Health Awareness TV

Health Awareness TV Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Health Awareness TV, Medical and health, Kano.

01/12/2024

Kokasan Zaka Iya Aurar me HIV Koda Kaibaka Da Ita Kuma Kuyi Rayuwa Batareda Kakamu Ba Kaima🤔🤔
World HIV Day 1st December

01/12/2024

1 December
World HIV Day
Millions mutane
suna dauke da Cutar HIV Amman Basu sani ba!!

SHA KA FASHE (DEXAMETHASONE)Dexamethasone magani ne wanda aka fi sani da suna SHA KA FASHE. Ya kasance magani wanda ake ...
25/11/2024

SHA KA FASHE (DEXAMETHASONE)
Dexamethasone magani ne wanda aka fi sani da suna SHA KA FASHE. Ya kasance magani wanda ake magance matsalolin rashin lafiya daban daban. Amma fa yawan amfani da shi ba a bisa ka'ida ba na iya janyo ma lafiyar mutum matsaloli masu yawa.

Eh, Tabbas yana sa KIBA (ta hanyar sanya kitse a tumbi, fuska da bayan wuya), hakan yasa wasu mutane suna amfani da shi Wajen neman yin jiki (kiba). Abin lura shi ne cewa wannan maganin fa asalin shi ba don kiba aka yi shi ba, side effect (illa) na yawan amfani da shi ne ke kawo kibar. Yin amfani da shi ba a bisa ka'ida ba na tattara ma jikin mutum matsaloli masu yawa.

Yawan amfani da sha ka fashe (Dexamethasone) na iya kawo abubuwa kamar haka:
1. Ciwon suga (Diabetes)
2. Hawan jini (Hypertension)
3. Kafafun mutum zasu suntuma (ba kiba bace, taruwan ruwa ne a cikin jiki, wanda ba a son hakan).
4. Kamuwa da cutar osteoporosis (kasusuwan cikin jikin mutum zasu zama sirara) wanda hakan na iya kawo ciwon gaɓɓai, da saurin karaya da an ɗan faɗi ko buge.
5. Idanuwan mutum zasu dafe, zai rage gani a hankali a hankali (cutar Cataract).

Dan Allah a kiyaye da amfani da wannan maganin har sai in likita ne ya rubuta cewa ayi amfani da shi. Ba shi kaÉ—ai ba har da yan'uwan shi irin su PREDNISOLONE.

A nemi karin bayani akan magunguna a koyaushe daga kwararru masanan magunguna.

ABUBUWAN DA YAKAMATA KI SANI DA ZARAR KIN HAIHU1. Ki fara shayar da jaririn ki da zarar kin haifeshi,kifara shayarda shi...
24/11/2024

ABUBUWAN DA YAKAMATA KI SANI DA ZARAR KIN HAIHU

1. Ki fara shayar da jaririn ki da zarar kin haifeshi,kifara shayarda shi cikin awa dayan farko na rayuwarsa.

2. Ruwan nono shine abinci mafi kyau ga jariri wanda yake zuwa tatacce tare da dauke da duk wani abu da jariri ke bukata.

3. Ki shayar da jaririn ki safe da dare duk lokacin da ya bukata,Hakan zai taimaka miki wajen karuwar ruwan nono sannan ya kareki daga ciwo da kumburin nono

4. Shayar da jaririn ki cikin yan mintina kadan bayan haihuwa zai taimaka miki mabiyarki(placenta) ta fito da wuri sannan yarage miki zubar jini bayan haihuwa

5. Madarar dake fara fitowa bayan kinhaihu ba dattin nono bane,ki tabbata jaririnki yasha,wannan madarar itace rigakafi mafi muhimmanci da yaranki zai samu wanda zata fara bashi kariya daga ciwuka

Hemorrhoid/Pile Basir ke nan da hausa kumburi ne da ake samu a jijiyoyin sashen qarshe na hanji (Re**um) ko kuma hanyar ...
11/11/2024

Hemorrhoid/Pile Basir ke nan da hausa kumburi ne da ake samu a jijiyoyin sashen qarshe na hanji (Re**um) ko kuma hanyar fitar bayan gida (A**s).

ME YAKE KAWO BASIR

-Dadewa a tsigune ko zaune a bandaki lokacin bahaya

-Qarancin sinadarin Fibre a abinchi

-Juna biyu ga mata masu ciki

-Nauyin jiki ko qiba

-Amfani da magungunan da kan haifar da Zawayi (Laxatives)

-Taruwar bayan gida a ciki (Constipation)

-Bambamcin yanayin halittar qarshen hanji(Re**um)ko hanyar wucewar bayan gida (A**s) dana sauran mutane.

-Nishi wurin qoqarin yin bayan gida (Straining).

-Mu'amalar aure ta hanyar fitar bayan gida.

-Da sauran su.

ALAMOMIN BASIR

-Kumburin hanyar fitar bayan gida

-Qaiqayi

-Jin zafi lokacin bahaya

-Zazzagowa ko fitar wani sashi ko naman hanyar wucewar bayan gida

-Fitar jini lokacin bahaya

-Da sauran su

HANYOYIN MAGANCE BASIR IDAN ANA FAMA DASHI

-Tsaftace wurin akai-akai ta hanyar tsarki da ruwan dumi. Idan da sarari za'a iya amfani da ruwan dakan taimaka wurin kashe qwayoyin cututtuka da akan iya sawa a jiki wato Antiseptic solution.

-A ringa yawaita amfani da kayan abinchin da suke dauke da sinadarin fiber,ganyayyaki da kayan marmari domin su taimaka wurin hana taruwar bayan gida a hanji, kuma a ringa samun sauqin fitar sa lokacin bahaya.

-Za'a iya zama a cikin bawo mai ruwan dumin da jiki bazai qone ba domin samun sauqin jin zafin wurin.

-A guji amfani da hannu ace za'a tura Idan ya fito.

-Da zarar anji bahaya a daina jinkiri ayi maza ayi domin qin yinsa a lokacin da ya kamata yana qara masa tauri.

-A daina amfani da magungunan da kan saka Zawayi(Laxatives) ga masu son rage qiba indai ba rubuta musu akayi a asibiti ba.

-A ringa yawaita motsa jiki da atisaye dai-dai gwargwado domin lafiyar hanji da sauran gabobin jiki.

-Idan bayan gida bai zo ba, a daina qoqarin nishi wurin ganin cewa dole sai an fiti dashi.

-Akwai magungunan rage zafi da akan iya samu a kowanne shagon sai da magunguna (Analgesic) na Sha ko na shafawa, za'a iya amfani da shi wurin rage ciwon da ake ji saboda basir din.

-Idan ba'a samu afuwa ba,ko kuma ya fara fitowa, ayi gaggawar zuwa asibiti domin ganin jami'an lafiyan da s**a qware a wurin domin samun kulawar data kamata a lokacin da ya dace, domin Idan yayi tsanani sai anyi aiki a wurin kafin magance shi.

Allah ya bawa masu fama da larurar lafiya. Ameen!

Amb(Nr)Sumayya Ibrahim Sa'ad
RN,RM,PND


11/11/2024
24/10/2024

Kokasan Zaka Iya Aurar me HIV Koda Kaibaka Da Ita Kuma Kuyi Rayuwa Batareda Kakamu Ba Kaima

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Health Awareness TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share