
27/07/2025
Me Ya Sa Mata Masu Juna Biyu Zasu Iya Barin Ciki Saboda Rhesus Factor?
Rhesus (Rh) factor wani ƙarin nau'in jinine da ke cikin jininmu – yana bayyana ko jininmu Rh-Positive ne ko Rh-Negative misali ace ("O" Rh Positive). Wannan yana taka muhimmiyar rawa musamman ga mata masu juna biyu.
🟥 Idan matar da ke da juna biyu tana da Rh-Negative, amma mijinta yana da Rh-Positive, akwai yiwuwar jaririn zai gaji Rh-Positive daga wajen mahaifinsa. Wannan na iya sa jikinta ya fara ganin jinin jaririn a matsayin abokin gaba – ya fara ƙirƙirar ƙwayoyin rigakafi da zasu iya kaiwa jinin jaririn hari, musamman a cikin haihuwa ta biyu ko ta gaba.
🟡 Idan Ba A Farga Dawuri Ba Zai Iya Haddasa:
Barin ciki (miscarriage)
Ciwo ga jariri
Kumburi ko karancin jini
Ko kuma jaririn na iya mutuwa kafin ko bayan haihuwa 🕊️
Akwai Magani Ko Matakin Da Za A Iya Dauka!
Eh ana iya hana wannan rikici da injection ta Anti-D kafin ko bayan haihuwa. Amma sai an gano matsalar tun da wuri!
---
🛑 Shin Kin San Irin Jininki? Shin Mijinki Yasan Kalar Nashi?
> Idan ba ku sani ba — kuyi gwajin blood group don sanin nau'in Rhesus kafin ɗaukar ciki ko aure. Wannan gwaji ba ya da tsada, amma yana iya kare rayuka!
💡Ya Akeyin Wannan Awon?
🧪 Acikin awon nau'in jini(Blood Group)ake haɗawa da shi, sai dai idan ba a ganshi ba ana bin wasu matakai don tabbatar da baka dashi, watakan (Negative) ne kai.
---
✊ Kira Zuwa Ga Jama'a:
Masu aure, likitoci, malamai, da shugabannin al’umma — mu yada wannan sako. Rhesus factor ba ƙarya bane. Yana da haɗari ga uwa da ɗan cikin ta.
🩺 mu je mu gwada jininmu.
📢 Mu faɗakar da mata da samari.
❤️ Mu kula da rayuka kafin su zo duniya.
---
— In da Ilimi da Lafiya ke haduwa guri guda ~
🩸 Lafiya itace gatan rayuwa.
🍀
🍀
🍀
🍀
🍀
🍀
🔖 Hashtags: