16/03/2026
Me Ke Kawo Habo? Ga Hanyoyin Dakatar da Zubar Jinin Hanci?
Assalamu Alaikum Everyone! Sunana Attahir Abubakar (Dr. Tariq) a yau zamudanyi tsokaci a kan zubar jini a hanci (Habo) da hanyoyin dayakamata abi idan yafaru.
Habo wato zubar jini daga hanci matsala ce da mutane da dama kan fuskanta a wani lokaci. A mafi yawan lokuta ba matsala mai tsanani ba ce, amma wani lokaci tana iya nuna cewa akwai wata matsalar lafiya da ya kamata a kula da ita.
Masana lafiya sun bayyana cewa hanci yana da ƙananan jijiyoyin jini masu yawa, kuma waɗannan jijiyoyin suna kusa da saman fata. Saboda haka suna iya fashewa cikin sauƙi su jawo zubar jini.
Dalilan da Ke Kawo Habo
Masana daga Mayo Clinic sun bayyana cewa akwai dalilai da dama da ke jawo habo.
1. Bushewar Hanci:
Idan iska ta yi bushe ko sanyi sosai, cikin hanci na iya bushewa. Wannan bushewar na iya sa ƙananan jijiyoyin jini su fashe su jawo zubar jini.
2. Tsotsar Hanci da Yatsa:
Yawan saka yatsa a hanci ko tsotsar hanci na iya raunana ƙananan jijiyoyin jini, wanda zai sa su fashe.
3. Ciwon Sanyi ko Allergy:
Ciwon sanyi ko rashin jituwa da wasu abubuwa (allergy) na iya sa mutum ya rika goge hanci akai-akai, wanda zai iya haifar da zubar jini.
4. Bugun Hanci ko Rauni:
Idan an buge hanci ko an samu wani rauni a fuska, hakan na iya jawo fashewar jijiyoyin jini a hanci.
5. Hawan Jini:
Hypertension na iya ƙara matsin lamba a jijiyoyin jini, wanda wani lokaci kan jawo zubar jini daga hanci, musamman ga manya.
Abin da Za a Yi Idan Habo Ta Faru a Gida:
– Ka zauna ka karkatar da kai kaɗan zuwa gaba, ba baya ba.
– Ka matse hancin da yatsun hannu na tsawon mintuna 10 zuwa 15 domin jinin ya tsaya.
– Ka yi numfashi ta baki yayin da kake matse hancin.
– Saka ƙanƙara ko abu mai sanyi a saman hanci na iya taimakawa wajen rage zubar jinin.
– Kada ka kwanta ko ka karkatar da kai baya, domin jinin na iya shiga cikin makogwaro.
Yaushe Ya Kamata a Je Asibiti?
Idan jinin bai tsaya ba bayan mintuna 20
habo tana faruwa akai-akai.