10/07/2025
*KUMBURIN MAHAIFA MAI SANYA ZUBAR JINI (ENDOMETRITIS)*
Endometritis kumburin bangon mahaifa ne (endometrium) wanda yake haddasa zubar jini daga gaban mace. Zai iya kasancewa mai tsanani amma baya daukar dogon lokaci (acute). Hakanan zai iya zamowa mai tsanani kuma mai daukar dogon lokaci (chronic). Mafi yawanci kwayoyin cutar bacteria ne suke kawo shi, musamman wadanda suke k**a al'aurar mace bayan ta haihu, ko kuma a lokacin da ake yi mata aikin tiyata a mahaifa ko mara.
Bincike ya tabbatar da cewa manyan dalilai masu kawo endometritis sune:
1. Haihuwa (childbirth): idan kwayoyin cutar bacteria s**a shiga cikin mahaifa a lokacin da mace take yin nakudar haihuwa, to, zasu iya haddasa mata matsalar endometritis, musamman idan tayi diguwar nakuda (prolonged labour), ko yagewar jakar ruwan mahaifa (amniotic sac rapture), ko yawan duba mata budewar farjinta (multiple vaginal examination - VE).
2. Aikin tiyatar cire jariri (caesarian section - CS): macen da akayiwa tiyatar CS sunfi kowa hatsarin kamuwa da endometritis, duk da kasancewar kayan aikin da kuma dakin tiyatar masu matukar tsabta ne. Hakan yana da nasaba da tsanin yawa, naci, da kankantar bacteria din ne.
3. Ayyukan tiyatar da s**a shafi farji da marar mace (gynaecological procedures): wadannan sun kunshi wankin ciki (dilation and evacuation), aikin duba mahaifa (hysteroscopy), daukar wani abu daga cikin mahaifa domin yin awon wata cuta (endometrial biopsy). Kwayoyin cutar bacteria zasu iya shigar mahaifa a lokacin wadannan ayyukan.
4. Cututtukan da ake dauka a wajen jima'i (s*xually transmitted diseases - STDs): wadannan sun kunshi chlamydia, gonorrhea, staphylococcus, da sauransu. Duk suna iya haifar da endometritis idan s**a shiga mahaifa.
*ALAMUNSA (SYMPTOMS*)
Alamun endometritis sune:
1. Zubar ruwan da mace bata saba gani ba daga gabanta (abnormal vaginal discharge): ruwan zai iya kasancewa mai wari ko karni, sa'annan mai launin ruwan kwai (yellowish) ko ruwan ganye (greenish).