28/07/2025
💋💋 KINA WA MIJINKI SUMBA (KISS) KUWA??? 💋💋
💋 KISS YANA ƘARA DANKON SOYAYYA TSAKANIN MA’AURATA 💋
✦ Amma kar a manta: tsaftar baki dole ce kafin kiss!
Ya ke uwar gida, ko ke ce amarya ko uwargida, kin taɓa lura cewa yin sumba (kiss) ga mijinki na iya jawo hankalinsa ya koma gare ki gaba ɗaya?
Kada ki manta:
Yin kiss ba wai kawai yana motsa sha'awa ba ne, har ma yana bayyana soyayya da kulawa, yana sa miji yaji babu wata mace a duniya da ta kai ki.
ME KISS KE NUNI DA SHI?
Yana nuna babu kyama ko jin kunya tsakaninku
Yana ƙara ƙauna da nutsuwa
Yana rage fushi da yawan sabani
Yana motsa sha'awa da ƙara jin daɗin kusanci
A INA ZA A IYA KISS?
Kiss ba lallai sai a baki kawai ba:
💋 A goshinsa
💋 A fuskarsa
💋 A kirjinsa
💋 A cibiyarsa
💋 A kunnen sa
💋 Har ma da hannunsa ko bayansa
Haka shima miji zai iya yi miki a:
💋 Bakinki
💋 Fuski
💋 Nonuwa
💋 Goshi
💋 Ciki
💋 Cinyoyi
Da sauransu...
KISS BA ISKANCINE BA!
Wasu mata suna ganin kiss kamar aikata alfasha, musamman idan mijinsu ya musu — sai su ce iskanci ne. To wannan ra'ayi kuskure ne! Kiss halal ne, kuma alamar ƙauna ce idan kuna da aure. Idan kina da shakku, sai a tambayi malamai
KISS NA IYA CHANJA RAYUWARKI
Wata uwar gida ta ce,
> "Naga mijina ya dawo dai-dai da ni, duk da ba wani abu na daban na yi masa — sai dai na fara masa kiss."
Kiss kaɗai na iya dawo da soyayya, ya ɓoye dukkan laifinki, ya sa miji ya manta da fushinsa
MATAR DA TA MANTA KISS, TA MANTA SIRRI DAYA NA GIDA.
Idan har ba kya wa mijinki kiss saboda kunya ko rashin sani, to ki gwada sau É—aya, zaki sha mamaki
ABIN LURA:
Ki tabbatar da tsafta: wanke baki, shan ruwa, da tsaftace jiki
Kada a yi kiss da bakin da ya É—auko wari
A sanya niyyar soyayya da nishadi, ba sha'awa kaÉ—ai ba
Ki gwada, ki gani. Ki karɓi mijinki da kiss, ki dawo da martabar ki