09/09/2023
WAI SHIN KUNSAN KUNSAN GLAUCOMA CIWON IDO MAISA MAKANTA .
DA YADDA ZAMU MAGANCE MATSALOLIN CIWON DA IZININ ALLAH.
DAGA NAKU ( Dr.Khaleel👁️ ) .
Yawancin glaucoma yakan faru ne idan wani ruwa ya ginu a bangaren gaba ido. Wannan karin ruwa yana kara matsin lamba a ido, yana lalata jijiyar gani.
Glaucoma dai ita ce kan gaba wajen haddasa makanta ga mutanen da s**a haura shekara 60. Amma sau da yawa ana iya hana wannan makanta daga kamuwa da cutar glaucoma da wuri.
Wasu mutane na iya samun jijiyoyin na gani wadanda ke da matukar damuwa da matsanan cin ciwon ido na al'ada. Wannan na nufin hadarin da suke da shi na samun glaucoma ya yayi karfi sosai . Gwajin ido na yau da kullum na da muhimmanci don gano alamomin farko na lalacewar jijiyoyin gani.
GA ALAMUN WANI MUMMUNAN HARI NA CIWON GLAUCOMA:
* Mutum yadinga yawan ciwon ido mai tsanani.
* Kokuma mutum yadinga yawan ciwon Kai.
* Ko mutum yadinga Gani disu disu.
* Ko Rashin son Ganin haske .
* Ko Rashin Ganin abinda ke nesa.
To wayan'nan suna daga cikin alamun ciwon glaucoma,Kuma yakamata damunga wayan'nan alamu mu Maida hankali Dan Ganin likita.
Kuma akansamu wannan ciwon ta wani fanni ne daga brain wato Kwakwalwa , akwai wasu jijiyoyin Ido dasuke makale ajikin Kwakwalwa suna samo wani sinadarin Gani ne ta yadda mutum zega wani abu ko kuma ya iya Fitar da hawaye, ko samun bacci ,
To kusani cewa idan wayan'nan jijiyoyin s**a samu matsala mutum baze taba samun bacci ko kyakkyawan Gani ba , Kuma s**an samu bushewa ne ta rashin zagayawar wasu ruwaye wayan'da suke temakawa ido ,
Yakamata kayi magana da likitanka idan kasan kanada wayan'nan matsalolin domin saukakawa lafiyar idonka don inganta lafiyar ganika .
GA ABUWAN DA MAI GLAUCOMA YAKAMATA YADINGA ANFANI DASHI .
( 1 ) yawan cin kan kifi . 🐟
( 2 ) yin anfani da man carrot 🥕
( 3 ) Shan man carrot murfi daya idan za'akwanta bacci. 🪔
( 4 ) Yawan cin cucumber 🥒
( 5) ko dinga zam zam acikin idonka
Wannan zasu taemaka ma idanuwa insha Allah