Likitanchi A Muslunchi

Likitanchi A Muslunchi Herbal Medicine and Marriage Counseling

ILLLOLIN AMFANI DA CONDOM WAJEN SADUWA.Dafarko condon wata robace da turawa s**a kirkira domin gujewa daukar ciki ko kam...
27/06/2025

ILLLOLIN AMFANI DA CONDOM WAJEN SADUWA.

Dafarko condon wata robace da turawa s**a kirkira domin gujewa daukar ciki ko kamuwa da wasu cuttuka lokachin saduwa kokunsan cewa amfanida condom yanada illa ga lafiyar dan Adam?

A shekarar 2014 Danish sunyi bincike sungano cewa kowane condom yana daukeda abubuwa sama da dari daka iya zama barazana ga lafiyar mata da maza.

wanda sun hada da hormone disruptor, glycerin, petroleum derivatives, spermcides , parabens dadai sauransu wanda duk zasu iya lalata banganyen mahaifar mace.

kada kataba tunanin amfani da condom zaibaka cikakkiyar kariya wajen daukar cutttuka domin abu mai saukine dauki wata cutar jikin condom din.

Bazaka dauki cuta jikin condom kaitsayeba amma ahankali cutttukan zasu rika wanzuwa cikin jikinka.

Domi karin bayani ko neman wasu shawarwari zaku iya Nemanmu a khalifa harbal medicine and marriage councelling

07067344494

YADDA MIYAR KUKA KE KAR KARFIN MAZA DA KARIN NI'IMA GA MATA.Miyar Kuka - ta fi dukkanin sauran gayyakin da Hausawa ke mi...
03/06/2025

YADDA MIYAR KUKA KE KAR KARFIN MAZA DA KARIN NI'IMA GA MATA.

Miyar Kuka - ta fi dukkanin sauran gayyakin da Hausawa ke miya da su amfani ga jiki saboda yawan sinataran da ta ke dauke da su, a cewar masana.

Tabbas kuka ta fi alayyahu da kuɓewa cikin ire-iren gayayyaki da ƴaƴan ita ce da Hausawa ke yin miya da su a abinci.

mutanen ƙauye ke yawan shan kuka yana ƙara masu lafiya, "shi ya sa yawancin cutukan da ake yi a gari da wuya a same su ƙauye."

kuka tana warkar da cututtuka da dama, kuma mutane ba su san amfanin kuka ba ne ya sa suke gujewa amfani da garinta ko ganyenta musamman a abinci.

Maganin da kuka ta ke yi

Kuka tana maganin zazzabin maleriya

kuka tana maganin tarin fuka TB

Tana kara ingana garkuwar jiki

Kuka tana ƙara jini a jiki

Kuka tana maganin gudawa

Kuka tana maganin hakori

Kuka tana maganin ulsa

Kuka tana rage ƙiba

YADDA AKE SARRAFA KUKA DOMIN KARFIN MAZAKUTA DA KARIN NI'IMA

Kuka tana ƙara ni'ima ga mata da mazakuta ga maza

Masana sun saboda tasirin kuka wajen inganta ruwan jikin mutum, tana kuma tasiri wajen ƙara ni'ima ga mata.

Yadda ya k**ata mata su yi amfani da kuma a cewar SHINE , za a samu sassaƙin kuka a wanke sosai sai dinga sha kofi ɗaya da safe da yamma.

Sannañ kuka tana kara wa maza karfin jiki da mazakuta. Haka kuma mazan da ke son jikinsu ya buɗe kuka tana taimakawa saboda sinadaran da ke cikinta.

Maza zasù debo saiwar kuka a shanyata ta bushe banyan ta bushe a tafasa arika shan ruwan kofi daya safe da yamma.

Allah yasa Mudache Ameen

Khalifa harbal medicine and marriage councelling

07067344494

KINSAN AMFANIN DA KANUNFARI KEYI A JIKIN MACE..?Kamar yanda mata ke ajiye Zuma a gida haka yanzu mata basa rabuwa da kan...
02/06/2025

KINSAN AMFANIN DA KANUNFARI KEYI A JIKIN MACE..?

Kamar yanda mata ke ajiye Zuma a gida haka yanzu mata basa rabuwa da kanunfari domin duk wani hadin daka na musamman ko hadin ruwan jaraba ko wani tsumi idan kuka bincika zakuga akwai sa hannun kanunfari don haka kema ki ajiye shi don burge mijinki. .

Duk lokacinda zaki dafa shayi kada kimanta dashi domin
idan ya hadu da lefton yana aiki a jikin mace wajen karin ni'ima kuma ya na da kyau yajinki ya zama akwai kunfari aciki

Ana Amfani da kanimfari wajen rage tumbi ki jika shi aruwa idan ya yini ajike sai kishanye ruwan ki kara wani zaki ga cikin ki ya saki kinyi bayan gida wannan shine alamar yayi miki aiki

Ana Amfani da Kanimfari wajen maganin infection idan kika saka ruwa tafasashe a flast sai ki zuba shi aciki da ganyen magarya kirufe sai yayi k**ar sa'a daya (1 hour) zaki yini kina yin tsarki dashi har zuwa dare. Zaki iya daka garin kanimfari ki hadashi da totuwar raken
dakika sha yabushe sai ki sami farin muski (miskul dahra) ki cakuda shi sosai da garin da totuwar raken da kuma muskin idan ya bushe sai ki ringa turaren tsugunawa dashi wannan kada ki barshi.

Dan Allah ku jaraba kusha mamaki

Daga khalifa herbal medicine and marriage counseling.

07067344494

AMFANIN TAZARGADE AGABAN MACE.Amfanida tazargade yanada matukar alfanu ga lafiyar alaurar mata musamman wajen kashe kway...
01/06/2025

AMFANIN TAZARGADE AGABAN MACE.

Amfanida tazargade yanada matukar alfanu ga lafiyar alaurar mata musamman wajen kashe kwayoyin cuta , kara matsi , ga macenda ta haihu kokuma gabanta ya bude sosai sannan yana taimakawa wajen karama gaban mache danshi da dumi da samarda wadattiyar niima dakuma kashe kwayoyin infection wanda yake janyo matsaloli k**ar haka :

* Karanchin Niima

* Rashin jindadin saduwa da maigida

* Bushewar gaba

* Jin zafi lokachin saduwa

* Fitar farin ruwa na cuta

* Kaikayin gaba.

YADDA AKE AMFANIDA TAZARGADE GA MATA.

Zaa debi cikon babban cokali daya azubashi acikin tafasasshen ruwa k**ar lita biyu faga bisani sai abarshi yadan huche kadan sai ashiga ciki azauna k**ar minti goma .

Anaso amaimaita haka kullum saudaya natsawon sati daya insha Allah zaaga abin mamaki.

Domin karin bayani ko neman wasu shawarwarin zaku iya tuntubarmu kai tsaye akoda yaushe.

Khalifa herbal medicine and marriage counseling

07067344494

AMFANIN GANYEN SHUWAKA GA LAFIYAR DAN ADAM.Mutane da dama kan yi amfani da shuwaka ne kawai a matsayin ganyen miya, amma...
01/06/2025

AMFANIN GANYEN SHUWAKA GA LAFIYAR DAN ADAM.

Mutane da dama kan yi amfani da shuwaka ne kawai a matsayin ganyen miya, amma in an yi amfani da ganyen yadda ya k**ata, akwai magunguna da dama a jikinsa. Masana harkokin bincike kan magunguna na kalifa herbal medicine and marriage councelling munyi matukar bincike kuma mun gano cewar ganyen shuwaka na dauke da sinadarai da dama da ke magungunan cututtuka daban-daban k**ar haka.

1.Ciwon Hanta. Ganyen shuwaka magani ne mai kyau na ciwon hanta ana amfani da shi k**ar haka: A samo abarba da ba ta nuna ba, sannan a samo ganyen yazawa (cashewy guda goma, sai cikin tafin hannu na ‘ya’yan auduga, sai kwalba goma na ruwa wanda za a tafasa. A rinka sha cikin babban cokali daya kullum har kwana goma.

2.A Markada namijin goro guda 20 har ya zama gari sannan a zuba cikin ruwan lemon tsami (Lime juice) a kawo kwalba daya na zuma mai kyau a hada su duka a waje daya a gauraya. A rinka shan babban cokali daya (dessertspoon) sau hudu a rana har na tsawon watanni biyu.

3.Markade ganyen shuwaka guda 40 a zuba cikin ruwa mai kyau da ya kai lita 4 a rinka shan kofi guda sau 3 a rana har na tsawon watanni biyu. Wannan yana magani sosai na ciwon hanta, in ruwan ya dade ana iya sake wani sabon jikon.

4.Zazzabi A tafasa busasshen ganyen shuwaka (gram 10) a samo gram 25 na busasshen garin TUMARIC a dafa a cikin ruwa kofi daya har sai ya tafasa. Tun da duminsa sai a sanya zuma cokali daya, daga nan bayan ya huce sai a sha sau uku a rana. Yana warkar da zazzabi sosai.

5.Sankara (Cancer) Kari (Kulun Da Ke Fita A Jiki) Shan ruwan da aka tatse daga ganyen shuwaka yana taimakawa wajen rage girman kari da jinkirtar da girman kwayoyin cutar sankara. Shan ruwan yana domin yana kara karfin garkuwan jiki.

6.Hawan Jini Ruwan ganyen shuwaka na taimakawa wajen rage yawan gishiri a jikin mutum domin yana dauke da sinadarin ‘potosium’ mai yawa, hakan kuma na kawo saukin hawan jini.

7.Ciwon Siga Yawan shan ruwan ganyen shuwaka a kaidance yana saukar da yawan su da ke cikin jini don haka na rage karfin cutar sugar. Ga yadda ake sha domin maganin hawan jini da na siga: A samo rabin cikin tafin hannu na ganyen shuwaka sabon tsinka, a wanke sannan a dafa a ruwan da ya kai kofi 3. Za a rinka shan ruwan sau biyu a rana.

8.Kaikayin JIKI. A samu gram daya na ganyen shuwaka da gram daya na garin citta a markade har sai ya zama gari sai a sanya a cikin ruwa mai kyau a gauraya a rinka sha sau uku a rana. Yana maganin kaikayin jiki sosai.

9.Maleriya. A samo ganyen shuwa cikin tafin hannu a dafa a ruwa kofi hudu har sai ya kone ruwan ya zamo k**ar saura kofi biyu sai a rinka sha sau uku a rana.

10.Ciwon Afendis (Appendicitis) A samo busasshen ganyen shuwaka gram 30 da ruwa 400ml da zuma mai kyau cikin babban cokali sai a dafa har sai ya kone ruwan ya zamo rabi sai kuma a sauke a kara cokali guda na zuma kuma in ya yi sanyi sai a rinka sha sau uku a rana a kai a kai.

11.Zazzabin Shawara (Typhoid) Haka kuma shuwaka na maganin typhoid in an sha k**ar haka. A samo ganyen shuwaka guda 10 zuwa
15 a dafa har sai ruwan ya rage kofi daya sai a bar shi ya yi sanyi sannan a zuba masa zuma a rinka sha a kai a kai kofi daya a kullun.

12.Ciwon Kunne Shuwaka na maganin ciwon kunne sosai. A samo ganyen shuwaka (fresh) a markade shi sai a rinka diga ruwan digo uku a kunnen da ke ciwo sau uku a rana kuma za a yi hakan har na kawanaki 4 zuwa 5. Wannan ganye na shuwaka yana yin magungunan cututtuka da dama. Sai dai kuma a lura cewa idan aka sha har yawansa ya wuce kai’da yana da illoli a jiki; k**ar sanya ciwon kai, gudawa da sauransu.

Da fatan za a yi amfani da shi yadda ya dace dan Allah duk wanda ya karanta wannan sako to ya ya yadashi duniya domin amfanuwar yanuwa musulmai. wannan faida tasamo asali daga Khalifa herbal medicine and marriage councelling

07067344494

AMFANIN IICEN DOGON YAROItacen dogon yaro ko kuma dalbejiya ya kasance ice mai matukar amfani ko a al’adar bahaushe. Ana...
31/05/2025

AMFANIN IICEN DOGON YARO

Itacen dogon yaro ko kuma dalbejiya ya kasance ice mai matukar amfani ko a al’adar bahaushe. Ana kiran itacen da ‘Neem tree’ a turance. Tana da daci amma tana da matukar amfani a jikin dan Adam.

Ga wasu amfanin dalbejiya a jikin mutum:

1. Ganyen dalbejiya na kare mutum daga kamuwa da cutar bugawar zuciya, musamman idan aka dafa ganyen ana shan ruwan k**ar shayi.

2. Yana taimakawa wajen tacewa da tsaftace jinin jikin mutum.

3. Ganyen na maganin cutar zazzabin cizon sauro da typhoid.

4. Yana maganin cutar ciwon ciki, musamman idan mutum ya murde saboda wani abinci da aka ci.

5. Ganyen dalbejiya da man shi na gyara fatar jikin mutum.

6. Ganyen na maganain saiko, amosanin kai da kuma sa tsawon gashin kai.

7. Ana iya amfani da man dalbejiya a matsayin dabarar bada tazarar iyali.

8. Ganyen na kawar da cutar daji, musamman na nono da ‘ya’yan maraina.

9- Man diyan dalbejiya yana maganche kuraje kowane irine kai atakace yana magache duk wata matsala da tashafi fata koda kuturtache.

Allah Kabamu lafiya da zama lafiya

Khalifa heŕbal medicine and marriage councelling

07067344494

080 83 389761

AMFANIN MANGWARO WAJEN KARA LAFIYAR JIKIN DAN-ADAM 1.Yana sakin tsokar zuciya ta samu dadin yin aikinta.2.Mangwaro yana ...
30/05/2025

AMFANIN MANGWARO WAJEN KARA LAFIYAR JIKIN DAN-ADAM

1.Yana sakin tsokar zuciya ta samu dadin yin aikinta.

2.Mangwaro yana dawo da dandano ga marar lafyar da
ba ya jin dandano.

3.Yana ba da kariya daga kamuwa da cutar Syphilis

4.Yana kara gudanawar jini.

5- Mangwaro yana taimakawa wajen kariya da kamuwa daga cutar kansa.

5.Yana gyara idanu, da warkar da cutar ido, misali
kaikayin ido, zafin ido ko ido yay ja.

6. Mangwaro yana temakawa wajen fitar da bahaya ga masu yin kashi da tauri.

7.Yana sa fitsari ga masu matsalar rashin fitarsa.

8.yana wanke ciki sannan yana taimakawa wajen
narkar da abinci.

9.Magwaro yana gyara jiki ta hanyar fitar da abubuwa
masu cutarwa ga jiki.

10.Yana magance yawan zafin jiki, k**ar zazzabi
sannan yana maganin yawan gumi, ko jin zufa.

11. Mangwari yana taimakawa wajen wanke koda.

12.yakan temaka wajen saurin warkewar rauni da bada kariya ga ciki daga cututtuka.

AMMA A KULA

Duk da dumbin amfanin da Mangwaro yake da shi
zai iya cutarwa idan aka sha shi ba bisa ka'ida ba.
Saboda
★Yawan shan Mangwaro yana sa sinadarin
sikari dake cikin jinin mutum ya nunku, wanda
hakan barazana ne ga lafiyar jiki.

★Shan sa ba bisa ka'ida ba yana sa ciki ya saki,
har ta kai ga gudawa.

★Shan Mangwaro da yawa yana kara nauyi da
te6a a jikin mutum. Don haka masu son rage kiba
kada su yawaita shan sa.

★A shawarce, idan za a sha Mangwaro to ya fi
kyau a sha shi shi kadai, kada a hada shi da wani abu k**ar masu kara masa sikari ko kuma yankawa a abinci.

07067344494
08083389761

Allah yasa mu dace

11/03/2025

MAGANIN SAURIN KAWOWA DA KARFIN GABAN NAMIJI.

Hanyoyin magance saurin inzali suna da yawa , wasu hanyoyin na yiwa wasu aiki, wasu kuma sabanin haka , don haka ga hanyoyi k**ar haka da mutum zai iya jarrabawa domin neman dacewa:

a) Rage ƙosawa/ƙagara. Mai saurin inzali ya k**ata ya cire tunanin jima'i daga ƙwalwarsa a lokacinda yake saduwa da iyalinsa. Matsanancin tunani ko kamuwa da yawa kafin fara jima'i zai iya sanya mutum "ya ƙone tun kafin ya tafasa". Masana sun nuna cewa bujiro tunanin wani abu a cikin rai wanda ba jima'i ba marar daɗi a lokacin saduwa na ƙarawa mutum tsawon lokaci ba tare da ya lura da hakan ba. Ɗaukin jima'i baya biya, abinda zai taimakawa mai matsalar saurin kawowa shine, rage yawan tunanin jima'i ne yake aikatawa, ko kuma ya bar yin tunanin cewa yana yin jima'i ne domin samun gamsuwa wacce iyalinsa da yake sha'awa take biya masa. Kamata yayi tunaninsa ya kasance cewa yana aikata jima'i ne domin ya biyawa iyalinsa bukata farko kamin tasa. Abin lura, ka ɗauka ma cewa ba jima'i bane kake yi a lokacinda kake tarawa da iyalinka.

b) A nemi kuɓewa ɗanya (okra) guda 5, a wanke sa'annan a yanke gutsun-gutsun a cikin tukunya, sai a sami kofi ɗaya na ruwa a zuba cikin tukunyar sa'annan a ɗaura akan wuta a rufe tukunya. Da zaran ruwan ya tafasa sai a sauke tukunya a tashe ruwan a kofin shayi , sai a zuba zuma ta bada ɗanɗano , a bari ya huce kaɗan amma asha da ɗumi. Ayi haka sau 2 a rana har na tsawon kwana 10 ko fiye da haka. Kubewa nada sinadari mai amfani mai sanya jinkirin kawowa ga maza.

c) A nemi citta (ginger) musamman ɗanya, a wanke a kuma karkare ta , sa'annan a dake ta , ayi shayi da ita , bayan an tashe ta a kofin shayi sai a zuba zuma ta bada ɗanɗano asha shayin da ɗumi. Ayi hakan safe da rana. Citta nada sinadari mai zafi na "gingerol" mai sanya yawan gudanar jini ga laura , wanda hakan na sanya ƙarfin gaba da jinkirin kawowa.

d) A nemi man na'a-na'a (peppermint oil) mai kyau, musammman ɗan Misra ko na kamfanin Hemani (Pakistan) . A wanke gaba da ruwan dumi , a goge lemar sa'annan a shafa man ga zakari ya shiga fata, ga kai (g***s) da tsawon sandar zakari (shaft) , amma banda kofar fitsari (urethra). Musamman a shafa idan zakari yana mike, sai jira bayan minti 10 zuwa 15 sa'annan a sadu da iyali. Man na'a-na'a na rage "sensitivity" na zakari , wato rage kaifin ɗanɗano da zakari keji ta yanda zai hana saurin kawowa lokacin jima'i. Haka kuma za'a iya amfani da man kanimfari (clove oil) mai kyau a maimakon man na'a-na'a. Bugu da kari, man kanimfari na maganin karfin gaba.

e) Fita daga gaban mace na 'yan mintoci a lokacinda mutum yaji ya kusa kawowa, da kuma fita daga cikin farji da matse kan zakari da hannu (squeeze and pause technique/pen*s grip) a lokacinda mutum yake akan hanyar kawowa.

f) Bayan kawowar farko, kawowa ta biyu na zuwa da lokaci mai tsawo kafin mutum ya sake fitar da wani maniyyin a karo na biyu. Don haka idan mutum yana son ya daɗe bai yi inzali ba to ya tari jima'i a karo na biyu wanda zai bashi lokaci mai tsawo kafin yayi inzali.

g) Hanyoyin neman magani na musamman daga Likitan asibiti ko Malamin Islamic Chemist. Idan hanyoyin da muka zayyana basu yiwa mutum ba to sai yabi hanyar ganin ɗaya daga cikin wadannan mutanen domin neman taimako. Akwai wasu hanyoyi da dama na magance mastalar. Khalifa herbal medicine and marriage councelling

07067344494

08026494424

MAGANIN RIKICEWAR ALADA DA DAUKEWAR ALADA DA ZOBO.Zobo wanda mukasani da ake sarrafawa da kayan kamshi da irinsu citta d...
04/02/2025

MAGANIN RIKICEWAR ALADA DA DAUKEWAR ALADA DA ZOBO.

Zobo wanda mukasani da ake sarrafawa da kayan kamshi da irinsu citta da kaninfari asha domin samun nishadi to ba anan kadai yatsayaba zobo yana taka muhimmiyar rawa wajen inganta lafiyar dan adam misali.

Amfani da zobo yadda yadace babu shakka yana saukaka rikicewar alada sannan yana maganin daukewar alada dakuma inganta zuwan jinin aladar yadda yak**ata.

Idan kina fama da rikicewar alada amfani da zobo yana taimakawa wajen daidaita aladar bugu da kari bayan maganche rikicewar aladar to amfani da zobo yana maganin ciwon mara lokachin aladar.

Yanada kyau mata su fahimchi kowace mace akwai akwai yanayin yadda alada kezomata , wasu alada kanzo kowane wata wasu kuma s**an tsallake watanni kai wasuma tana zuwa farkon wata wani lokachin tsakiyar wata wani lokachin ma karshen wata, shi jinin alada zai iya chanzawa akowane lokachinda wasu alamurran rayuwa s**a chanza.

Mata dayawa s**an fuskanchi matsalar rikicewar alada lokachinda tsufa ke riskarsu maana idan suna kusa da gama jinin aladar baki daya.

Hanyarda zakibi domin gane kinada rikicewar alada ko akasin haka shine kirubuta lokachinda jinin kezomaki kowane wata sannna ki kirga kwanakin ki gani shin suna zuwa daidai ko suna sabawa?.

Idan kika tabbatar da suna sabawa abinda zakiyi shine kisamu zobonki mai kyau kidafa kisa citta da kaninfari ki kirga daga ranar da kika fara period zuwa kwana sha hudu kisha duk bayan kwana daya har ranar dazakifara wani period din saiki daina to insha Allahu duk wani matsalar period kowane iri zakiga chanji.

Do Allah duk wanda Yakaranta wannan post yayi kokarin watsama duniya Domin Alumma dayawa su amfana.

Allah yabamu dacewa Ameen daga khalifa herbal medicine and marriage counseling

07067344494

AMFANIN GANYEN BADO DA SAIWARSA DA FURENSA.(1) Saiwar bado idan akayi garinta ana sha da madara tana kara ruwan maniyyi ...
29/01/2025

AMFANIN GANYEN BADO DA SAIWARSA DA FURENSA.

(1) Saiwar bado idan akayi garinta ana sha da madara tana kara ruwan maniyyi sannan tana maganche sanyi kowa kala.

(2) Sama da shekaru dubu ana amfanida furen bado akasar Egypt ( Misra ) domin maganche matsaloliin saduwa da neman haihuwa.

(3) Anayin shayi da ganyen bado asa zuma asha sau biyu kullum domin kara karfin maza da karin niima ga mata. Yanada kayau mata da miji su rike wannan fatawa.

(4) Anayin shayi da furensa asa zuma cokali biyu kafin akwanta bacci yana kara ma mutum walwala da Nishadi.

(5) chin tsabar bado akai akai yana kara karfin kwakwalwa.

(6) Ana daka garin ganyen bado akwaba da zuma arika shan cokali biyu da safe biyu da yamma tsawan wata biyu yana maganin ciwon hanta.

(7) Mache mai fama da yawan Bari intasamu juna biyu tasamu saiwar bado ta wanke sosai tayo gari tarika zuba cokali daya cikin ruwan dumi zuma cokali daya tana sha sau biyu kullum Insha Allah zata samu lafiya.

(8) Mai fama da ciwon hauka ko falfadiya arika shayi da ganyen bado da ganyen doddoya ana sa zuma yanasha safe da yamma insha Allah zai warke hauka.

Mutane dadama na bukar ganin wannan post duk wanda Allah yasa Ya karanta yayi kokarin sharing dinsa ga Yanuwa. Domin karin bayani koneman wasu shawarwarin zuku iya nemanmu akoda yaushe.

Khalifa herbal medicine and marriage counseling.

07067344494

08083389761

28/01/2025

ALAMOMIN CIWON SANYIN MARA NA MATA / SANYIN MATA WANDA AKE YAƊAWA TA JIMA'I

Waɗansu daga cikin alamomin ciwon sanyin mata da ake samu ta hanyar saduwa da namiji ko mace mai ɗauke da ciwon : (STD/STI):

1. Fitar ruwa daga farji, ruwa mai kauri ko silili, kalar madara ko koren ruwa daga farji.

2. Kuraje masu ɗurar ruwa da fashewa a farji , musamman wurinda pant ya rufe.

3. Feshin ƙananan ƙuraje a farji ko cikin farji

4. Raɗaɗin zafi a lokacin yin fitsari

5. Jin zafi cikin farji lokacin jima'i

6. Zubar jinin al'ada mai yawa ko zuwan jinin al'ada mai wasa, wato akan lokacinda ya saba zuwa ba

7. Ciwon mara

8. Zazzaɓi

9 . Ciwon kai

10. Murar maƙoshi/maƙogwaro

11. Kasala/raunin jiki

12. Zubar jini lokacin saduwa

13. Dakushewar sha'awa, ko rashin sha'awa ko ɗaukewar ni'ima

14. Bushewar farji

15. Ƙaiƙayin farji

16. Warin farji (ɗoyi) mai ƙarfi

17. Kumburin farji da yin jawur

18. Gudawa

18. Ko rashin ganin wata alama daga cikin wadannan alamomin da muka bayyana a sama.

A can baya munyi bayanin ciwon sanyin mata na "toilet infection" (vaginitiies: Yeast infection & Bacterial vaginosis) wanda cutar sanyin mara ce wacce ba'a yaɗata ta hanyar jima'i - wato sanyin mara wanda mace bazata iya harbin mijinta da cutar ba, wanda akafi samu daga "toilet" (bandaki/bayan gari). Duk da haka , munyi bayanin wata nau'in cutar sanyi guda 1 (Trichomoniasis) a cikin waɗancan bayanan da s**a gabata, wacce cuta ce da mace ka iya sakawa mijinta ciwon (STD). A wannan karon kuwa zamu yi bayani ne kaɗai akan ciwon sanyin mata wanda akafi samunsa ko yaɗawa ta hanyar jima'i (STD/STI).

Ciwon sanyi cuta ce da akafi yaɗawa ta hanyar jima'i, wato ta hanyar saduwa da mai dauke da ciwon, shiyasa ake kiran dangin cututtukan da turanci da suna SEXUALLY TRANSMITTED DISEASES/ SEXUALLY INFECTIONS (STDs/STIs), wato CUTUTTUKAN DA AKE YAƊAWA TA HANYAR JIMA'I. Ciwon sanyi anfi yaɗasa ne ta hanyar jima'i kuma maza na iya harbin mata da ciwon ko kuma su matan masu ɗauke da ciwon su sakawa maza mararsa ciwon. Ciwon yafi yaɗuwa kuma anfi samunsa ga maza masu neman mata ko mata masu bin mazaje.

Haka kuma za'a iya samun cututtukan sanyi ta wata hanyar daba jima'i ba, k**ar ta hanyar bada jini ga marar lafiya - jinin mai ɗauke da cutar sanyi daga wani mutum, ko haɗuwar jikin wani da wani - fata-da-fata ; wato idan fata mai ɗauke da cutar ta fashe zata iya harbin fatar wani mutum mai lafiya da cutar, ta jini ko ruwan jiki dake a jikin fatar mai cutar zuwa fatar wanda baya da cutar - wato idan akwai kafa buɗaɗɗiya komin ƙaƙantarta zuwa cikin hanyoyin jinin wanda baya da ciwon a fata zai iya samun cutar, misali ta hanyar sunbata (kissing) ko tsotsar al'aurar mai ciwon (oral s*x), ko ta hanyar saka kayan sawar wata (pant) mai ɗauke da kwayar cutar mai rai, ko ta hanyar amfani da reza (razor blade) wanda wani yayi amfani da ita, rezar mai ɗauke da kwayar cutar mai rai, da kuma wasu hanyoyin na daban. Ataƙaice, ƙwayoyin halittun dake sanya cutar ana yaɗa sune daga wani mutum zuwa wani mutum, ta jini, maniyyi, ruwan farji ko ruwan jiki.

Alamomin ciwon sanyi ga mata sun sha banban tsakanin mata wanda ciwon ya harba. Hakan ya danganta ne da nau'in ƙwayar halittar cutar wacce ta haddasa ciwon da kuma matakin da cutar ta takai a jikin mace - ma'ana, alamomi ko matakin farko da kamuwar cutar ko alamomi na gaba bayan ta soma jimawa a jikin marar lafiyar. Haka kuma, suma yanayin alamomin sunsha banban ta fuskar tsanani ko sauƙinsu, koma rashin ganin alama ko ɗaya duk da cewa kau akwai cutar a jikin mace. A taƙaice dai, alamomin ciwon sanyin zasu iya ɓuya amma gwaji a asibiti zai iya nuna akwai cutar ko akasin haka.

Alamomin ciwon sanyi na " toilet infection " na iya k**a da alamomin cutar sanyi da ake samu ta jima'i (STD/STI). Saidai banbancin shine hanyoyin samun cututtukan , kuma cutar sanyin "toilet infection" tafi saukin magancewa; ita kuwa cutar sanyin da ake yaɗawa ta jima'i (STD) nada wuyar magani da naci, musamman saboda wasu na'uin cutar daga kwayar cutar "virus" ne (k**ar "syphillis" da "ge***al herpes"). Gwaji a asibiti shine zai iya nuna na'uin cutar da maganin da ya dace, imma "toilet infection" ko kuma cutar sanyin jima'i wacce tafi muni da wuyar magani.

MATSALOLIN DA CIWON SANYIN ZAI IYA HADDASAWA MACE:

a) RASHIN SAMUN JUNA-BIYU/ HAIHUWA: Cutar sanyi mai suna "Gonorrhea" (Gonoriya) , ƙwayar cuta ce daga halittar "bacteria" kuma zata iya laɓewa a cikin jiki ba tare da wasu alamomi ba. Itace mafi tsohuwar cutar sanyin da akafi sani. Gonoriya bata cika nuna alamun taba a jikin mace, musamman a matakin farko na shigarta cikin jiki, ba k**ar ga maza ba wanda alamomin kan bayyana gare su . Mata da yawa basu san ma suna dauke da cutar ba a jikinsu. Duk da haka, tana iya zuwa da alamomi k**ar fitar ruwa daga farji ko ɗan koren ruwa, mai kalar madara daga farkon cutar, yin fitsari da zafi da yawan yin fitsari, yawan zubar jinin al'adah, murar maƙoshi/maƙogwaro, jin zafi a farji yayin jima'i, da sauransu. Idan ba'a lura da cutar da wuri ba kuma aka magance ta, zata iya sanya rashin haifuwa ga mace ko namji. Tana shafar wani hangaren mahaifa da yi masa dameji, sai mace ta kasa samun juna-biyu.

Haka kuma itama cutar "Chlamydia" (kilamidiya), wacce kwayar halittar "bacteria" ke haddasata , na daga cikin game garin cutar sanyi wacce ke hana mace ɗaukar ciki. Hakan yafi faruwa idan mace nada cutar na tsawon lokaci ko kuma ta samu cutar wasu lokutta na rayuwarta da dama. Idan an gano cutar kuma an magance ta da wuri zai rage illa ga mahaifar mace a gaba. Cutar "Chlamydia" maɓannaciya ce da take illa a ɓoye kuma mafi yawanci bata nuna wata alama a zahiri ga mai ɗauke da cutar. Ana samunta bainar mata da yawa fiye da maza. Mafi yawanci bata nuna wata alama sai haddasa rashin haihuwa.

b) RASHIN JIN DADIN JIMA'I , ƊAUKEWAR NI'IMA , KO DAKUSHEWAR SHA'AWA KOMA RASHINTA

Sanyin gaba mai zuwa da 'yan 'kananan kuraje cikin farji , na sanya mace taji zafi wajen jima'i yayinda zakari ke kai-kawo cikin farji, wanda sau da yawa masu kurajen basu ma san suna da kurajen ba cikin al'aura, saidai s**e suna jin zafi lokacin saduwa. Kurajen suna fashewa saboda da gugar zakari, sai wurin ya zama rauni. Hakan nasa mata tsoron jima'i da ganinsa abin azabtarwa gare su mai maimakon abin jin dadi. Sau tari basu san abinda ya haddasa zafin ba, wanda kuma mai yiwuwa ciwon sanyi. Ciwon sanyi na iya dakushe sha'awar mace ko namiji. Ciwon sanyi na iya haddasa bushewar gaba (vaginal dryness) wanda alamunsa shine daukewar ni'ima da 'kaikayin gaba. Idan gaba ya bushe zaiyi wahala mace da miji suji dadin jima'i in banda zafi.

Wasu daga cikin cututtukan sanyin da ake samu ta jima'i da ƙwayoyin halittu wanda ke haddasa su (a yaren turanci):

a) CHANCROID (bacteria) , cuta ce wacce ke zuwa da yanayin gyambo wani lokacin tare da ƙululu a hantsa.

b) CRABS (parasite), 'yan ƙananan halittu sosai , yanayin kwalkwata, masu cizo da tsotsar jini mai sanya mugun ƙaiƙayi. Ana samunsu daga gashin mara inda s**a maida gidansu, ana kuma iya ɗaukarsu daga gashin gaban wani mutum zuwa na wani lokacin jima'i. Ana kuma iya samunsu ta kayan sawa, gado da sauransu.

c) GE***AL HERPES (virus) , cuta wacce take zuwa da ƙuraje masu ɗurar ruwa a baki ko kan zakari, ƙurajen masu k**a dana zazzaɓin dare (fever blisters). Idan ƙurajen s**a fashe sai su zama gyambo. Haka kuma za'a iya samun ƙurajen a ɗuwawu, cinyoyi, ko a dubura. Ciwon kai ko baya, ko mura (flu) mai ɗauke da zazzaɓi, ko kaluluwa da raunin jiki/kasala.

d) SYPHILIS (bacteria), anfi samunta wajen 'yan luwaɗi. Tana da matakai bayan shigarta a jiki. Misali, matakin farko (1): fitowar wani irin gyambo (chancre), wannan gyambon shine wajenda cutar ta shiga jikin mutum. Gyambon mai tauri, mai zagaye marar zafi. Wani lokacin abuɗe yake kuma da lema, ko zurfi musamman a hular zakari, wanda zaka ga wurin ya lotsa. Ana samunsa a zakari ko dubura ko leɓe (a baki). Ana kuma iya samun gyambon a ɓoye wani wajen cikin jiki. Mataki na biyu (2): ƙuraje a tafin hannu ko ƙarkashin tafin ƙafa ko wani sashen na jiki. 'Yar mura, zubar gashi, zazzabi marar tsanani, kasala, murar maƙoshi, ciwon kai ko ciwon naman jiki da sauransu. Mataki na gaba: mataki na gaba ko ƙarshe shine wanda cutar zata iya ɓoyewa a jiki, 'buya idan ba'a magance taba, kuma zata iya sanya ƙululun kansa/ciwon daji (tumour), makanta, mutuwar sashen jiki, matsalar ƙwalwa, kurumta, ciwon mantuwa mai tsanani (dimentia). Ana iya magance cutar cikin sauki da idan an lura da ita, da wuri, da yardar Allah.

e) TRICHOMONIASIS (parasitic organism) , cutar sanyi maisa warin farji, mace zata iya harbin mijinta da cutar ko mijin ga matar. Idan ya kasance miji nada wata mata ko yana neman matan waje masu cutar ko kuma macen ta taba saduwa da wani mutum mai cutar daya samo cutar daga wata mace, to akwai yiwuwar ma'aurata su samu cutar. Mazaje ba kaso suke sanin suna da cutar ba kasancewar alamomin cutar basu cika bayyana ga maza ba. Yawanci sai idan ciwon ya k**a matan su suna cikin neman magani a asibiti suke gano suna da cutar. Wasu daga cikin alamomin cutar ga mata: zubar ruwa mai launin kore-da-dorawa - mai kumfa da wari, zafi wajen yin fitsari, rashin jin dadi wajen jima'i. Wannan cuta tana da hadari ga mace mai juna-biyu da abinda ke cikinta

f) DA SAURANSU, suna da yawa kuma alamomin wani ciwon na k**a da na wani ciwon wani lokacin. Don haka bincike a asibiti shine zai nuna nau'in ciwon.

Ciwon sanyi anfi yaɗasa ne ta hanyar jima'i kuma maza na iya harbin mata da ciwon ko kuma su matan masu ɗauke da ciwon su sakawa maza mararsa ciwon. Ciwon yafi yaɗuwa kuma anfi samunsa ga maza masu neman mata ko mata masu bin mazaje. Haka kuma mutum zaya iya kamuwa da ciwon ta wasu hanyoyin na daban daba jima'i ba. Kuma lallai ciwon nada wuyar magani , musamman idan mutum bai samu magani ingantacce ba. Zai iya yin wuyar magancewa saboda rashin samun sahihin magani ko daɗewarsa cikin jiki ba'a magance ba. Sau da yawa zaka ga cewa mutane s**an sha magunguna domin kaiwa ciwon hari da s**ar alluran likita amma hakan bai razana ciwon ba sai kaga yana wa mutane jeka-ka-dawo tsawon watanni koma shekaru da dama ba'a samu waraka ba.

DOMIN NEMAN MAGANI

07067344494

26/01/2025

MAGANIN SANYIN MATA KO INFECTION

Idan mace tana fama da kaikayi ko kuraje ko fitar farin ruwa mai wari ko bushewa ko daukewa ko budewa da kwailewa da rashin sha'awa ko gamsuwa da sauran cututtukan sanyi, sai a gwada daya daga cikin wadannan hanyoyi.

1)A samu Saiwar Garafuni da Sassaken Magarya, sai a tafasa, idan ya dan huce sai mace ta dinga k**a ruwa da shi. Kullum sau daya.
Yana maganin budewa da kaikayi.

2) A samu Garafuni da Sassaken Sanya sai a tafasa,
Sai mace ta dinga shan rabin kofi da safe, rabi da yamma.
Yana fitar da dattin mara da maganin farin ruwa mai wari.

3) A samu Furen Tumfafiya, sai a shanya ya bushe, a daka a dinga zubawa a cikin Nono ana sha.
Yana magance matsalar ruwan infection.

4) A samu Lalle da Ganyen Magarya da Kanumfari, a hada waje daya a daka sannan a tafasa a zuba farin miski a ciki. Idan ya dan huce sai ta shiga ciki ta zauna tsawon k**ar minti goma.
Yin haka yana maganin kaikayi da kuraje da budewa da dadewar gaba.

5) A samu Kabewa a dafa ta, bayan an dafa sai a tsame daga ruwa a jajjagata ko a birga, a zuba Madara ko Nono sannan a sa Zuma a sha.
Wannan yana mganin rashin sha'awa da bushewa da rashin gamsuwa.

6) A dafa Zogale, idan ya dahu sai a murje shi ko a dama, a tace, a yi lemon juice da shi.
Yana maganin fitar farin ruwa mai wari da cushewar mara kuma yana kara ni'ima.

7) A samu `Dan-Tamburawa da Albabunaj a tafasa a zuba Man Hulba a ciki.
Sai ta dan tsuguna tururin ya dinga shigarta.
Idan ya dan huce kuma sai ta shiga ciki ta zauna.
Zai magance mata kaikayi da kuraje kuma yana sa matsewa.

8)A samu Farar Albasa da Kanumfari da Citta da Malmo da Barkono da Raihatul Hubbi,
sai ta dake su tayi Yaji ta dinga cin abinci da shi.
Yana saukar da ni'ima da magance duk
matasalolin sanyi.

9)A samu Sabulun Zaitun da Sabulun Habba sai a daka su.
A samu ganyen Magarya da Garin Bagaruwa a daka a tankade.
Sai a zuba akan sabulan da aka daka sannan a kwa6a da Ma'ul Khal, a zuba Man Tafarnuwa da Farin Almiski.
Sai mace ta dinga k**a ruwa da shi kullum sau daya. Da ruwan dumi amma ake tsarki da shi. Wannan Sabulu yana maganin kuraje da kaikayi da fitar wari.

10) A samu Man Zaitun da Man Habba da Man Tafarnuwa da Man Kanumfari sai a hadesu waje daya.
Mace ta dinga shan cokali daya kullum kafin ta karya.
Yana wanke dattin mara kuma yana samar da ni'ima.

11) A samu Ciyawar Kashe-Zaqi da Farin Magani sai ta hada waje daya ta dinga jika rabin karamin cokali tana sha. Sannan ta dinga shan Man Zaitun Cokali daya kullum kafin ta karya.
Wannan yana maganin dattin mara da wanke daudar mahaifa.

ABUBUWAN DA SUKE KAWOWA MATA CIWON SANYI KO INFECTION.

1)Rashin sanya pant.
2)Barin pant yayi dauda sosai ba a canja ba.
Ana so in da hali kullum a canja pant sau biyu a wanke.
3)Saka pant a jiqe da ruwa.
4)Yawan tsarki da ruwan sanyi.
5)Yawan tsarki da ruwan da zafinsa yayi yawa.
6)Rashin aski.
7)Wasa da gaba.
8)Yawan cin `Danyar Albasa.
9)Yin amfani da Magungunan mata marasa inganci.
10)Dadewa akan Masai ko toilet.
11)Rashin shan iska.
12)Musanyar tufafi.
13)Saduwa da mai cutar.
12)Cutar Aljanu, wato

Jinnul Ashiq. Su ma suna sanyawa mace infection mai wuyar magani.

ILLOLIN DA SANYI KO INFECTION YAKE YI WA MATA

1)Yana sa Rashin Sha'awa.

2)Yana sa ciwon mara mai tsanani.

3)Yana haifar da kurajen bakin mahaifa ko ya toshe mahaifar baki daya.

4)Yana sa mace ta dinga jinin al'ada baki kirin mai wari.

5) Yana sanya farin ruwa mai wari ya dinga fito mata.

6)Yana sanyawa a dinga jin mace tana wari mara dadi kuma a rasa ta ina yake fitowa duk wankanta.

7)Yana sa jin zafi yayin saduwar aure ko kuma ganin jini a maimakon ruwa.

8)Yana rikitawa mace kwanakin al'adarta, su dinga karuwa ko raguwa ko jinin ya dinga wasa.

9)Yana sanyawa mace tusar gaba, wato iska ta dinga fita ta gabanta.

10)Yana sanyawa mace yawan `Barin ciki ko kuma rashin shigar cikin kwata-kwata.
11)In yayi karfi yana hana mace haihuwa.

12) Wani infection din alama ce ta zaman Aljanu a jikin mace, musamman idan tana mafarkin namiji dare ko jarirai.

Abin lura:-
Idan mace tayi magungunan Asibiti
da kuma irin wadannan da mu ka ambata amma infection din bai warke ba, To ta nemi maganin jinnul Ashiq, wato magungunan Aljanu don zai iya yiwuwa matsalarsu ce.
Sannan duk maganinda muka fada to tabbas muna saida hadaddensa.

Ina rokon dan Allah duk wanda yakaranta wannan post to yayi share dinshi domin kararuwar yan uwa musulmai. Daga khalifa harbal medicine and marriage councelling.

07067344494

Address

Katsina

Telephone

+2347067344494

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Likitanchi A Muslunchi posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category