
04/12/2024
๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐
Yau wani uzuri ya kaini sashen ido na ABUTH Shika. Anan ne naga wani dattijo wanda yake gab da rasa ganinshi na ido daya. Dalili kuwa shine ciyawa ta shiga idon nasa tun wata daya da ya wuce, yayin da yake aiki a gona. Yace ya je ya ga likita(wataฦila ba na ido ba) ya bashi magani amma dai ciwon babu sauฦi. Hakan tasa dole ya garzayo nan don ganin ya samu lafiya.
Watakila da ya samu ganin ฦwararren likitan ido tun da fari, da tuni an ceto idon nashi. Yanzu kam likitan ta tabbatar da cewa idon nashi yayi nisa. An dai bashi magunguna da ake fatan, in da rabo, zasu iya ceto abun da ya rage.
Don haka idan kaji ciwo (musamman na ido), to ka garzaya asibiti don ganin ฦwararren likitan ษangaren. A kowane babban asibiti akwai sashen ganin likitocin ido, wanda sune kaษai ke da alhakin duba idanu tare da bada magani, ko yin aiki. ฦangaren ido na ษaya daga cikin ษangarorin da kai tsaye ake zuwa don ganin ฦwararren likita, ba tare da biye-biye ba. Don haka yawanci ake kiransu da "Eye Clinics".
Allah ya ฦara tsare mana lafiyar idanun mu da ta sauran jikinmu gaba daya.
Adam Kabir Tukur
03/12/2024.