31/08/2025
Lokacin da mace ta haihu, jikinta yana bukatar kulawa ta musamman domin murmurewa da samun cikakkiyar lafiya. Ga hanyoyi masu muhimmanci da masana lafiya ke ba da shawara a farkon makonni biyu bayan haihuwa:
1) Ki yi kokari ki dinga samu kina hutawa a duk lokacin da jaririnki ya ke yin barci.
2) Ki nemi taimako wurin yan uwa ko abokai don su taimaka miki da aiyukan gida – kar ki sake ki matsa wa kanki.
3) Ci abinci mai gina jiki yana taimakawa wajen dawo da lafiyar jiki bayan haihuwa. Ki mai da hankali wajen cin kayan lambu, kayan marmari, hatsi, kifi ko nama.
4) Ana son wadda ta haihu ta yawaita shan ruwa, musamman idan tana shayarwa domin kare jikinta daga bushewa ko karancin ruwan nono.
5) Idan kin samu yagewa a lokacin haihuwa za ai miki dinki, don haka ki kula da tsafar wajen, wanke gabanki da ruwa mai dumi bayan kin yi bayan-gida.
6) Yi amfani da pad har sai kin warke gabaki daya.
7) Amfani ruwan dumi (sitz bath) na iya rage kumburi da radadi a farji.
8) Idan kina jin zafi, ki tuntubi likita kafin shan kowane irin magani.
9) Ki dinga zama a kan matashin kujera mai laushi don rage ciwo.
10) Idan kina jin zazzaɓi ko ciwon mama mai tsanani, ki gaggauta kai rahoto asibiti.
11) Jin sauye-sauye ko damuwa bayan haihuwa abu ne da yake yawan faruwa ga matan da s**a haihu. Ki nemi taimakon likita idan damuwar ta yi tsanani.
12) Kar ki ɓoye abin da k**e ji. Magana da likitoci ko abokai na taimakawa.
13) Ki saurari jikin ki kafin ki koma motsa jikinki sosai.
14) Ki fara motsa jikinki kadan-kadan kuma mai sauki kamar sintiri a cikin gida ko wajen gida, muddin likita bai hanaki ba.
15) Yawaita cin abinci mai kunshe da fiber, shan ruwa don kauce wa matsalar wahalar bayan-gida.
Ba dole ba ne ki koma yadda kika kasance kafin haihuwa nan da nan. Hana damuwa da hakuri sune mafita. Idan kina ganin matsalar lafiya ta yi tsanani, sanar da likita nan da nan.
Idan kina fuskantar zubar jini mai yawa, zazzaɓi mai tsanani, ko wani nau'in ciwo da ke damunki, gaggauta zuwa asibiti ko ki tuntubi kwararren likita.
Allah ya kara lafiya, ya raya mana zuri'a.
⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️
LITTAFI NA MUSAMMAN GA MA’AURATA 👩❤️👨
“Salon Kwanciya da Tambayoyin Jima’i ga Masu Juna Biyu”
Littafin nan yana kunshe da ❓Tambayoyi da Amsoshinsu sama da 20 game da saduwa da mace mai ciki 🤰, tare da 🛏️ salon kwanciya guda 6 da hotuna 🖼️ da cikakken bayani 📝 yadda ake yinsu da amfaninsu.
Yana taimakawa ma’aurata su samu nutsuwa 🕊️ da fahimta 🤝, musamman masu juna biyu.
💰 Farashi: ₦500 kacal!
🏦 Biyan Kuɗi:
📛 Account Name: Hafsat Bako
🔢 Account Number: 0030220053
🏛️ Bank: Sterling Bank
📲 Bayan biyan kuɗi:
Tura shaida ta WhatsApp zuwa: 07049840410
✅ Da zarar an tabbatar da biyan, za a tura maka littafin PDF kai tsaye ta WhatsApp.