10/02/2026
TARAWIHI TSAKANIN TSAWAITAWA DA TAKAITAWA
Ya kamata mu duba nassosin shari’a gaba ɗayansu, ba mu ɗauki nassi guda mu yi amfani da shi a wajen da ba shi ne abin da ake magana a kansa ba. Misali, Annabi ﷺ ya ce: *“Idan ɗayanku ya yi (limanci) salla, to ya sauƙaƙa, domin a cikinku akwai mai rauni da tsoho, da mai bukata.”*
Wannan hadisin yana nufin sallar farilla. Wato idan mutum yana yin salla, musamman sallar Isha’i, Magariba, da sauran sallolin farilla, ya kamata a sauƙaƙa su gwargwadon yanayin masu salla.
Amma wasu salloli na daban, misali sallar kusufin rana ko wata, sunnah ce a tsawaita ta. Annabi ﷺ ya kasance yana karatu har sai kusufin ya gushe. Ma’ana, yana iya yin raka’a biyu ko fiye da haka. Saboda haka idan wani ya zo ya ce mana: shi mara lafiya ne ko mai bukata ne, sai mu ce masa: kada ka yi wannan salla, domin ita sunnah ce mustahabbiya, kuma bukatunka watakila sun fi cancanta ka kula da su a wannan lokacin.
Haka ma sallar Tarawihi. Sunanta Tarawihi wato: huhhutawa (bayan doguwar tsayuwa) kuma ana kiran ta Qiyam saboda tsawon tsayuwar liman a cikinta. Shi ya sa, idan liman yana son ya karanta juzu’i ɗaya, ko biyu, ko uku, sai wasu mutane su zo su ce “a tausaya mana”. Sai mu koma mu duba nassosi: shin a irin waɗannan salloli—kamar sallar Qiyam, Tarawihi, da sallar kusuf—sunnah ita ce gajarta ko tsawaita? Halin salaf kuwa shi ne suna jingina da sanda saboda tsawon tsayuwa; daga tsawon raka’a huɗu sai su huta, sannan su ci gaba. Wannan yana nuna cewa asali a wannan sallah shi ne tsawaitawa.
Saboda haka, kada mu gauraya nassosin shari’a mu ce: sunnah ita ce taƙaitawa, ko gajartawa, ko sauƙaƙawa a kowane hali. Eh, hakan yana cikin sallar farilla. Amma a sallolin nafila, abin da aka fi so shi ne mutum ya kiyaye su kamar Tarawihi, domin asalinsu tsawaita salla ne.
Allah Ya albarkace ku. Idan wani me uzuri ya ce: “Ni ina so in yi Tarawihi,” sai mu ce masa: ka yi ta a gidanka. Domin sallar mutum a gidansa ta fi alheri sai dai sallar farilla, kamar yadda Annabi