kofi a samusu man kanunfari to sai ayi shayi dashi asha, in Allah ya yarda idan akai wannan k**ar sau shida a yini kafin magriba murya zata dawo ana jinta sosai murya zata bude, koma mutum lafiyarsa lau wanda yake son gyaran muryarsa to zai dinga yin hadin to muryarsa zata bude in Allah ya yarda
Wani lokaci ana samun mura irin wadda take sa zubar da majina in kuna magana da mutum yayita yawan kaki ya watsar
babu laifi a samu habbatussaudah ya’yanta a dakasu k**ar rabin kofi sai a sa ruwa kofi biyu a tafasa sai mutum yayi sirace da wannan hayakin bayan ya gama a zuba masa zuma yasha, To in Allah ya yarda wannan majinar zata zama ta kwanta.

(c). SA’AD BIN ABI WAKAS ISLAMIC MEDICINE

12/06/2023

[Ko wace Cuta da maganinta part12]


Au’zubillahi minashaidanirrajiem Bismillahirrahminrrahim
Assalamu alaik*m wa rahmatullahi wa barakatuh.
masu bibiyar Mu a wannann shafi na Ko wace cuta da maganinta wanda yake zuwa muku daga nan
SA’AD BIN ABI WAKAS

TO alhamdulillah bayan mun gama bayani dangane da matsaloli na fatar ka, k**ar yanda nayi Alkawari a baya To a yau k*ma zamu tattauna dangane da matsala ta shi kansa kan Domin kai Shine Injin Dan adam Mota tana dainji wanda in ba inji bazata tafi bah, Haka shima kansa dan adam injinsa shine kai domin ba’a bukatar idan an yanke kai k*ma ace za’a sake jona shi shikenan mutum ya mutu,
[Kai] da kuke ganinsa ya hada gabbai masu yawa domin a jikinsa ake samun baki ake samun hakora, harshe makogaro, Sannan k*ma. daga jikinsa ake samun kunne da hanci da ido to bari mu bisu dallla dallah amma bara mu dauki matsalar [kan], su malamai na musulunci na bangaren likitanci suna cewa shi ciwon kai idan akaso a rabashi za’a iya rabashi arba’in da hudu(44) cikinsu masu muni sune gudu hudun,
akwai na
*kwakwalwa
fatar kwakwalwa
hawan jini
shedani.
To wadancan arba’in din suna bayuwa ne izuwa hanyoyo da dama a cikinsu akwai masu zaman kansu da wanda ba zaman kansu suke bah.
wadanda sule ba zaman kansu suke ba wani abu ne ya bijiro musu yake sabbaba ciwon kan, zan fadi missli daga cikinsu, Akwai wanda yake sshiga rana da, in ka shiga rana sai kaga kanka na ciwo kaga wannan na bijirowa ne? akwai na jin yunwa akwai na dukan kai, da na kuka da ciwon ido yakansa ciwon kai, Sannan wani idan ya kalli waje mai tsaho haka. da ya sauke kai sai kansa ya k**a ciwo wani k*ma idan yayi jim’i to bayan sun gama da iyalinsa sai ya k**a ciwon kai, wani idan ya shiga ma’aikata ya shaki chemical mai karfi sai ya k**a ciwon kai wani baci rai yana sa shi ciwon kai, wani idan ya samu kansa a wani hali na wajen da bai nusti dashi bah sai yaji kansa ya juya to wadannan su ake kira da saababu da k*ma dangoginsu suna da. yawa k*ma ana kiransu da ciwon kai wanda yake bijirowa dan adam to idan muka dauki masu zmaan kansu a cikinsu zamu samu wanda yake k**ar wato yana cikin wani hali na cuta wanda ciwon kan ya sa masa har ya zama ma ya sarke shi, misali akwai mutumin da yake fama. da ciwon aljani, ma’ana cutar aljani, Shashin aljani kenan zakaga diban wa abadan a cikin ciwon kai yake kaga wanna shi nasa daban yake har ya sarke shi, zakaga ko ya sha magani mintuna ne k*ma sai kaga ya dawo To sanna k*ma ana samun wanda zaisha ruwan sanyi wato na mura kenan shima sai kaga ya k**a ciwon kai kaga shima wannan shi ya haifarwa kansa wannan ciwon kan, kai tsaye ba na bijirowa bane na dalili ne, shima sai an kauda wannan abun da ya sabbaba shine (mura) to sai a samu lafiya , To wani lokacin ana samun tari in yayi yawa yana haifar da ciwon kai wanda yakan nasu zuwa ciwon kirji. Amma muna magana akan ciwon kai nei shima ta dalilin wanan tarin sai ya sa masa ciwon kai, Shima wannaan dalili ne ne sai an kauda shi kan zai dena ciwo, To idan muka dauki a wanan kaso da malamai s**ai na ciwon kai zamuga cewa lallai kam ciwon kai yana da kyau ayi bayani da yawa ko ayi bayanin magungunansa da dama dangane da wadannaan matsloli to in muka so muyi haka sai mu kauda wadancan na farkon wato wanda mukace wani dalili ne yake kawo shi k**ar na yunwa, da anci abinci anyi maganin ciwon kan ciwon nai na kuka da anyi bacci an tashi an dena ciwon kan, ciwon kai na bacci in mutum bai bacci ba yakan sa ciwon kai to da an kwanta anyi baccin an tashi, shi bai bukatar magani ciwon kai na chemicak d aaka shaka da an fita da wajen sai a samu lfy, ciwon kai na wato dukan kai bacci yakan lawo lafiya, Duk wadannaan basu bukatar kasha magani haka malamai sula ce to in haka ne sai mu dawo mu dauki wadanda zamu iya magance su ta hanyar abinda ya haifar dasuu k**ar na mura k**ar tarin da ya haifar da ciwon kai, k**ar na kwakwalwa k**ar na fatar kwakwalwa k**ar na hawan jini sanna. k*ma da na wato shedanu to inshallah u zamu dora dangane da wannan na’ui na ciwukan kai da magungunansu akan ko wace matsala ta sanyi ko ta tarin ko ta hawan jinin ko ta shedanun inshaallahu

(c) Sa’ad bin Abi wakas Islamic medicine_______

11/06/2023

[Ko wace cuta Da maganinta part11]


Bismillahirrahmanirrahim
Assalamu alaik*m wa rahmatullahi wa barakatuh,
Masu bibiyarmu a wannan shafi na ko wace cuta da maganinta, Hakane tabbas,
A yau insha’allahu zamuyi bayani dangane da wasu matsalolin Gashi da k*ma magungunansu, Sananen abune ya k**ata kowa ya sani cewa Allah subhanau wa ta’ala yakan halicci bayi ta inda k*ma zai banbanta halittunsu,
Ina nufin cewa Akwai wadanda zakaga Allah ya halicce su gaba dayan gashinsu ja nei, wanda zakaga duk abinda zakai masa zai wahala yayi yayi [baki], Saboda haka halittar tasu take,
To ire iren wadannan malamai suna cewa kar kayiwa mai cuta kuskure ko kai masa yaudara kace zai samu lafiya domin k**ar sanja halittar ubangiji ce irinsu wadanda suke zuwa da kankanin (Gaba) kace gabansu ya kara tsayi wannnan zamuxo bayani akansa dan haka dai. ana kiransa( tagyiru kalkillahi) to ba muna magana akansa bane, muna magana akan wanda ko asali tunda ta taso din, ko tunda , Gshinsa yana zubewa yana kwaikwayewa To yanxu tunda munsan wannan k*ma munyi bayani dangani da abinda yake haifar da wanna, idan Anbi waccan hanyar da muka fada in Allah yaso ya yarda ta matsaloli na fata to babu laifi in Allah yaso ya yarda za’a sami sauki, in Allah yaso ya yarda za’a warware wannan matsala, Amma idan ba wannan matsalar bace gashin yana tafiya haka kawai ya dinga kakkaryewa to s**ace wannan shima za’ayi bincike a gani domin akwai abinda ya samu asalin fatar shine ya haifar da wannan matslar, to yanxu dai mu dauki cewa gashin ne yake fitowa amma baya tsayi to shi hanyoyinsa suna da yawa da gaske da masu sauki da masu k*ma tsada, To da yake mu nan muna bada magani ne ta inda za’a iya hadawa bari mu dinga dibar masu saukin ta inda zai zamto cewa sun fa’idantu da wuri,

INA MACEN DA TAKE DA BUKATA GASHINTA YAYI KYAU,TSAWO DA KUMA LAUSHI?
——————-
in An tabbatar babu waccan matsalar cikin wadancan matsalolin da na fatar ka to babu laifi sai ta nemi
*Zaitu laus (man laus)
* man kwakwa
* man habbatussaudah
* man Albasa
* man tafarnuwa
* man na’ana
* man Alaiyadi, dukda ana cewa laus shine alaiyadi
* man zaitun
To idan ta hada wannan zata samu fa’idoji da yawao koda da akwai wasu matsaloli da suke damun gashin shi man na’na zai kashe shi saboda yana da zafi haka idan ta hadasu ana son ta mayar da shi man kitsonta ko da wani lokaci, In Allah yaso ya yarda za’a sha mamaki gashi sai ana nadews musamman idan aka juri lokaci ana amfani dashi
Hanya ta biyu idan mutum baida kudin da zai hada wancan, sai a sami

*Bawon kwakwa, wannan bawon mai kwarinnan sai a kona shi, in aka kona shi yana ci kar a bari ya zama toka da ya fara ci anga yayi fari sai a kashe wutar a zuba masa ruwa, Sai a daka shi a shanya, in ya bushe sai a daka shi yayi laushi sosai a tankade sai a kwaba shi da man zaitun, in anayin kitso dashi, zai bada mamaki za’a sha mamaki wajen bakin gashi da k*ma laushin Gashi, Wata hanyar bayan wannan hanyoyin Guda biyu,
Idan mace tana da bukatar gashinta yayi kyau yayi laushi , yayi baki ya dinga sheki to babu laifi ta samu
* Man kwakwa
* man bakadunus
* man kuzbaara
* man habbatussaudah
* man zaitun
ta hadasu in ta hadasu da dare ta w**ke kan da sabulun zaitun idan ya bushe sai ta zuba wannan man a cikin gashinta ta mulke gashin kanta dashi to sai ta samu leda ta rife ya kwana, da safe sai ta w**ke da sabulun zaitun ta barshi ya sha iska a rana kar a kitsa shi har sai anyo hakan sau uku to sai a dinga mata kitso da man, wannan mujarrabi ne sosai gashi zaiyi kyau sosai sai an tambayeki ina kika samo wannan gashin.
Bayan haka akwai wata hanya bayan wannan idan gashin kai ya zamanto cewa ba na halitta bane, yayi ja, har ya zamanto cewa da baki nei, To shi wannan babu laifi a samu
* habbatussaudah ita kadai a dinga shafawa alan, To in allah ya yarda zaiyi baki zzai tura kan, k*ma babu laifi a samu man albabunaj a dinga shafa masa shima inshallahu zaiyi baki sosai Bayan wannan idan mace k*ma tsyin gashi take so, tana dashi yana da laushi k*ma yayi baki amma ba tsahi
To ta dinga sanya man simsim wanda. aka hadashi da man hulba, idan aka hada su Guda biyu sai ta dinga shafa su yana bubbugo da gashi, amma shi yanda ale shafa shi ana son a dinga zubu shi ta cikin fatar tukunnan a dinga shafa shi, Sai take da tsahin gashin gashi yayi duhu Amma babu laushi tana bukatar yayi laushi To wannan abu daya ma zata dauka in Allah ya yarda ta samu man simsim man ridi ta dinga amfani dashi inshallahu ba dadewa gashinta zai kyau
Ina macen da take da matsala ta gashinta yana fitowa wani lokacin ma ya gwaguwye ko ya kary, to ba matsalar da muka ambata a baya bace, Domin ya danganta da irin tambayoyin da za’ayi mata shedani da yake zubda wannan gashin ya danganta da yanda za’a mata tambayoyi irinsu bacin rai faduwar gaba mafarkemafake jin haushin makusanta, wannan matsalar idan aka mata tambayoyi aka gano to za’a kori shedanin ne ta hanyar addu’oi da magunguna bayan shedanin ya tafi to in Allah ya yarda gashin zai dawo dan akwai aljanin da yake aske kan mace saboda kar ma a ganta a nemi aurenta da ya sa mata muni, in an samu wannan hanyar abinda aleyi kenan bayan an gama sai a samu man zaitun da man habbatussaudah ayi karatu a cikinsa inshalahu zai zama labari

(c) Sa’ad bin Abi wakas Islamic medicine

09/06/2023

[Ko wace Cuta da maganinta part10]

———————————————————
Bismillahirrahmanirrahiem
masu sauraron mu da karanta, ko bibiyar shafin mu da muke bayanin cutuka da k*ma magungunansu
Assalamu alaik*m wa rahmatullahi wa barakatuh.
Muna nan dai a cigaba da bayani dangane da abinda ya shafi wasu matsaloli da suke haifuwa izuwa fatar ka, wanda ita k*ma fatar ka din itace take bayuwa kai tsaye izuwa fito da gashi mai kyau ko akasin haka.
Bayan munyi magana game da amosani na ka, da illarsa da maganinsa, kadan daga cikin maganinsa mukazo maukai maganaAkan [kora], illarsa da magungunansa da k*ma abinda ke haifar dashi. Kari akan wannan bangare da zamu takaita akansa shine
Akan samu wani lokacin wato cuta ta wata halitta daga cikin halittocin ubangiji k**ar kwari su dinga shiga. kan mutum, wannan ya danganta da inda yake kwana da k*ma rashin tsaftar wurin, Idan nace kwari, k**ar su kudin cizo, kudin cizo kwaro ne, sannan akansamu kaska takan shiga kai, wanda k*ma idan s**a shiga suna haifar da lalacewar fatar ka tunda ciwon wuin suke, suna tsotsar jini a gurin, matsala ce babba, k*ma jini sai sun zuba cuta,
To idan aka samu wannan gaskiya akwai bukatar ayi gaggawa, daga mace har namiji, shik*ma ana gane shi ne, zamu iya shigo da kwarkwata itama zata iya shigowa ciki, to idan an samu wannan wajibi ne a dinga aske kai akai akai, s**ace kada a dinga wuce kwana uku da yawaita dafa ruwan zafi a dinga w**kewa da sabulun zaitun da safe da dadre k*ma a w**ke da ruwan zafi a w**kw da sabulun habba, a dinga yawaita haka tare da binsa da man kuzbarah, To inshallah wannan kwari zasu kau daga wurin, Kuma a dinga tsaftace inda ake kwanciyar ko ake sa ran ana dibar kwarin a gurin
To amma idan ya zamanto kaska ce, Domin tafi divan jini ita tafi illah sosai dan ko a dabba zakaga idan kaska ta shiga jikinta tana wahalar da ita sosai, Ma’ana idan ba kudin cizo bane ba kwarkwata bace, in aka gano Wato kaska ce, Wani zai iya mamaki ya za’ayi kaska ta hau kan mutum har ta cije shi, kai da kake da kulaawa da hankali da tsafta haka zaka gani, Amma akan samu mahaukata wanda suke yawo da kaya karshe abun ya dinga cutar dasu, yayin da akazo za’a musu maganin abun to anan muke magana To babu laifi sai a aske kan shi wannan mara lafiyan, Bayan an aske sai a samo garin habbatussaudah a hada da garin kusdul hindi, da hulba a dafa su gaba daya, to sai a cire kansa a cude shi da sabulun salo ana w**kewa da wannan ruwan haka za’a yimasa Sau uku kullum har kwana bakwai, ana haka, Amma za’a bashi man habba ya dinga shan cokali biyu sau uku, Biyu da safe, biyu da rana, Biyu da dare dan dawo da wannan jini da aka rasa sanna k*ma babu laifi in anyi wannan, in an kwana biyu a samu tumatur a dinga matse masa k**ar rabin kofi sai k*ma. a hada a dinga sa masa gishir kadan da dan suga kadan ana dumamma masa ana bashi yana sha, dan dawo masa wannan jini da ya rasa da k*ma kau da wannan cuta da dafin wannan kaska, Inshallah cutar zata tafi.
Idan k*ma matsala ce ta {kwarkwata}, idan mace ce to ba sai an aske kan ba,babu laifi a daka garin habbatussaudah ya daku, in ya daku to sai a samu a dinga bin cikin gashin ana busawa ko ina yana shiga ciki, in ya shiga sai a rufe kan to in dare yayi sai a samu garin habbatussaudah a dafa shi, a w**ke kan da k*ma garin habbatussaudah in Allah ya yarda in akai haka to duk mai kwarkwata ko mace ko namiji za’ayi wannan hanyar, idan namiji ne za’ayi aski amma idan mace ce ba sai anyi aski bah, Domin abinda yasa mukace a can baya a aske din saboda akwai kudin cizo da k*ma kaska to wannan su dole sai an kauda duk shirgin da suke kan kafin wani sabon gashin, ya ya’ uwa masu karatu ya k**ata ku sani wadannan abubuwan da muke cewa ayi din, Suna temakawa ne wajen a sake samun gashin to sai gashin ya fito mai kyau ba tare da an samu karyewa ayita ganin yana cukurkudewa dan haka da yawa zakaga ana mamakin aske kan mace, k**awa yake, in ya k**a a aske to a aske shi duka dan jiran wani gashin ya fito, k*ma tunda a lokacin ana neman a gyara gashin. ne to dole k*ma sai an gyara inda gashin zai fito, Idan k*ma {kudin cizo} ne ya zamanto yana cizon mutum har k*ma ake sa rai ya shiga cikin kam mutum yana sa mutum soshe soshe, kudin cizo yana da matsala karama ce bata kai ta kwarkwata bah, dan. bashida naci to babu laifi a dinga turara habbatussaudah ana yiwa kan surace ko ba’a aske ba, Amma k**ar yanda na fada inda za’a aske din zaifi saurin warware matslar da ke ciki, Domin akai masa wannaan suracen na garin habbatussaudah to zai mutu sai dai k*ma ya za’ayi a fitar dashi, kunga kenan mafi kyau a aske shi, to in anaskeshi in Allah ya yarda zai zama labari, ina ganin yan uwa anan zamu dakata da bayani angane da abinda ya shafi matsala ta fatar kai, wacce itace asalin uwa da take bada gashi mai kyau ko yayi baki ko yayi laushi ko yayi tsayi, to idan dai aka bi wannan hanyoyin to in Allah yaso ya yarda ko wace irin matsala ce zata kau, Sai dai abinda zamu kara cewa, wanda k*ma yake baida wannan matslar, k*ma yana so ya gyara shi ko yayi rigakafi To in Allah yaso ya yarda yawan shan habbatussaudah da man zaitun da k*ma shafe kan tare dashi yana gyara wannan duk matslolin, k*ma yana hana shigar wannan matsalolin da muka ambata a baya, k**ar yanda muka ambata a baya, Ana kiransa rigakafi babu laifi a dinga yiwa yara in s**a taso zakaga sun taso babu wannan matsalar inshallahu, dan haka sai a tara gaba a bayanin da zamuyi, bayani k*ma wajen mas’alar gashin kaa da k*ma matsalolinsa da karyewarsa da k*ma abinda yake sa masa laushi inshallahu wallahi ta’alah A’alam

(c)Sa’ad Bin Abi Wakas Islamic Medicine

03/06/2023

[Ko wace Cuta Da maganinta part9]
__________________________________________
Cuta ta Uku itace cuta ta sanko
kOk*ma rashin fitowar Gashi a kaa Akan rasa daga keya, k*m akan rasa daga tsakiya k*ma akan rasa daga farko, ya danganta da inda Allah ya jarabci ko wani bawa, To babu laifi ita ba cuta ce da za’a tayar da hankali bah, Amma idan mutum yana bukatar ya dawo da wannan, din daga maza har mata, Sai dai su galibi mata nasu bai fiya nunawa bah ta yanda yake nuna na maza,
To babu laifi a samu albasa, Albasa wadda ake ci wannan a dinga gogawa a inda babu gashin safe da ana da daddare a samu k**ar minti Goma ana gogawar, ana dannawa da karfi ana gogawa,
Hanya ta biyu s**ace lemon zaki wannan bawon nasa mai yajin nanna, A dinga sawa a wajen bayan an mulka an mulka ana shafa man albasa a wajen, Albasa tana da ruwa tana da mai to ba ruwan ba, man albasar to shima in Allah yayarda yana fito da gashi da gaggawa, Sa’annan s**ace wanda yake ganin wannan din zai bashi matsla to ya yawaita cin albasa ma’ana wadda aka dafata bata dahu ba luguf tayi garas garas, to in Allah ya yarda wannan abun yana hauhawa izuwa fito masa da gashi.a inda bashi da gashi wannan k*ma ga mata da maza duk gabadaya akan samu matsalar k*ma duk wannan hanyoyin suna magance su, A nan zamu tsaya
Wassalamu alaik*m wa rahmatullahi wa barakatuh
(c)Sa’ad bin Abi Wakas Islamic chemist

03/06/2023

[Ko wace Cuta da maganinta part8]
_____________________________________
Bismillahirrahmanirrahim
Masu sauraron mu da karaanta bayanan mu muna muku fatan Alkairi.
To A yau inshaallahu zamu dora dangane da matsalolin da fatar ka take fama dashi wanda k*ma ya k**ata mai karantawa ya sani baazamu samu lokacin da zamuyi gaba daya ba, Wasu a cikin tambayoyi bayanin zai fito a lokacin zamu fade su, Amma zamu fadi masu muhimmaanci da k*ma wadanda suke addbar mutane

Matsala ta biyu shine wato akwai cutar kora, Cuta ce mai zaman kanta da ake ce mata Kora, wanda galibi yan zamani wasu basu sannta ba, Amma duk dan shekara ashirin, da biyar, talatin baya yasan me ake nufi da kora.
Wata cuta ce da take fitowa a fatar kaa, a sak**akon karancin ruwan da yake gudana a fatar ka, in aka sami karancinsa to si ta haifar da matsalar da har bushewar wajen zai naso izuwa waje ta inda za’a dinga samun wani farin Gari yana fita a kan mutum, Kuma yana cinye gashi yana cinye fata, yakan sa k*ma kaikayi mai tsanani wani lokacin k*ma yakan zuba k**ar dusa haka, to Alhamdulillahi da yake ita cuta ce mai zaman kanta, sak**akon k*ma yanda. shugabanni s**a tsaya tsayin Daka Alhamdulillah a yaunzu kusan a kauda wannan cuta, Amma dai takan faru wani lokaci izuwa lokaci,
To idan an samu irin wannan matsala ta karancin ruwan da yake fatar kaa har ta haifar da wannan cuta ta kora to ita babu babanci tskanin mata da maza Dole sai an aske gashin kan gabadaya sannan k*ma akwai bukatar lallai a dau lokaci ana kula da wannan fatar, kusan kace Gona ce ta lalace akai shekara da shekaru baa nomata, Sak**akon haka za’a samu abubuwa da yawa sun fito a cikinta wanda duk sanda akace za’a dawo da ita asalinta sai ansha wahala, shima wannan cuta ta kora itama kusan k**ar haka nei, Don haka ba’a maga gaggawa.
Dan A kallah suna bada magunguna da ake amfani dashi,Wani lokacin mako shida, bakwai har sha biyu, ana gane haka ne ta inda korar taci galabar kai, Amma idan yar kadan ce ta fito akan dauki mataki da wuri ba’a kaiwa wannan lokacin ana mata magani, To idan An samu wannan matsala

Babu laifi sai a aske gashin kan gaba daya sai a samu albabunaj, shidai albabunaj wani tsiro ne cikin tsirrai nah magunguna na muslinci sai a dakashi a hadashi da hindiba’u, hidiba’u wata saiwa ce tana da yaya’to ya’yan za’a dauka a daka su, sai a hada da albabunaj, a kwaba su sai a dinga sawa a kan gaba daya in aka sa akan sai a dinga shiga rana anayin k**ar 10mins, rana ta dake shi. to daga nan k*ma sai a. bar kan haka ko mace ko nakiji haka ake so bayan an samu k**ar awa shida sai a w**ka a kara hadawa a sake shiga rana inda ragowar ranar kusan za’ayi so uku kafin magriba, k**ar yanda na fada za’a dauki Dogon lokaci anayi, Gwargwadon yanda aka ga ana samun cigaba da fitowar gashin gwargwadon yanda za’a dena,
Hanya ta biyu, Sukace idan akwa gwada wacca ba’a samu lafiya bah babu laifi a gwada hanya ta biyu,
a aske kan Sai a samu ruwan zaitun sai a w**ke kan dashii, Sai a sami mai na bakadunas sai a shafa, shima ana so a dinga shiga ranar Amma za’a dinga shan ruwan zaitun din chokali uku a kullum insha’Allahu za’a dau dogon lokaci anayi yayin da akaga cutar ta kau to sai a dena

Hanya ta uku, in aka gwada waccan hanyoyi ba’a samu lfy bah to sai a aske kan sai a nemi cittta danya. a hada da albasa sai a kirba a dinga shafe kan, safe da rana sannan k*ma a dinga shan man habbatussaudah original a dinga shan cokali daya da safe da rana da dare, shima yana maganin wannan cuta ta korah

Hanya ta hudu, Sukace babu laifi idan akai wadannann Allah bai kaddara an samu lafia ba to sai a aske kan, sai a nemi kusbara da kishruman kowanne chokali biyu garinsu, sannan sai a sami tazargade sai a daka a samu cokali biyu to sai a kwaba su gaba daya da man tafarnuwa insha’allahu zai kau da wannan cuta, shima k*ma ana son a dinga shan wannan ruwan zaitun din cokali biyu-biyu safe da rana, tuwan zaitunannaan yana da fa’idah sosai in Allah ya yarda zamu cigaba da fadansa domin ba kowa ya sanshi bah domin ami ruwansa da ake kawo shi fari kallllll a kwalna, ba k*ma ya’yansa bah Wannan hanyar babu babanci maza da mata, yara da manya insha’allahu zaka kauda wannan matsalah
(c) Sa’ad Bin Abi Wakas Islamic Medicine

30/05/2023

[ Ko wace Cuta da maganinta part 7]

————————————————————-

Au’zubillahi minashaidanirrajiem Bismlahirahmanirrahim.
Masu bibiyar mu da sauraren mu ina muku fatan Alkairi.
Assalamu alaik*m wa rahmatullahi wa barakatuh.
A cikin bashin da kuke bin Abinda ya k**ata ayi muku bayani shine akwai wato bayani dangane da matsalata ta fatar kaa wacce k*ma muka dauko matsala ta farko daga cikinta wadda k*ma itace Cutar amosanin ka, kadan daga ciki mun bayyana wasu matsaloli da suke sa A sami amosani na maza wanda k*ma yau muka ce zamu tattauna k*ma a bangaren matsalar ta mata.

To a ka’ida yak**ata mai karantawa ya sani su mata galibi duk wasu matsalolinmu Guda biyar to su za’a same su da guda takwas saboda haka idan an samu matsala a wajen mu irin wannan to zaka samu nasu yana fifituwa ko yana karuwa sama da namu ba dan komai ba saboda wasu abubuwa da suke dauke dashi da shara’a ta kallafa musu wajen boy jikinsu misali cutuka da yawa da mukeyinsu mu warke da wuri su basa barinsu sai sun rfe wajen. kamr abinda ya shafi matse matsi kasan nono, Abinda ya shafi hammata abinda ya shafi cibiya da dai sssuransu, k*ma ba’a maganar k*ma wanda suke wajen gabanta akwai cutuka kusan sama da guda bakwai da suke cikin gaban mace, dukkaninsu k*ma suna bukata kulawa in ba haka ba su haifar mata da matsala…
Sannan k*ma baya da haka in tana shayarwa tana samun matsa ta mahaifa, k*ma wajen shayarwar ma ana samun matsalar daukewar Nono, Wanda duk wannan mu maza bamuda su, To shima wajen wannaan matsalar tasu tana hauhawa sama da tamu
Wato ita mace galibi idan aka same ta da wannan matsala ta zubar wannan dusa ta amosani a ka, to za’a samet k*ma da matsala ta lalacewar gashi da gaggawa ba dan komi ba saboda w**ke kan da zatai k*ma ta rufe, baya shan iska dan haka sai aka bada hanyoyi sama da guda Goma sha wani abu dangane da warwarewar wannan matsala tasu Amma zamu ambaci kadan daga ciki,
Idan mace ta samu kanta a wannnan hali na amosani na ka, wanda shima ya kan doru izuwa haifar da matsala ta ido, ido yayi jaaa ko yayi kaikayi to daya ne. daidai yake da namu a wannan lokacin ba’a. son ya zamnto tana wannan halin domin nasu yana musu kaikayi wanda k*ma yakan bayu wani lokacin a kaddara ko zuwa kwarkwata ce akansu to shima ruwan kal ake samu, Ruwan kal su nasu ana son a kallaah kalar cokali biyar a cikin ruwa kofi daya sai a dafa sai a w**ke an da sabulun zaitun da daddare, a barshi a bude ya kwana da safe. za’a hada mayuka k**ar Guda biyar
Man zaitun
man tafarnuwa
man na’na
man jirjir
man kwakwa
a hadasu gaba daya sai ayi kokari a bude gashin kan bayan ya sha iska sai aga a tabbatar an zuba a cikin gashin daga kasansa tunda a lokacin muna bukatar mu gyara fatar nei, dan a. tabbatar ya hau ckin fatar sai a sa hannu a cucuda to haka. zata rufe kan k*ma ta yini dashi zata dinga yin haka har kimanin kwana Goma sha daya daga nan sai a kitse kan a cigaba da sa wannan mayuka guda biyar a tsakankanin wannan kitso da aai mata, inshallahu dauukan wannan mataki na farko na warkar da wannan matsala k*ma k**ar na yarda na fada a wannan matsala na maza, indai an warware wannnan matsala ta amosannin da yake zuba to in Allah ya yarda shima za’a samu na idon wannan jaaa da yakeyi da kaikai in Allah ya yarda zaii dena

Akwai Hanya ta biyu in An gwada waccan in Allah ya kaddara ba’a dace bah babu laifi sai a sami wato tsamiya a dafa ta in aka dafata sai a sami ya’yan zaitun akwai ya’yan zaitun da ake ci suna nan a cikin kwalba to ya’yan in akaci akwai kwallonsu, shi kwallon nasu sai a daka sh sai a hadashi a cikin wannan ruwan tsamiyar a samu yayi k**ar kwana daya a tsume to shi wannnan ruwan w**ke kai dashi, Insha’allahu kai tsaye indai aka juri yi cikin sati biyu da ikon Allah zai kau da amosani’.
Duka idan anyi wadannan hanyoyi Allah bai kaddara samun lafiya bah babu laifi ja’izi ne halacvi nei mutum ya nemi magani sai a tsefe kan, kar a barshi da kitso a warware shi a w**k kan da ruwan zafi, aka w**k shi da ruwan zafi sai a nemo man karas a hadashi da man jirjir da man kanunfari idan aka hadasu s**a hadu gaba daya shi wannan man abinda akeyi dashi kitso ne, idan ana kitso dashi inshallah duk bayan kwana biyu aka dauki sati biyu ana yi, da ikon Allah za’a warke,
Idan akai waccan hanya ta uku Allaah bai kawo sauki ba to akwI hanya ta hudu da akeyi shine sai a w**ke kan da sabulun zaitun sai a barshi ya bushe, bayan ya bushe sai a samu man habba mai karfi, in so samu ne a samu miracle Almu’ujiza sai a kwarara a ciki yayi yawo a cikin fatar wann ana son kwana bakwai, ayita yi, in ALLAH YA yarda iya ita kadai wannan habbar takai karfin hakan in Allah ya yarda zata kauda wannan matsalar.
Hanya ta biyar idan akai wadannan duka Allah baisa an samu lafiya bah malamai s**ace babu lalifi wanna mace ta zammto tana kitso akaiakai amma duk sanda akazo yin kitson kafin ayi a tabbatar an jika kan gabadaya da man tafarnuwa, To ana cikin yi k*ma ana barbada garin tafarnuwa akai ana barbawa haka to da angama sai a rufe kan, To a ranar ana son ya yini a rufe, to da safe sai a warware kan, a w**ke shi da ruwan zafi da sabulun zaitun inshallah bin wannan hanyar shima da gaggawa ana samun suki
Hanya ta shida da malamai s**ac babu laifi ida mace ta samu matsla akan wannan matsala ta amosani sai a tsefe kanta, idan aka tsefe kanta sai a hada mayuka biyu kachal,
Man habba
man tafarnuwa
garin tafaruwa chokali daya garin habba chokali ddaya, sai a dinga mata kitso da iya wanna cikin sati zuwa kwana goma sha biyu in Allah ya yarda za’a samu lafiya ubangiji Allah yasa mu dace, Wannan kadan daga cikin matsala ta amosani na ka kenann, yanxu k*ma cigaba zamu dora da wata matsala matsala ta biyu dangane da abinda yake haifar da matsala a fata ta ka, wanda yake haifar da gashi karyewa ko dashin fitowa ko k*ma canja masa launi yayi jaa ko yayi wata kala daban, inshallah wassalamu Alaik*m wa rahmatullahi wa barakatuh……

(c) Sa’ad Bin Abi Wakas Islamic Medicine

Address

Kano Nigeris
Kano

Telephone

+2348039275780

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sa'ad bin abi wakas islamic medicine posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Share on Facebook Share on Twitter Share on LinkedIn
Share on Pinterest Share on Reddit Share via Email
Share on WhatsApp Share on Instagram Share on Telegram